A GIDANA 22
{22}
Gaba daya ya gama rikecewa da irin salon da take mai, kan kujera suka fada ciki sali ta zare rigarta, hankalinsa ne ya tashi ya sa bakinsa ya fara tsotsa, a hankali komai ya dawo cikin kwakwalwarsa, da sauri ya hankadeta ya mike.
Zufa ce ta shiga keto mai, cikin tsananin fargaba da tashin hankali ne karara ya bayyana a fuskarsa, kuka Sadiya ta saka tare da kankame jikinta.
Kallanta yai yana maida zuciya tare da komawa jikin bango.
Kuka take sosai, wanda yasa yace 鈥渮aman mu anan mu kadai ne da alama shedsn ya dirsa mana wani abin.鈥�
Cikin kuka tace 鈥淵aya meya faru? Ya akai na ke zaune anan ba riga?鈥�
Tashin hankali ne karara ya bayyana a fuskarsa ya juya baya da sauri ganin ta sauke hannunta.
Dakinsa ya shiga cikin hanzari, ya zube a bakin kofa yana maida wani irin numfashi.
Yana komawa dakinta bishi da wani wulakancen kallo a fili tace 鈥渒omin fansa nazo dauka i can鈥檛 let you have me.鈥�
Ta dau vest dinta cikin jin dadi ta dau wayarta dake gefe ta kashe sannan ta shiga daki.
Wayar ta kara danawa tana duba abinda tai da wayar fuskarta a hade cikin jin haushi.
Idanunta ta lumshe sannan a fili tai tsaki tace 鈥淯seless鈥�
Kwafa tai sannan tace 鈥渁m almost there.鈥�
********
Dady cikin jin dadi ya kalli Zainab cikin hirarsu yace 鈥淎mma kuna zaune lafiya ko?鈥�
Tace 鈥渆h Dady, Adam mutumin kirki ne sosai muna zaune lafiya da shi da mahaifiyarsa.鈥�
Cikin jin dadi Dady yace 鈥渕asha Allah, amma Nabila tace kina aiki dayawa.鈥�
Murmushi tai tace 鈥渉aryanzu baya aiki Dady kaga dolene na dage sosai.鈥�
Shiru Dady yai kafin yace 鈥淎mma Zainab kina ganin rayuwa zata tafi a haka? Yana namiji sai dai ki bashi?鈥�
Tace 鈥測ana nema insha Allahu zai samu.鈥�
Ido Dady ya zuba mata kafin yace 鈥渋n samo mai?鈥�
Da sauri tace 鈥淒ady in har bazai samu dakanshi ba a barshi, meye amfanin aikin da mutum ya samu bada kokarinshi ba?鈥�
Dady kallanta kawai yake cikin wani yanayi yace 鈥淎llah yasa bani na maidake haka ba.鈥�
Kallansa tai jiki a sanyaye tace 鈥測a ya?鈥�
Kai a girgiza cikin wani yanayi yace 鈥渒omanki kinayinsa cikin isa wanda na tabbatar mijinki da wadanda ke kusa dake suna samun hakan a wata fuska ta daban.鈥�
Shiru tai batace komai ba, murmushi yai yace 鈥渁 dinga rausana murya in za鈥檃i magana, kinji?鈥�
Kai ta daga a hankali batace komai ba.
Dady yasa aka kawo musu abinci sukaci, kallanta yai cikin kewa yace 鈥渒iyi hakuri Zainab, bansan mekike ciki ba duk tsayin shekarun nan.鈥�
Shiru tai batace komai ba, yace 鈥渘agode sosai da kika yima kanki tarbiyya na gari, aikin iyaye ne sai dai ke naki mahaifin ya gaza.鈥�
Idanunta ne suka ciko ta dago ta kalleshi, yace 鈥渒iyi hakuri, da tun farko na sanar dake kin fadamin abinda mahaifiyarki ta fada miki da yanzu rayuwar mu ta canza.鈥�
Maida kwallarta tai cikin dakiya tace 鈥渒a yafemin Dady, duk taurin kai ne irin nawa, dana saki fuska da nemi kebancewa dakai na tabbatar hakan bazata faru ba.鈥�
Shiru yai yana kallanta cikin tausayawa da tsananin kauna, dan san da yake ma Zainab daban ne.
Sun yi hira sosai, kafin yace 鈥渮asu wuce saboda dare kar yayi.
Tare suka fito ya rakota har jikin motarta.
Kallanta yai yace 鈥済ashi nazo a kuraren lokaci bansan me zan baki ba.鈥�
Dariya tai tace 鈥渂asai ka ban komai ba dady, hira da fahimtar juna da mukai yafimin komai a duniya, sai dai kayi hakuri amma banajin zan yafewa matarka.鈥�
Kallan Khalid yai wanda ganinsu yasa ya fito daga motarsa.
Dady ya kalleshi sannan ya kalleta yace 鈥淎 ina kika samoshi? Tun jiya nake yabawa da halayensa duk da ban sanshi sosai ba.鈥�
Dan kallansa tai kadan sannan tace 鈥淎bokin Adam ne.鈥�
Cikin mamaki yace 鈥淎boki?鈥�
Tace 鈥渆h, tare sukai skul, da alama yayi kokari sosai a skul dinsu aiki me baisamu ba.鈥�
Cikin rashin jin dadi Dady yace 鈥測a gwada cike application na aikin Electricity ko za鈥檃 dace.鈥�
Batasan sanda tace 鈥渘a ce ya gwada aikinmu.鈥�
Dariya dady yai yace 鈥渉akan ma is good, nasan Zainab tun tana karama mai tausayi ce, harnaji dadi jin tausayin yana nan bai tafi ba.鈥�
Kasa tai dakai kawai tana dariya.
Kusa da Khalid suka iso, Ya gaisheda Dady, hannu Dady yasa a kafadarsa yace 鈥淣agode, Allah ya taimakeka ya bada sa鈥檃 ya kuma daukaka ka.鈥�
Ameen nagode Khalid yace.
Cikin mota ta shiga sukai sallama da Dady sannan Khalid ya shiga suka kama hanya.
Shiru tai gaba daya haushin kanta da yanda tai rayuwa ne ya shiga damunta.
Wayarta ce tai kara alamar shigowar text.
鈥淜o kinsan mijinki ya salwantar da rayuwar wata saboda ya sameki?鈥�
Ido ta zubawa text din kafin taja wani tsaki, Khalid ne yace 鈥淎re you alright?鈥�
Kallansa tai tace 鈥渢ext akamin, bansan meke damun mutane ba.鈥�
Bai tanka mata ba, sai can yai tunanin wannan mutumin, da sauri yai parking bai juyo ba yace 鈥渨ace number ce?鈥�
Tace 鈥渋s okay da alama wanine kuma wannan?鈥�
Khalid baisan sanda yace 鈥渕utane nawa kika batama rai da……..鈥�
Sai kums yai shiru, ranta ne ya baci ta kalleshi tace 鈥渉ar yaushe ka samu hurumin shiga abinda bai shafe ka ba? Ko mutane nawa na batawa rai meye naks s ciki?鈥�
Ransa ne ya baci, ko magana baiyi ba yajs mots ya nufi gidanta, shiru tai bayan ta fadi haka sai kuma tai tunanin kamar bata kyauta ba duba da yanayin shi ya cece ta daga irin wannan matsalar.
Sai dai bata tanka ba ganin yanda ya dame fuska yana tafiya.
Har suka iso gids ba wands ya sake magana, ledar flask dinta ta dauka tace 鈥渂ari na juye na kawoma flask din.鈥�
Ba matsala na tafi dashi jibi.
Kofa ta bude tace 鈥渒a mata godiya.鈥�
Okay kawai yace bai ko kara magana ba, fitowa tai itama rai a bace.
Tana shiga falo tace 鈥淪ai kwarewa gun cewa Okay.鈥�
Sai a lokacim ta kalli falan ba kowa a ciki, cikin mamaki ta shiga kitchen ta ajiye sannan ta nufi daki.
Adam ta gani a kwance, ta shiga tace 鈥淗oney bacci?鈥�
Jin muryarta yasa gabansa ya kara faduwa, yace 鈥渁鈥檃 bana dan jin dadi ne.鈥�
Cikin kulawa ta matsa da sauri tasa hannu a saman kansa, jin ba zafi yasa tai ajiyar zuciya tace 鈥淎lhamdulila ba zazzabi.鈥�
Kallanta yai sai dai abinds ya faru dazu ke fadi mai.
Mikewa tai tace 鈥渒a tashi kasha magani, bari in duba Sadiya.鈥�
Tana shiga taga Sadiya a cikin bargo itama, cikin mamaki ta karasa tace 鈥淪adiya lafiya?鈥�
Sadiya tana hawaye tace 鈥渂anajin dadi ne Aunty.鈥�
Cikin mamaki tace 鈥渒e da yayanki duk ba lafiya?鈥�
Da sauri ta fito ta shiga daki, wayar Adam ta dauka ta kira Khalid, wanda ke bakin titi yana jiran taxi.
Hello Adam!
Zainab tace 鈥渁m sorry in kana kusa ko zaka taimaka mun zuwa asibiti.鈥�
Okay kawai yace ya kashe wayar, dawowa yai ya kwankwasa.
Budewa tai da sauri tace 鈥渘agode.鈥�
Nan ta taso Adam suka fito tana rike dashi, yana karasowa Khalid ya rikeshi ita kuma ta koma ta taso Sadiya.
Adam dake zaune a bayan mota ganin Sadiya yasa gabansa ya fadi, ya dauka shi kadai za鈥檃 kai meya kawo ta?鈥�
A kusa da Adam Zainab tasa Sadiya sannan ta bude gaba ta shiga.
Khalid ne wanda ke tsaye har aka sa Sadiya a mota yana kallanta, ina yasan fuskar nan?
Jin Zainab tace muje.
Yasa Khalid ya shiga.
Adam ya juya kanshi gefe, a hankali yace 鈥淗oney ciwon fa basai munje asibiti ba.鈥�
Tace 鈥渉aka da na dauka amma ganin Sadiya ma ba lafiya nasan da abinds kila kuka ci, ya na barku lafiya na dawo duk bakuda lafiya.鈥�
Khalid ne ya fara tafiya hakan yasa motar tai shiru.
Kafa sadiya tasa a tsakiyan kafar Adam, yatsun kafarta ne suka goge gefen kafafunsa.
A zabure ya kalleta sannan ya kalli Zainab.
Kwantar da kanta tai sannan ta lumshe idanunta tana sosa kafafunsa da yatsun tafin kafarsa.
Gaba daya hankalin Adam ya tashi, suna isa asibitin Standard sukai parking.
Zainab ce ta fara fita akan tana zuwa.
Khalid wanda yake nazarin yarinyar dayake gani kamar ya santa, amma ya akai Zainab ta zaunar dasu tare?
Juyowa yai ya kalli Adam wanda yasa kafa ya ture kafar Sadiya da sauri, Khalid cikin mamaki yace 鈥渓afiya?鈥�
A tsorace Adam yace 鈥淏akomai.鈥�
Kallanta yai sannan ya kalli Adam yace 鈥渨a?鈥�
Cikin sauri Adam yace 鈥渒anwatacw Sadiya.鈥�
Sadiya?
Da sauri Adam yace eh.
Khalid ya jinjina kai bayan ya kara kallanta, kanta ta saukar kasa sannan ta gaisheshi a hankali.
Khalid ya fita daga motar ganin kiran Abba.
Ya sanar dashi zaiyi dare sannan ya kashe wayar, dawowa yai jikin motar sai jiyai Adam yace 鈥淪adiya meke damunki? Bakida hankali ne?鈥�
Kuka tasa tace 鈥渕e nayi kuma yaya? Ni wlh bansan meyasa yanzu kake min fada batare da nasan abinda na aikata ba.鈥�
Zainab yaga ta nufo gun tamai alama daya fito da Adam.
Kofar ya bude, hakan yasa sukai shiru da sauri.
Nan suka shiga, dr ganin ba abinda ke damunsu yasa ta basu paracetamol suka fito.
Khalid ya maidasu gida ya tafi.
**********
鈥淲allahi Allah an dauken kudina.鈥�
Goggo ta fada tana kokarin nuna cikin jakarta.
Uwar Amarya wato kawar goggo tace 鈥測anzu dan Allah a gidan nan ma sai anyi sata? Wannan wani irin wulakanci ne?鈥�
鈥淒ubu biyar wallahi na taho dasu bayan wanda na baki amma gashi ko biyar babu.鈥� Goggo ta fada cikin bacin rai.
Nan aka fara maganganu, Goggo tace aikam sai kowa ya bude jakarsa ta duba.
Nan ran manyan matan masu kudi dake zaune ya baci, akan dubu biyar kike fadawa kanki magana?
Goggo tace 鈥渁i ko dubu daya ne halak dina ne鈥�
Wata ya tabe baki tace ko dubu biyar din aka safe kina da bakin magana ne? Zuwank uban abinda kikaci ai yafi na dubu biyar, komai aka kawo ssi kinci kinsa wani a jaka, wayasan ko garin tusa kayan abinci cikin jakar kika yadda kudin?鈥�
Nan fa ran Goggo ya baci tace 鈥渘aci din ba dan aci aka dafa ba?鈥�
Ganin haka yasa Uwar Amarya ta jawo Goggo suka fito tana bata hakuri.
Cikin kufula Goggo tace gids zan koma bazan iya wannan wulakancin ba.