NOVELSUncategorized

A GIDANA 3

Haske Writers Association馃挕

Shafi na uku
Khalid na shiga dakinsa ya zauna abakin gadansa ya dafe kansa yana kallan number dake hannunsa, ajihar zuciya kawai yai dan baimasan tuno abinda ya faru.
 Kirim ya maka kanshi akan gadon dan takici.


********

 Cikin bacci taji hannunsa a cikin rigarta, juyowa tai ta kalleshi.

 Kara matsowa yai yace “kin gaji ko?”

 Murmushi tamai duk da dai ba gani yake ba saboda duhun dakin, sannan ta kai bakinta cikin nata……..

 Bayan sunyi wanka ne ta kalli agoggo, karfe 2 na dare kasancewar gobe asabar yasa bata damu ba, zuwa yai ya kwanta kusa da ita, sun danyi shiru kafin ta nisa ta kalleshi cikin kulawa tace “Ko muje asibiti?”

 Shima juyowa yao saitin da take kallansa yace “kin matso ne?”

 Kai tadan girgiza kadan tace ” i feel like kamar yin planing din danai farkon auran mu ne yake neman ja min matsala, sannan ina tunanin ko ba kaiba nasan Goggo nasan ganin jikanta.”

 Jawota yai jikinsa yace “karki wani damu, ni ba abinda yake damuna, let’s try slowly.”

 Murmushi tamai sannan ta kura mai ido, a koda yaushe wadan nan kalan nasa ne yake sa take ganin duk abinda tamai bata fadi ba, tana sanshi sannan tana san a sota, shiyasa ko yan uwanta sunyi maganar rashin aikinshi abin bai damunta.

  Iska ya hura mata yace “kallan fa?”
 Murmushi ta dake mai sannan ta sumbaci goshinsa a hankali cikin rada tace am touched.

 Kallan juna sukai a hankali sukai murmushi, bacci ne ya daukesu suna yar hira sama sama.

 Yau da yake asabar ce basu tashi ba bayan sunyi sallar asuba sai karfe goma sha daya.

 Sha dayan ma ahi ya fara tashi, yana shiga toilet ta bude idanunta, agoggon wayarta ta kalla sannan taga sako ya shigo mata.

 Tana karantawa ya fito, kallansa tai tace “Honey wai anjima su Nusaiba da Nabila zasuzo, dama tun shekaranjiya sukace zasu tambayi Dady ko zai barsu.”

 Kallanta yai yace “yau din nan?”

 Tace “Hmm kana tsoro ne?”

 Dariya yasa yace “bari na dauko Panadol na ajiye kusa da ni.”

 Itama dariya tai tace ” Mutanen Goggo.”

 Mikewa tai ta shiga toilet, zama yai a bakin gado yana kallan wayarsa, Khalid please ka kirani ko text kamin…..

 Tana fitowa suka fito falo tare, Goggo na zaune tana shan shayi tana kallo suka fito, gaisheta tai sannan tace “Goggo anjima su Nusaiba zasuzo.”

 Da sauri ta kalleta tace “har an kuma yin wani hutun?”
Adam ya kalleta yace “wace tambaya ce wannan Goggo?”

 Kallan Zainab tai wacce ke kallanta cikin rashin fahimta sai tai saurin wayancewa tace “ah wai nagane kamar basu dade da zuwa waccan hutun ba, ko da yake kwanakin yanzu ai ba wuya.”

 Zainab ta fahimceta sai dai dauke kai tai daga manufarta ta barshi a yanda take nufi da cewa “lokaci yanzu ai ba wuya.”

 Goggo tai dariya tace “yan dambe mutane na.”

 Itadai Zainab batace komai ba ta wuce kitchen.

 Adam ne ya kalli Goggo yace “Ko ba kyasan suzo ai bakya nuna haka ba.”

 Wani kallo tamai tace “kaima so kake suzo? Yaran da suna zuwa ba nutsuwa a gidan nan, fada sai suyi kusan sai hudu a rana daya.”

 Mikewa yai yace “kedai Goggo kallanki ne bakyasan su tare miki tv da kallab india da korea, na fa sani.”

 Bata kulashi ba ta cigaba da cin breadin ta.

 Kitchen ya nufa ya tadda ita tana fere dankali.
Yasan halinta tunda yaga bata kulashi ba harya shigo kitchen din to batasan a mata magana a wannan lokacin.

 ***********

 Yau tun safe duk wanda yazo siyan koko sai Umma ta fadamai ai ya samu dan karamin aiki a cikin garin kano, badai wani aiki bane sosai amma babbar mace Hajiya zai dinga tukawa.

聽 Yana daga cikin daki yaji ana mai Allah ya sanya alkairi, a lokacin yana zaune yana duba result din wani test da sukaje sukai, jin yanda matar ke mai Allah ya sanya alkairi ne yasashi mikewa, tana fita ya shigo cikin gidan, Umma na zaune tana dama koko, sai daya gaisheta sannan yace “Umma badai harkin fara fadawa mutane na samu aikin tuki ba?”

 Cikin farinciki tace “yanzu Salamatu tazo takemin zancen Salmanu na hada lefe shine nake mata zancen? Da wani abu ne?”

 Dan huci yai kafin yace “ai da kin bari na soma aikin sai ki fada musu, in abu yazo da tsautsayi fa?”

 Cikin tashin hankali tace “akwai matsala ne?”

 Ganin yanda tai yasa yai saurin cewa “a’a kawai dai da kin bari sai dana fara.”

 Umma tace “ai salamatu da Karima kwai na fadawa.”
 A ransa yace ai su kadai bakinsu radio ne, amma a fili baice komai ba.

 Gun Abba ya shiga wanda ke kwance, Abba yace “yanzu dama zan sa a kiraka, dan taimaka ka kaini bayan gida.”

 Nan Khalid ya dagashi suka nufi toilet, sai daya gama sannan ya kirashi suka fito.

 Abba yai dariya yace “ai wasa wasa wannan dabarar ta bature ta taimaka, yanzu kaga da bandakinmu na da ne sai dai in san yanda zanyi, ga kafa daya babu gashi kuma tsugunno ake, kaga kuwa wannan dakasa aka sa mana na zama ai yafi.”

 Murmushi kawai yai baice komai ba, sai da Abba ya zauna sannan yace mai “Khalid!”
 “Naam Abba.”

 Ya kalleshi fuskarsa cikin kulawa yace “ka fahimci mahaifiyarka, tsabar zumudi ne yasa ta kasa yin shiru.”

 Khalid yace “na sani Abba.”

 Dan dariya Abba yai yace “yaushe zaka fara aikin?”

 Yace “hmm.”

 Abba ya kalleshi yace “akwai matsala ne?”

 Shiru yai yana kallan Abban, yana san sanar mai gaskiya sai dai yana tsoron yanda zasu kara shiga damuwa tun balle in sukaji matar abokinsa wanda sukai makaranta tare ne ya tabbatar sai sunji ba dadi, hakan yasa kawai yace “a’a anjima zanji sanda zan fara.”

 Abba ya saki fuska cikin jin dadi yace “Allah yayi albarka yasa a fara a sa’a, duk da ina tsoronka da tukin mota sai dai ina fatan ka fara dashi a hankali kuma ka cigaba da duba aikin yi, yanda kake da jarabawa mai kyau din nan banda dai kasarmu ta zama abinda ta zama ai aiki kam bai kamata ka rasa ba.”

聽 Khalid yace “Amin Abba insha Allah lokacin da za’a samu aikin zai zo.”

 Abba yace “haka ne, Allah yasa a dace.”

 Amin yace sannan ya mike ya fara gyara mai zaman sa.

 Umma ce ta kirashi ya fito ya dau abincinsa ya shiga daki.

 Shiru yai a cikin dakin ya zubawa koko da kosan ido yana tunanin mafita, takardar dake rike a hannunsa ta number waye Adam yake ta bi da kallo.

 Yanzu ya samu ya biya kudin makarantarsu Asiya, nan gaba kadan zai sake biyan wani tunda rabi yake badawa a farko sai ya cika rabin daga baya, ga bashi, ga hidimomin gida, ga jikin Abba, idanunsa ya runste saboda yana ganin zaben abinyi a wannan lokacin sam ba nashi bane.


 Abincin yaci yana gamawa ya dau wayarsa ya kira Salmanu, ya kuna kanon ne?
 Salmanu yace eh wlh, ai naji haushi da baka samu aikin nan ba, gashi haryanzu ba wani labari.”

 Khalid yace “bakomai ai aiki lafiya.”

 Ya kashe wayar yi shiru yana kallan wayarsa, mikewa yai da sauri ya shiga cikin gida yai wanka, yana gamawa ya fita waje dan ganin abinyi, ya bari akan in dai har yamma bai samu wani abu ba to fa lalai zai kira Adam.


*******

 Karfe biyar na yamma tanata girki, Goggo ta shigo kitchen din tace “dame za’a tayaki? Naga yau sai girke girke kikeyi.”

 Tace “barshi wlh Goggo ai na ma gama.”

 Goggo tace “to ki bar wanke wanken nayi.”

 Zainab tace “su Nusaiba in sun huta sayi.”

 Kamar da wasa tana rufe baki taji karar bude gate, da sauri ta dauraye hannunta dan dama duk ta juye abincin a flask, ta nufi falo cikin tsananin farin ciki.

 Goggo ta kalleta tace “goben nan za’a jiku kina musu fada.”

 Tana bude kofar waje ta hangosu suna fito da akwatinsu daga mota.

 N square abinda ta fada kenan suka waigo ai suna ganint suka bar akwatin suka nufota da gudu suka rungumeta.

 Cikin farinciki tace “Welcome.”

 Dagowa sukai suna dariya Nabila tace “kai wasa wasa Allah Aunty na gaji, tafiya taki karewa.”

 Nusaiba tace “har wani tafiya taki karewa banda uban baccin da kika maka a hanya.”

“Yaushe nai baccin? Dan na rufe ido shine……”

 Da sauri tace “zaky fara ne?” Ta fada cikin hade rai, sun san halinta akwai fara’a da wasa da dariya amma fa in taso, sannan in ta birkice to fa ba kanta.

 Da sauri suka guntse bakinsu sannan suka jawo akwatin da kayan da suka taho mata dashi suka nufi ciki.

聽 Goggo tana falo suka shigo, “oyoyo oyoyo ga mutanen nawa sun iso.”

 Nusaiba tace “Goggo.”

 Goggo ta kara ware fuska tace “lale lale maraban inji larabawa.”

 Nabila tasa dariya tace “Marhaba suke cewa Goggo, yau kuma garin larabawa muka nufa?”

 Zainab tace “koma me suke cewa tunda kin gane na miye wannan dogon sharhin.

Gate aka sake bude wa wanda yasasu juyawa, Nabila tace “Ya Adam na yawo…….”

 Kallan da Zainab ta mata ne yasa tai gum.

 Shiga da jakakkunan nasu sukai dakin da suke kwana, suna fitowa ya shigo shida Dauda driver wanda ya kawo su Nusaiba.

Yana shigowa yace “My headache kuna ina??”

 Fitowa sukau daga daki, Nabila tace “bayan munyi fushi, kasan zamuzo ka fita.”

 Dariya yai yace “ai yanzun nan na fita nima ko Honey?”

 Ya fada yana kallan Zainab, tace “ko yanzu ya fita ko dazu ya fita meye naku a ciki?”

 Goggo ta kalleshi cikin takaici, ya bari kowa ya rainashi, kallan Goggo yai sannan ya dauke kai dan ya gane wani abin bai mata dadi ba.

 Zama sukai bayan sunyi sallar da ta riskesu a hanya aka fara cin abinci.


*********


 Khalid ne ya dawo gida bayan yawon daya sha a garin na dan batta, can ya samu jiran shago yadanyi aka biyashi, shiru yai a cikin daki kawai ya gama yanke shawara zai fara wannan aikin sai dai sai yaji abubuwa guda biyu, na farko shi bashida gun da zai zauna a kano sai abu na biyu baisan aikin da za’a kankantar dashi.

 Yana cikin tunanin nan bai fargaba kawai yaji ance Hello!

 Shiru yai daga can bangaren Adam dake zaune ana hira ya mike yai daki ya kara cewa “Hello!”

 Khalid ya daure yace “is me Khalid Danbatta.”

 Cikin mamaki Adam ya kalli wayar sannan ya kara karata a kunne yace “who?”

 “Khalid Usman Danbatta.”

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button