NOVELSUncategorized

A GIDANA 2

Haske Writers Association馃挕

Shafi na biyu
******

聽 Khalid yana sauka ya wuce inda Salmanu yamai kwatance, ganin anata aiki agun yasa ya gane ya iso, da sauri yasa hannu ya dauko wayarsa ya kirashi.


 Jiki a sanyaye Salmanu ya daga yace “Khalid!”

 “Na iso, kana ina?”

 Salmanu yace “bari nazo.” Ya kashe wayar.
Bai jima ba sai ga shi nan ya fito, Khalid na ganinsa ya matsa gun da sauri yace “ya? Har an fara?”

 Cikin rashin jin dadi Salmanu yace “Khalid kayi hakuri wai mutanen da sukeso sun isa, ma fada musu akwai sauran daya da zai karaso yanzu sunce wai a’a iya mutum biyar zasu dauka.”

 Murmushi yai tare da dan dafashi yace “bakomai, shiyasa duk kai wani iri?”

 Kallansa yai yace “Allah duk abin ne yaban haushi, gashi ni kuma wlh kudin nakeso kasan ina tara lefe da wlh na barma kayi.”

 Khalid yai dariya yace “Just forget, kaidai yanzu ka shiga kayi aikinka, kafin kai laifi.”

 Salmanu ya dauko dari biyu yace “gashi dan Allah na asarar mota dana saka.”

 “Kai ka sani? Ko na sa kaina?”

 Salmanu yace “ni na saka wlh.”

 Khalid ya zare hannunsa daga kafadarsa yace “Good luck ni nayi nan.”

 Yai gaba ya barshi rike da dari biyun, Salmanu ya bishi da kallo a ransa yana jin haushin wannan lamari na kasarmu, bazai manta yanda Khalid yai karatu a makaranta ba, duk wani abu da za’ai a faculty’s dinsu, shine yake wakiltarsu, shine yi musu tutorials da sauransu amma dan bashida hanya gashi nan ko karamin teaching ya kasa samu.

 Khalid kam yana tafe yana tunanin kalaman Adam, ba shakka ransa ya sosu da yanda ya mai magana, dan duk wanda ya kalleshi ya kalli yanayinsa yasan yanayine na dauriya da wahala, amma wai tambayarsa yakeyi wai wani company din yake aiki?
 Murmushin takaici yai tare da sa hannu a aljihunsa, dauramai dari uku.

 Ajiyar zuciya yai dan wata yunwa da yakeji gashi kuma kudin motar komawa ma yamai kadan.

 Mezai danyi yadan samu kudin da zaici abinci ya kara kudin mota?

*********
“Duka duka anan muka kawo karshen shirin mu na Yammacin mu a Yau, sai mun hadu daku a shiri na gaba.

 Ni Zainab Aliyu Tahir nake cewa mu huta lafiya.”

Ana dauke camera daga kanta ta shiga bubuga kafadarta saboda dan gajiyar datai, kallanta staffs din gun sukai sukace “Hajiya akoda yaushe ke ta dabance, in kina shiri gaba daya komai tsayawa yakeyi, mu kanmu rasa wayar da zamu dauka da texts din da zamu karanta mukeyo.”

 Kallan mai maganar tai tace “kuma sannunku da kokari.”

 Ruwan dake gabanta ta dauka ta sha sannan ta mike tace “Ina Ramla?”

 Bata nan, dazu kuma tana nan a tsaye.

 “A ce mata ta sameni a office.”
 Ta fada tare da wucewa.

 Zama tai a office dinta tare da daukan wasu takardu tana dubawa.

 Knocking din datajine yasa tace “shigo.”
Ramla ta shigo cikin yanayin tsoro dan ta tabbatar laifi tai, ko kofar bata maida ta rufe ba ta watso mata takardun dake hannunta.
 Gaban Ramla ya fadi ta kalleta a tsorace.

 “Me kika dauki media?”
 Murya na rawa tace “media? Aunty Zee?”

 Fuska ta daure sosai, tace “ya akai kika samu aiki a nan?”

Bakinta na rawa tace “munyi interview……”

 Bashi nake tambayarki ba, kallanta tai a tsorace tace “munzo munyi audition….”

 “Kin min shiru ko sai ranki ya baci? Karatun aikin jarida kikai ko me?”
Da sauri tace “shinai.”

 “Then uban me kika rubutamin?”

 Idanunta ne ya ciciko tace “binciken da kikace naje nai….”

 Ki koma kije ki sake report din nan sannan don’t expect me in sake kiranki na miki bayani, ma tabbatar kinsan halina kinji me nakeyi in har nama mutum magana.”

 Hawaye ne suka zubo mata tace “insha Allah.”
Haka ta tsugunna ta shiga kwashe takardunta, tana gamawa ta fita tana hawaye.

Zainab ta dansa hannu akanta dake dan sara mata, agoggo ta kalla, ta kusa tashi, nan ta dau waya ta kira Adam.

********

 Shikam Adam yana rabuwa da Khalid ya wuce majalisarsu ta yan zaman kashe wando, suka sha hira da gulma, akai ta fasamai kai akan yanda ba cas ba as sai jin dadin rayuwa da yakeyi.

 Dariya yasa sosai yace “nifa dama can ba mutum bane mai san wahala dan dai Allah bai bani dama bane, shiyasa yanzu da Allah yaban dama nake morar jin dadi na.”

 Nazifi ya kalleshi yace “wai da gaske kake ma ka nemi aikin kuwa?”
 Yace “tab ai ko form ban taba siya ba, itadai ta dauka samune banyi ba.”

 Nazifi yace “Shegen aikai Allah ya maka baiwar sanin yanda zaka so kanka.”

 Adamu yace “kasan Ita akwai san bin abu yanda ya kamata, danace tasa a nemomin aiki fa cewa wai corruption ne.”

 Nazifi yace “ai shiyasa nakejin haushin yar iskar Kubran nan, sai anyi magana tace batada kudi, ni wlh haushi take bani, da alama aure zan sake wlh, kuma Hajiya zan nema nima.”

 Wata muguwar dariya Adam ya saki yace “tab amma lalai kai dan mugun san banza ne, irinsu Zee dita an fada maka sunada yawa ne??”
 Nazifi yace “mudai yau mijin Hajiya dan Allah ka dubemu mu dan tauna mai yaji yaji.”

 Nan ya zaro dubu biyo aka siyo musu balango suka ci suka kora da lemo, sannan ya mike ya nufi gida.

 Goggo na zaune tanata kallo tana dariyar ta ya shigo.
 Tana ganinshi ta mike tace ” Ina ka tsaya ne?”

 Kallanta yai sannan ya kalli Tv yace “wai Goggo dan Allah bakya gajiya ke da kallo ne? Kullum kina gaban kujera kina kallo.”

 Tace “wannan ba damuwarka bane, sannan in na zauna a dakin ma me zanyi? Ba gwara nai kallo na debe kewa ba, ni ba wannan ba, bani kudina.”

“Wai nawane ankon? Ai baki fadi kudin ba.”

Kallansa tai tace “ban san fa iya shege ce maka akai bansan me nake ba? Ni bani kudina bansan jan magana.”

 Dubu biyar ya zaro ya mika mata yace “gashinan, amma wlh nasan ankon nan baifi dubu 3 ba.”

 Amsa tai sannan tace “wai ni Adamu wannan kudinka ne?”
“Na matata ne.”
 Komawa tai ta zauna tace “daga baya kenan, kudi ba naka ba sai bin ba’asi, wannan da kaine ma kake aikin kila ba ci zanyi ba.”

 Wucewa ciki yai ya kwanta, kan kace me bacci yayi gaba dashi.

 Baccinsa yasha sosai, dan wayar Zainab ce ta tasheshi.

 Yana ganin sunanta ya kalli agoggo sannan ya mike zaune.

 “Honey kana ina?”

 Cikin maganar bacci yace “ina gida na sha bacci ne.”
 Tace “nakusa聽 tashi inka samu driver din ka turoshi yazo ya dauken.”

 Da sauri yace “yanzu zanzo, bansamu ba tukunna.”

 Kashe wayar tai sannan ta duba laptop din dake gabanta, tana gamawa ta fara hada kayanta.

Adam kam suna gama magana ya sauko daga kan gado, da sauri ya dau key zai fita yaji fitsari, nan ya koma toilet yai sannan ya fito ko Goggo baima magana ba wacce ke zaune tana kallo tana cin abinci.

 Da sauri ya shiga mota ya ja ya fita, dole na nemo driver bazan iya yawon nan ba, tuno da Khalid dayai ne yasashi yin dogon tsaki, ya akai ban amshi number shi ba? Ai da masifa da sai na sashi yin aikin nan.

 Yana isa ya kirata a waya.
Nan tai sallama dasu ta fito.

 Tana shiga ya kalleta cikin kulawa yace “Ayya Honey da alama kin gaji.”

 Murmushi tai tace “kawai dai fadan da ake sanine yake sani gajiya.”

 Hannunta ya riko ya sa akan kuncinsa yace “nasan duk wanda yaga shirin ki na yau zai ce waccece wannan? Ni kuma da ina gun zanyi saurin cewa My Wife, da magana ne.”

 Yanzu kam dariya tadanyi sannan ta zare hannunta tace “Honey.”

Yace “kinga gashi harna saki kin ware.”

 Murmushi tai sannan tace “as always.”

 Mota ya tada dannan ya juya suka hau kan titi, kallanta yai yace “Honey zaki iya tuna Kwaro? Cinye du?”

 Kallansa tai tace “wanda kake yawan labarinsa? Wanda ya maidaku hoto?”

 Da sauri yace “shi shi, ai na fada miki komai malamai sai dai suce shi ko?” Tace “eh, ya akai?”

 Wata dariya ya sheka yace “kinsan yau na ganshi?”

 Kallan mamaki tamai tace how?

 Cikin zumudi yace “a hanya, kin ganshi?” Ha ha ha unbelievable wai bai samu aiki ba, sannan kina kallanshi kamar talakan kauyen.”

Kallansa tai yanda yaketa dariya tace “lalai Honey to menene na dariya?”

 Kallanta yai yace “can you imagine?”

 Tace “a yanayin kasarmu sosai, saboda mutane nawa ne suka dace suka cancanta a basu aiki amma suna nan ba labari?”

 Dariya yake sosai yana cewa “ban taba kawowa ba wlh.”

 Kallan mamaki take mai, dan haryanzu bataga abin dariya ba.

 Da kyar ya gama dariyar sannan yace “ai naji haushi wlh ban amshi number shi ba.”

 Kallansa tai batace komai ba.
 Yace “namai rayin aikin driver dinki ai, wayyo Allah ubangiji yasa ya amsa.”

 “Driver?” Ta fada tana kallansa, yace “eh.”

 Wani murmushi tai sannan tace “baka tunanin u hurt his pride?”

 Yace “taimakon sa zanyi ai, dayaje yana neman abinyi ga aiki a gida?”

 Kanta tasa jikin window dan ta kasa fahimtar me yake nufi.

 Adam ya jawo hannunta yace “me? Bakyaso?”

 Tace “no, kawai dai ina ganin kamar bai kamata ba, abokinka ne fa?”

 Ganin yanda ta dau lamarin yasa yai saurin canza maganarsa yace “na san bai kamata ba, amma bansan yands zanyi na taimakeshi ba, kins gani nima fama nake da neman aikin nan.”

 Murmushi tai tace “na fahimta yanzu, amma dai still da baka mai zancen ba, ba lalai ya fahimci dalilinka ba.”

 Hakane kuma, gashi banda numbersa.

 Tace “kawai dai Allah yasa yai calling dinka back sai ka nusar dashi.”

 Kai ya jinjina sannan yace “Thanks.”

 Dame?

 “Komai ma.”
Murmushi sukama juna.


***************

Khalid kam mariri ya shiga yaje gun masu ruwa ya amsa kura akan zai biyasu duk kaiwa daya, haka yai tayi ya hada dubu daya ya nemi abinci yaci yahau mota ya koma gida.

 Yana shiga danbatta ya tsaya yasai lemon fata ya wuce gida.

 Suna zaune a tsakar gida Asiya na alawar madara da take kaiwa makaranta ya shigo.

 Yana tafe su Asif na binsa a baya shi da Amir, wanda ya kamosu daga wajen wasan kwallo.

 Bayan sun gaisa da Umma ne ta kalleshi tace “an dace?”

 Yace “naje wlh wai sun cika, amma insha Allah………”

聽 Umma ce tai ajiyar zuciya ta kalli Abba dake zaune yayi shiru, tace “Khalid bayanda za’ai mu samu ko dubu uku ne?”

 Kallanta yai yace “wani abu ya faru ne? Tace “dazu daka fita Amir yana wasa ya bige Abbanka aka fama ciwon sai da muka kira mota muka kaishi chemist aka gyara, gashi bashin gun Karima naci, ka santa.”

聽 Kallan Abba yai ya matsa da sauri yace “Abba ya jikin?”

 Abba ya share kwallarsa yace “Khalid kayi hakuri inata karama nauyi.”

 Da sauri khalid yace “ko kadan Abba.”

 Umma dake share hawayenta itama tace “Khalid gashi yau ba komai a gidan, kokon dana saida shi na mana abincin rana dashi.”

 Kuka ne yadan kwace mata, hankalinsa ya tashi, gata tana kuka ga Abba ma na hawaye, Asiya ma daurewa kawai tai amma sai da kwalla suka zubo mata.

 Bai san sanda yace “Umma na samu aiki.”

 Da sauri ta kalleshi Abba ma ya kalleshi yace “Da gaske? A ina?”

 Idanu ya runtse, me yace? Me ya kaishi?

 Umma ta kalleshi tace “nasan wasa kakeyi, wannan lamari dame yai kama? Sai bani jari kake yana karyewa, duk wahalar da kakesha haryanzu……..”

 Da sauri ya zaro takardar dake aljihunsa yace “kingani number wanda ya daukeni ne, matarsa ce take neman mai tuka mata mota shine yakeso in amshi aikin.”

 Matarsa? Abba ya fada yana kallansa, sannan yacigaba “kana ganin abinda ya sameni a aikin tukin mota banaso kaima ka gadoni.”

 Asiya ce da sauri tace “Alhamdulila yaya indai har driver suke nema聽 da alama sunada kudi kenan? Nawa zasu dinga biyanka? A ina zaka zauna tunda dai nasan a kano ne.”

 Yace “to Hajiyar tambaya.”

 Umma ce ta kalli Abba tace “shekararka nawa kana aikin? Ai tsautsayine da kaddara.”

Sannan ta cigaba “kai Alhamdulila.”

Khalid ya kallesu dan baisan me zaice ba……

 Ni kaina jinai bansan me zance ba….lol

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button