NOVELSUncategorized

A GIDANA 37

{37}


  Goggo na zaune adan kucilin falanta da tana kallo, Adam dake kwance a dan mitsilin dakinsu ne yace “Goggo dan Allah rage magana haba, tsakani da Allah 


kallo da sassafen nan?”

 Ranta a bace tace “ka fito ka bar gidan nan ko sai jikinka ya gayama? Ai tun jiya nace ka samo aran yar mota ka kaini gidan Hajiya Bilki.”

 Komawa yai ya ja bargo baice mata komai ba, haushi ya kamata ta taso ta shigo dakin da karfi ta yaye bargon tace “ko tsinaniya kujera banda ita sai dai na 

zauna a kasa amma kai ka shige cikin bargo banda uban bacci da yawon banza baka da abinyi.”

 Cikin kufula yace “koma me nake meya dameki? Ni ki barni da rashin matata dake damuna.”

 Wani kallan banza tamai tace “har wani rashin matarka? Nawane ragowar kudin mu?”

 Kallanta yai yace “wani kudin bayan kin kwacesu?”

 Yaushe?

 Kallanta yai ya saki baki kafin yace “banasan wasa, wancan satin kikace nawane ragowar kudinmu nace miki dubu dari da ashirin kika ce na kawo miki darin 

baki yadda dani ba kinji kudin sunyi saurin karewa.

Kanta tadan sosa tace “ina nasa?”

 Da sauri ya mike yace “bangane ba.”

 Hankali a tashe suka fara neman kudi a cikin dakin, hankalin Goggo yayi dubu ya tashi ji take kamar rayuwarta aka gutseri.

Gaba daya kayan dan kayan nasu suka fito dashi waje suna dubawa, sai dai bashi ba labarinsa.

 Goggo ta kalli Adam tace “yaushe ka bani?”

Shiru yai yana tunani kafin yace “kamar da safe ne?”

 Karya kake wlh, ni baka ban ko ficika ba, bayanda za’ai ka ban makudan kudi nai wazgarere dasu har sati daya bansan inda suke ba.

 Gabansa ne ya fadi dan maganar gaskiya ranar ya ciro kudin daga masallaci sai majalisa yaje yana dawowa gida zai bata yaga wayam, kallanta yai yace “ki dai 

duba Goggo.”

 Daga can makotanta ta kalla wadanda kowa ya fito yana kallansu, haushi ya kamata tace “ku kuma me kuke kallo?”

 Asabe da dakinta ke kusa da nasu tace “kudai kusan barawon daya dauke a cikin ku dan mu gidan nan ba’a sata.”

Ran Goggo ya baci ta kwashi kaya ta shiga ciki, kallan Adam tai tace “fadamin, uban wa kaba kudin?”

 Yace “wai Goggo wa nake dashi da zan ba inba ke ba?”

 Zama tai dabas a kasa tace “yanzu ya kake so muyi?”

Yace “nizance haka Goggo yanzu ya zamuyi?”

 Takaici ne ya kamata tace “wai uban me ma kake harynzu baka samu aiki ba?”

 Ransa ne ya baci ya fita daga gidan, kanta ta rike wanda ke sarawa.

********

Gaba daya sun sa kaya a cikin mota, Nusaiba da Nabila sai murna ake za’abi Zainab.

 Zainab dake daki ta kalli dakin, bata taba kawowa zata dawo tai dogon zama a gidan nan ba, duk da wata uku tai amma agunta dogo ne.

Jawo dakin tai ta fito, a falo taga Basma, fuskarta a hade tace “zamu wuce.”

 Basma ta matso tace “Dady yace ki kirashi kafin ku wuce.”

 To tace batace komai ba daga nan.

 Basma tai shiru tanaji suna waya da Dady yana ce mata su tafi da mammab ya dinga kwana a dakin waje kafin asan yanda za’ai dan sam hankalinsa bai kwanta da 

barinta ita kadai ba, in su Nabila suka taho.

Suna sallama ta kalli Basma tace “mun wuce.”

 Da sauri Basma tace “Zainab!”

 Tsayawa tai batare da ta kalleta ba, Basma ta dan tako tace “Zainab ki yafemin, sharrin zuciya da sharrin kawaye ne ya sani yin abinda nai, akullum ina 

danasanin wannan abu, gashi dalilinshi bazan sake haihuwa ba.”


 Kallanta tai da sauri, hawayenta ta share tai murmushi tace “hukuncin da Dady yamin kenan”

 Gaba daya jikin Zainab ne yai sanyi, tama kasa ko cewa wani abu saboda mamakin wannan zancen.

Basma ta nufi kofa tace “Nusaiba banda fada dake da Nabila.”

 Nusaiba ta dan turo baki sannan tace “Mumy mun wuce.”

 Haka suka shiga mota Zainab ta shiga Mammab yaja suka tafi, gaba daya jikinta a sanyaye.


*********

 Sam Khalid ya kasa gasgata abinda ke faruwa, yana fitowa daga shago ya nufi garage inda suke dan aiki, yana yi yana mamaki, sam zuciyarsa taki amincewa.

Haka ya dawo gida, sai dai sam ya kasa fadawa Umma da Abba, gani yake karsu sa rai azo ba’a dace ba, dan harya gaji da sanar dasu zaije jarabawa sai sun 

gama sa rai yazo bai samu ba, duk sai yaji ba dadi.

 Shiyasa wannan karan ya barma kansa, in haryaje yaga da gaskene aka dace sai ya fada musu, dan ma yanzu hankalinsa ya kwanta ba bashin da ake binsu, duk 

sun biya, sannan Abba ba laifi in ya rike sanda biyu yana iya dan matsawa daga can zuwa can.

***********

Zufa ce ke karyo mata ta ko’ina, daga yanda take runtse ido zakasan mafarki take mara dadi, jin sautin numfashin Adam da Raziyya ne yasa ta sa hannunta 

toshe kunenta kafin a hankali ta bude idanunta.

 Kwance take a kan gujera a falo, wani abu tadan hadiya tare da kunna fitilar wayarta, duk da Dady da kansa yazo aka kwashe komai aka sa mata sabo na gidan 

amma ganin komai take kamar yanzu ake yinsa.

 Mikewa tai ta kunna watar falan kawai ta dako laptop dinta ta hau aiki, ta shirya abubuwa da dama wanda inta koma za’ai.

Haka tai ta aikinta har asuba tai, sallah tai sannan ta shirya, gadanta ta kalla, duk sanda zata fita yawanci Adam na bacci in bayayi kuwa to yana kitchen 

yana hada mata tea, wani abu ne mai daci ya zo bakinta hadiye shi tai sannan ta dau jakarta ta fita su Nabila na bacci.

 A waje ta tadda Mamman, nan ta gaisheshi suka tafi, a hanya tacemai idan su Nabila sun shirya ka kaisu sumana siyayyar abin gida, yace “to Hajiya.”

 Nan suka karasa ta fita tai ciki.

 Mutanen dataga sun fara hallara ne tai murmushi tace “is good to be serious.”

 Tana shiga station din taga duk staff dinsu a bakin kofa, hadda rike takardar da aka rubuta Welcome back.

Wani irin dadi taji dan dama wata ukun nan kamar mara lafiya tayisu saboda rashin aiki.

Murmushi ne yabayyana a fuskarta nan ta fara amsa gaisuwarsu cikin jin dadi, Head Director ne ya matso yana tafi, yace “barka Zainab yau kamar sallah nake 

jinta.”
Kallansa tai bayan sun gaisa tace “Yallabai inaji sai mun shiga meeting kafin a fara interview.”

Da sauri yace “an gama Hajiya.”

 Nan suka wuce, Ramlatu ta gani ta taho da sauri, kallanta tai da sauri ta gaisheta, Zainab ta amsa sannan sukai ciki.

Sun yi discussing akan abinda zasuyi sannan ta bashi takardun da zaiyi reviewing na abubuwan da za’asuyi nan gaba.

 Wani irin dadi yakeji na ganin Zainab balle data kawo abubuwan cigaba yasashi jin wani kwarin gwiwa.

Karfe goma tara daidai ta nufi dakin da za’ai interview kujerar ta ce a tsakiya, tana shiga ta zauna, kallan su tai tace “mu fara?”

 Sukace eh,

 Kowa ya shigo tana rike da takardar dayai jarabawa da ita, tana mai tambayoyi tana duba takardar, su takwas ne.

  Number 5 aka kira, ba tare da ta dago ba ta shiga duba takardarshi, ganin wannan takardar da ta wahalar da ita ne yasa ta kara dudubawa tana kara bin 

komai, har ya iso ya zauna.

 Rufe takardun tai sannan ta dago dan taganshi.

  Kallansa tai idanunta suka dan fito, tasan ita tace yai Applying amma bata kawo ya ci ba.

 Wulakancin da ya mata ta tuno, fuska ta daure sosai, sannan ta kalleshi, shima kallanta yai fuskarsa daidai ba alamar fara’a ba alamar daurewa.

 Takardarsa aka miko mata, ta amsa tana duba sunanshi, skul din dayai result dinsa da sauransu.

 Kallansa ta sakeyi, H.Director ne yasa dariya yana kallan takardunsa yace “masha Allah, irin wannan cik exams haka.”

 Cikin jin dadi ya kalli Zainab yace “Da alama kema abin ya birgeki.”

 Fuska ta hade tamau sannan ta kalleshi tare da ajiye biro din hannunta, nan ta fara watso mai tambaya, amsa yake bata yana kallanta, itama idanshi a kansa 

take mai tambayar.

 Dan kai ta dauke bayan duk ya gama bata amsar tambayoyinta sannan tace “ka tabbatar ba satar amsa kai ba?”

 Kallanta yai yace “satar amsa?”

 Tace “eh from this naga Math ka karanta, then taya ka bada wannan amsar? Ta fada tana circling din takardarsa shafi na biyu.”

 Wani dan murmushi yai tare da dan kauda kai kadan, dan ya fahimci da saninta take watsomai tambaya dan yanda ta dinga jero mai tambayoyi yanda yaga suna 

kallanta ya tabbatar ba haka tawa kowa ba.

 Fuska ta hade tace “Murmushin me kake?”

 Kallanta yai yace “da wanda yai satar amsa da masu kula da exams hall din har suka bari akai wanene mai laifi?”

 Fuska ta kare daurewa tace “kana nufin satar amsar kai?”

 Kallan na kusa da ita yai yace “Sir kasan yanda mukai Exams din nan it seems like she is not there.”

 Nan ya mata bayani ba yanda za’ai wani yai satar amsa.

 Kallan Khalid tai sannan tace “Idan aka baka aiki a news room ya zakai?”

 Nan ya cigaba da bata amsoshinta, sai kara mai tambaya take sai da H.Director yace “Zainab ya isa haka wannan tambaya haka.”

 Shiru tai tana mai wani kallo, kallansu yai ganin basa kallansa yadan daga mata kafada alamar ko a jikinshi.

 Haushi ya kara tukota ta harareshi tare da cewa “next.”

 Fita Khalid yai, har ta bude takarda ta kalli kofar inda ya fita sannan ta cigaba, sai da suka gama sannan ta fito.

 A inda suke zaune ta ganshi, dauke kai tai ta wuce.

 Shima yi yai kamar bai ganta ba yai gaba.

 Tana shiga office dinta ta zauna, Malama shigo? D’an Gidan nan?

 Haushi ya kara kamata data tuno maganganun daya watsa mata.

 Tana zaune Ramlatu ta shigo dasu saboda ana nunu namusu ko ina.

 Zainab tana dagowa suka hada ido, daure fuska tai ta maida kanta kan computer din dake gabanta, nan Ramlatu tace musu “wannan itace Director Zainab nasan 

kunganta agun Interview.”

Nan kowa ya gaisheta, dagowa tai ta kallesu, har Khalid sannan ta amsa tace “Sai kunji daga garemu.”

 Nan suka fita, haka suka gama aka sallamesu akan su koma su jira sai an nemesu.


 Khalid na fitowa ya runtse ido yana addu’a cikin zuciyarsa, wani irin yanayi yake ciki wanda shi kadai yasan ya yake ji.

 Fitowa yai da sauri dan yaje gida ya kai musu labari.

 Yana fitowa yaga wata mota tazo ta wuce, yarinyar dake janta kamar Raziyya.

 Da sauri ya kara kallan motae sai dai ta riga ta wuce, shiru yai kafin ya juya ya nufi tasha.


  Zainab kam kafadar da Khalid ya daga mata ta tuno wani mugun murmushi ta saki tace “ko a jikinka ko? Let me see in zaka juri wahalar da zan baka.”


 Ta saki wani murmushin jin dadi, samun kanta tai cikin nishadi in ta tuno wahalar da zata bashi.


********

 Ran Nusaiba a bace ta kalli Nabila tace “wai da gaske Aunty ta koreshi? Nifa Allah saboda shi na dage sai na zo.”

 Nabila ta kauda kai tana latsa wayarta tace “aikinyi ne bakidashi wlh, haka a skul kika bi kika ishemu da zancen Ya Khalid kamar kanin Dady.”

 Nabila tace “mijina ai yafi kanin Dady a guna.”

 Miji? Nabila ta tambaya sannan tace “Allah kanki ba daya ba, da alama kina bukatar ganin likita.”

 Ran Nusaiba ya baci tace “sai ki kaini ai.”

Mamman ne yce “ayi hakuri kar ai fada dan Allah.”

Nan kowa ya kauda kai har suka isa Jifatu.

*****

Khalid cikin sauri ya isa gidan, hannunsa rike da ledar ayaba da lemo.

Umma na ta shanyar kayan data wanke ya shigo, cikin jin dadin da ya kasa boyowa yace “Ummana.”

 Kallansa tai tare da dan goge hannunta a zaninta tace “Khalid an dawo?”

 Cikin jin dadi yace “Umma insha Allahu mun samu aiki.”

 Idanun Umma ne suka fifito tace “aiki?” Yanda tai maganar kadai zakasan wani irin yanayi ta shiga mai wuyar fassarawa.

Abba da ya dosanu sandar sa guda biyu yana kokarin fitowa waje ne yce “Aiki Khalid.”

 Cikin jin dadi yace “daga Interview nake yanzu.”

Wani irin dadi ne ya kama Umma harda hawayenta.

 Fadar irin dadin da suka shiga a wannan lokaci ma wahala ne dan ni kaina nasan Allah ne kadai yasan yanayin da suka shiga duba da irin lokacin daya deba 

yana gwagwarmayar neman aiki.


 (Yan uwa dake neman Aiki irinsu Khalid suma Allah ya dubesu ya basu)

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button