NOVELSUncategorized

A GIDANA 36

{36}

Shiru sukai suna tafiya a hanya gaba daya Khalid na lura da yanayin dady, hankalinsa ba a karamin tashe yake ba kuma da alama bai san barinta acan, dan dai 

ba yanda zaiyi ne.


 Kallansa Khalid yai yace “in bakasan barinta acan mu kuma a dakota.”

 Kallansa Dady yai sosai yaji dadin maganar dan abinda ke kunshe a ransa kenan sai dai tayaya?
 Kallan Khalid yai tare da yin murmushi yace “yauce rana ta farko tunda nake da Zainab dana taba ganin tana san zama a guri kamar gidanku, gidana a zaune 

kawai take amma sam ba ta sakewa a ciki, gidan kanwar mamanta data zauna kuwa dama kowa yasan ba so take ba tana zaune ne saboda batasan zama a guna, ta ya 

zan tilasta mata ta taho inda bazata ji dadi ba?”


  Mamaki ne ya kama Khalid dan sosai yana mamakin wannan halin na Dady taya zai zauna komai sai ra’ayin yarsa?

Cewa yai ” Amma ni ina ganin nesanta kanta daky da takeyi shiyasa bazata taba sakin jikinta ba, amma in ta zauna cikin yan uwanta dole ta saki jikinta.”

 Kallan Khalid yai cikin jin dadin kalamansa kafin yace “tsoro na akoda yaushe yanda halin rayuwa yake, ina tsoron ajali na yazo muna wannan zaman.”

 Labarin Razy ne ya fadomai, da tashin hankalin da suka shiga, ga ita kanta rayuwar da Zainab din ta fuskanta a gidan mijinta, rage gudun motar yai sannan 

ya kalli inda suke harsunzo kano dan suna daf da shiga kurna.

 “Ina ganin ba shawara bace a barta acan, hankalinka bazai taba kwanciya ba, sannan iddah zatai ni ba muharaminta bane, Kuma gidan mu ne dole zan shiga 

ciki, sannan inada abokai dake zuwa, Abba ma abokansa na zuwa dubashi baza’ace duk sanda wani yazo tana killace a daki ba.”

 Dady ne ya kalleshi yace “me kake tunani? Zainab bazata taho ba.”

 Zan ajiyeka a inda kai masauki zan kawota anjima ku wuce tare.

 Mamaki sosai ne ya kama Dady yace “kana tunanin zataji maganar ka?”

 Khalid baice komai ba ya wuce da Dady, sosai Dady yaji dadin abin nan sai dai sam baisa rai akan zata biyoshi ba, ya daiji dadi sosai a kalla Khalid ya 

nuna mai shi d’a nagari ne.

Khalid na ajiyeshi ya juya danbatta.

 Zainab na zaune a daki Umma na gefenta, ajiye kudin hannunta tai tace “Zainab ki ajiye mai annn duk randa yazo kya bashi, dan bazamu amshi waccen ku amshi 

wannan ba, waccen din ma a dole muka amsa dan karyaji ba dadi ne.”

 Zainab ta kalli Umma tace “Allah Umma bakomai dan Allah ki ajiye? Nima bazanji dadi ba in kika ki amsa.”

 Ajiye mata tai kusa da ita tace “saboda Allah nake zaune dake bawai dan wani abu ba, banasan harkar kudi ta ratsa daga nan in ba’ai wasa ba san zuciya ne 

zai shiga.”

 Kallan Umma tai sannan ta daga kai kawai batace komai ba dan rayuwar nan taso ba karamin birgeta take ba.

 Zama kusa da ita Umma tai tasa hannu a goshinta tace “masha Allah Zazzabin ya tafi.” Ta fada tana kallan Zainab wacce itama ke kallanta.

 A tare sukai murmushi Zainab jiki a sanyaye tace “Umma nagode sosai sosai.”

 Kafadarta ta dafa tace “ki rage sa komai a ranki, Allah baya dorawa bawansa abinda bazai iya ba, duk abinda ya sameki kisa a ranki kaddarace ta Allah sai 

kiyi fatan sa’ar cin jarabawar.”

 Kai ta daga ahankali idanunta sun ciciko da hawaye.

Murmushi Umma tai.

A falo ta zauna suna dan taba hira da Abba kasancewar su Asiya dasu Amir duk suna makarantar islamiya.

Jin sallamar Khalid ne yasa Umma ta kalli waje, dayake labulen a dage yake ta amsa tana cewa “har an dawo?”

 Karasowa yai yana cewa “eh Umma”

Abba yace “badai gudu kai ba ko?”

 Kallan kafar Abba da aka cire yai sannan yace “a hankali muka tafi.”

 Kallan Abba yai yace “Abba inaganin zamanta anan bazai yiwu ba.”

 A tare suka kalleshi, ya kalli Abba yace “iddah zatai bai kamata ta zauna inda ba muharammanta ba, sannan hankalin mahaifinta bazai taba kwanciya ba inya 

barta anan, kuma jikina naban kamar baya jin dadi.”

 Da sauri Umma tace “meke damunshi?”

Kai Khalid ya daga alamar rashin sani sannan yace “ban sani ba wlh haka dai nakeji.”

 Umma ta kalleshi zuciyarta duk ba dadi, dan maganar gaskiya tana san zama da yarinyar ta fahimci tana da tabo na rashin uwa ga kuma takaicin namiji.

Abba ne ya kalleta ya sani sarai zuciyarta ba dadi sai dai ya zasuyi? Kallan Khalid yai yace “bari a kirata na mata magana.”

Da sauri yace “bari na mata magana.”

 Kallansa sukai cikin mamaki, shikuwa yasan halinta dan zaman nan da sukai ya tabbata aka mata lagwalagwa ba abinda zai faru.

 Knocking din dakin yai, daga ciki tana zaure rike da takardar Adam tace “waye.”

 Khalid yace “nine.”
Mamaki ne ya kamata tace “ya akai?”
Magana zamuyi.

Umma ce ta mike tace “ko na mata magana?”

 Khalid ya girgiza kai alamar a’a daga ciki tasa hijab sannan tace “shigo.”

Tura kofar yai ya shiga a bakin kofar ya tsaya yace “kizo na kaiki kano, ku wuce da babanki.”

 Kallansa tai cikin mamaki tace “in wuce ina?”

Gidanku!

 Fuska ta hade sosai tace “a matsayinka nawa kenan?”

“Na d’an gidan nan”

 Baki ta bude cikin kuluwa da takaici tace “da nace ba d’an gidan nan bane kai?”

 Yace “tambayarki haka ta nuna min.”

 Wata dariyar takaici tai sannan tace “korata kake kenan kome?”

 Yace “ba korarki nai ba ina nufin ki bi babanki.”

“Nafi karfin ka wulakantani wlh.”

 Wani mugun kallo tamai ta mike a tsananin zuciya ko kayanta bata dauka ba kawai wayarta da laptop da tab dinta ta dauka ta fito rai a bace.

 Kofa ya bude mata alamar hanya, tsayawa tai tana kallansa cikin takaici kafin tai kwafa.

 Umma ta gani a tsaye a falo, Umma na ganinta ta matso tace “Zainab.”

Zainab tai kasa dakai idanunta suka fara neman rauni, dakewa tai tace “Umma zan wuce.”

 Tana fada tai hanyar neman fita, da sauri Umma ta rikota sannan ta dago da ita tace “ba korarki mukai ba Zainab, nikaina inasan zamanki anan sai dai ba 

yanda zanyi.”

 Kallan Khalid tai kenan shiya kawo wannan maganar? 
Abba ta tsuguna tawa sallama sannan ta kalli Umma tace “nagode muku Allah ya saka da alkairi.”

 Umma ta dauko yar wayarta tace “samin numberki.”

Nan Zainab tasawa Umma ta kira wayarta dashi sannan ta kalli Abba tace “Allah ya kara lafiya.”

 Khalid ta kalla wanda ke tsaye jikin kofar dakin Asiya, wani takaici ne ya kamata ta sake sallama da Abba ta fito.

 Umma har tsakar gida ta rakora tana neman fita waje Zainab tace takoma.

Kayan abincin da aka kawo Khalid ya fito dasu, kalan Umma tai tace “Umma ki taimaka ki bar wadan nan dan Allah badan ni ba.”

 Jikin Umma ne yai sanyi, ta jawo Zainab ta rungume idanunta harda hawaye, Zainab ta share nata da sauri tace “Umma ki taimaka.”

 Kallan Khalid tai tace ya barsu.

 Khalid ne ya fito waje, yana neman bude mota, kallansa tai tace “bani makulina.”

 Kallanta yai sannan ya kalli motar yace “wazai kaiki?”

 “Banaji wannan ya dameka tunda motatace.”

Kallanta yai yace “ki bari na kaiki tukun.”

 “Motarnan tawace sannan jikina ne banaji akwai damuwarka akai, bani.”
Ta karasa tare da mikamai hannu,

 Bai tanka taba ya shiga motar ya zauna, haushi ya kamata ta bude motar inda yake tace “fito.”

 Yace “shigo.”

Tace “Malam fito ko?”

Yace “Malama shigo ko?”

 Jitake kamar ta shakeshi, hankalinta harya kwanta zamanta anan ya koreta kuma yanzu yazo yana wani abu?

 Kallanta yai yace “dare nayi.”

 Ranta a tsananin bace ta bude ta shiga baya yaja suka tafi, har suka isa ba wanda yawa wani magana, kaini gidana.

Kallanta yai yace “kamar…….”

 Kaini nace, kome zan da rayuwata ba damuwarka bane.”

 Dauke kai yai yana kaita gidanta ta amshi key sannan ta kalleshi ta wuce ciki.

 Bala da gudu ya bude mata tana shiga tama Khalid text “You are Fired.”

 Yana fita ya gani, kallan gidan yai jiki a sanyaye sannan ya kira Dady ya fadamai.

 Dady cikin jin dadi yahau godiya, alokacin ya taho gidan.

 Zainab na zaune a falanta ta hade kafafunta tana kallan gida, komai na gidan bataso gani take komai anyi lalata dashi, kankame jikinta tai kawai tasa kuka.

 Dady wanda ya shigo ne ya kalleta cikin tausayi, tana ganinshi tasa kuka sosai, tausayinta ne ya kara kamashi yace “tashi mu wuce saboda ba’asan fita.”
 Kallansa tai tce “Dady anan zan zauna.”

Kallanta yai da sauri yace “bazai yiwu ba.”

Tace “to kaini gidan Aunty.”

Yace “wai akan me bazaki zo mu tafi ba?”

 Kallansa tai ta rasa me zatace, tuno da kalaman Khalid tai wai gidan iyayensa ne, Dady yace “mu tafi kinji?”

 Idanu ta runtse kafin ta daga kai.

 Haka Suka hada kaya suka wuce Abuja, tunda taje gidan magana ba hadasu take da Basma ba, kullum tana daki kamar yanda ta saba, Basma kuma ta rasa yanda 

zatai ta shawo kanta, Dady ne inyana nan yake kiranta falo shima da Basma su zauna duk da batama Basman magana ko ta mata a kalla tana amsamai in ya sako 

maganar Basman

Sai dai hakan ba karamin birgeshi yake ba duk da ba san zaman take ba akalla yanzu tana zama a falan in yana nan.


*******


A can bangarensu Goggo kuwa haka suk nufi kauye ganin ba yanda zasuyi dan dakyar goggo tai bacci ranar a cikin mota, gidan kawu shehu sukaje Goggo ta kalli 

Adam tace “karka fito da kayan tun kafin a tozartamu mu fara shiga tukun”
Haka suka shiga gidan Kawu shehu, matansa biyu da yaransa su goma sha daya, sai Sadiya dasuka barmai.

 Yana zaune a kan tabarmar kaba yana ta kankare kaho yaji ana ihun kawu Adam yazo.

 Shiga sukai cikin mamaki kowa ke kallansu, makota sai lekowa ake ta kanga, Goggo nasa kafa ta taka kashin kaza, da sauri ta matsa gefe tafara cewa 

“matsalata da kauye kenan, kaji ko ina…….”

 Kallan da Kawu Shehu da matansa suka mata ne yasata tai shiru, haka suka zauna, kowa na musu kallan mamaki, Kawu shehu yace “dama kuna raye? Ai mu tuni 

muka cire tarihinku.”

 Goggo tace “wato mutuwa kake so muyi ko me?”

Matarsa Delu tace “tunda danki yai aure kika bishi shekara hudu ko kafarki mun gani? Ko falen atamfa kin aiko mana? A matsayinmu na masu rike miki ‘ya.”

 Dariya Goggo tai tace “Adam ina taliyar da muka siyo dako ka shigo da ita.”

Kawu shehu ne yace “basai an shigo da ita ba, meya kawoku?”

Adam yace “dama Goggo ce zata dawo nan da zama.”

Delu tace “nan ina?
A wani dakin? Bayan mu kanmu gurin kwana wahala yake mana? Ruwa duk ya cinye mana gini?”

Kawu shehu ne yace “ki koma inda kika fito ki zauna nima yara rasa inda zasu kwanta mukeyi, lokacin da zaki tafi danace ki barmana gidanki me kikace? Hanani 

kikai a gabana kika saidashi ma abokina.”

 Goggo tasa dariya tace “wasa yakeyi kamar bakusan Adam ba, Sadiya nazo gani, tunda batanan bari mu wuce.”

 Har sun shiga mota Delu tace “taliyar, nan Adam ya bude mota dole ya cirota aka shiga da ita ciki.”

Suka ja suka tafi, haka Goggo suka je kano wajen gidan Zainab Goggo tana kallan gidan tana hawaye, Dakyar suka samu gidan haya daki daya a cikin katan gida 

mai dakuna kusan goma ban daki daya daga can kasan unguwar gidan Zainab suka zauna, Haka suka saida motarnan Goggo tasai yar mitsilar tv canjin suka sai 

kayan abinci suka zauna a gida.

Adam kam takaicin rashin mota sam yasa ko fita bayasanyi, wannan lamari na kona mai rai matukar gaske.

Banda fada shida Goggo kullum ba abinda suke a gidan, haka ya nemi majalisa yake zama, kudin mota kam an sashi a gaba sai ciye ciye akeyi kai kace bazai 

kareba.

 Duk gidan nan Goggo batawa kowa mutumci, dan garkame dakinta takeyi saboda batasan yara suzo mata kallo.

*********

Bayan wata uku……….

Wannan lokaci abubuwa da dama sun canza, su Nabila da Nusaiba an dawo, murna agun Zainab baya musaltuwa, Nabila kam taji bakin ciki dan jitai kamar ta je ta 

kashe Adam duk da batasan me ya mata ba amma haushin wulakanta hallacin Zainab yasata jin takaici matuka.

Su Khalid anyi Jarabawa, Zainab aka turowa takardun tai marking dan sai data turawa director din email akan ita zata dau ma’aikara dakanta, ganin yanda 

komai nasu yai kasa daga tafiyarta yasa yake lalabata, ta sanar kar wanda yasa suna sai dai ai amfani da numbers hakan yasa sanda tai marking batasan ko 

wanene na Khalid ba, sai dai akwai takarda daya wanda ita kanta sai datai bincike a google kafin tai marking dinshi saboda tsabar fasahar da aka rubuta ya 

wuce tunaninta.

 Kusan duk kwana biyu sai tayi waya da Umma sosai wannan wayar ke debe mata kewa, har Allah yai ta kammala iddar ta, sannan ta tura ranar interview ga 

wadanda suka ci sannan tahau shirin dawowa.

Khalid dake zaune cikin shagon dayake aiki ne sako ya shigo mai, baki ya sake sosai dan bai taba yin jarabawa ance yaje interview ba sai wannan, wayar ya 

kurawa ido yana kallan sakon dan ya kasa gasgata abinda yake gani…….


Related Articles

Leave a Reply

Back to top button