NOVELSUncategorized

A GIDANA 38

{38}


 Tana zaune tana kade sauran dake ta mata yawo akai, haushi duk ya bi ya isheta na rashin wuta da tun shekaran jiya wutar su ta samu matsala, wani uban 



tsaki taja data kalli taliya da manjan dake gabanta a roba wanda har yayi sanyi ta kasa ci saboda takaicin sauro.

 Kofa ta bude ta hau korar sauran, tanaji makotanta nata hira da shewa a waje, wani uban tsaki ta sake jaa tace “ka rasa uban me suke banda zaman gulma.”

 Buta ta dauka zata shiga bandaki, da sauri Asabe ta mike ta warce butarta tace “Tsohuwa wannan butar tawa ce”

 Kallanta tai tace “wace tsohuwar?”

 Asabe tace “to yarinya wannan butar tawa ce.”

 Haushi ya kara tike Goggo ta waiga taga bataga butarta ba tace “to uban waye ya daumin tawa butar?”

 Asabe tace “sai ki tambayi na gidan amma ba ni ba.”

 Ta ja kafarta ta bar gun, Goggo ta hau neman butarta sai dai bata ganta ba, nan ta matso inda suke hira tace “uban waye ya dau min buta?”

 Kande ta mata wani kallo tace “sai ki tambayi yaran da kika kira da danki tunda kinfi kowa sanin ba mai dau miki buta anan.”

Takaici ya kama Goggo ta juya rai a bace, waje ta leka, Adam ta gani suna zaune a kujera suna hira, rai a bace tace “Adamu!”

 Kalamta yai yace “Goggo.”

 Ka mikon butar nan ko kuwa?
 Butar dake gefensu ya kalla sannan ya mike ya dauko ya kawo mata, yana shigowa tace “wuce ciki yanzu zan fito.”

 Yace “hira muke.”

Ka wuce ko sai na makeka?

 Fuska ya hade ya shiga ciki, taliyar data bari ya jawo ya juya ya hau ci, bayan gida ta tsaya yi hakan yasa ya cinye taliyar kafin ta fito, yana lokar 

karshe ta bude labulen ta shigo.

 Kallansa tai tace “uban wa yace kacimin abinci?”

 Yace “au zakici? Gani nai tun dazu kika ajiye shi gashi haryai sanyi.”

 Ranta a matukar bace ta karaso tace “ni wai dan Allah yaran nan sai yaushe zakai hankali? Gaba daya ni bantaba ganin mutum wanda bashi da tunani ba irinka, 

kanyar mana da kudi ka kala min karyar ka bani, yanzu yar dubu ashirin din da muka siyo kayan abinci muke cancanawa kaci naka dazu amma yanzu ka tasa nawa 

ka handame.”

 “Yahkuri Goggo na dauka baci zakiyi ba”
“Ko ba ci zanyi ba ai ka bari nace bazanci ba ko?”

 Nadai baki hakuri ya isa haka nan.

 Ganin zasu sake fadam da kullum suke ciki yasa ta zauna ta kalleshi tace “yanzu Adam haka zamuyi ta zama? Ga kudi mun cinyesu ga nan da wata biyu za’a 

amshi kudin haya? Banda wahar rashin abinci da muke neman shiga?

Shiru yai yana kallanta yace “ Goggo na rasa yanda zamuyi duk inda nakai takarduna ko nemana yin jarabawa basayi.”

 Goggo ta baza tagumi tace “nikam da alama rayuwarmu tai kusan zuwa karshe.”

 Kallanta yai yace “karki damu Goggo ina tunanin zuwa gun Zainab ta taimaka min.”

 Wani wulakantacen kallo tamai tace “Zainab? Lalai bakada hankali, inda raban an kulleka daga nan kaga shikenan ni na huta ai.”

 Fuska ya hade tace “ni fita ka siyo mana maganin sauro.”

Mikewa yai ya fita rai a bace.


*********


Yau ake aka kira sababbin ma’aikata, tun safe take tunanin yanda zasu kare ita da Khalid dan tana tunanin abinda zatamai ta rama.

 Fitowa tai ta nufi inda aka kirata akan isowarsu.

 Tana shigowa suka fara gaisheta, kallansu ta hau yi daya bayan daya sai dai me? Gani tai sun cika su takwas ba tare da taga Khalid ba.

 Juyowa tai ta kalli Ramatu wacce itace ta taho dasu, tace “su kenan?”

 Ramatu tace “eh.”

 Kallansu Zainab ta sakeyi, a hankli ta fara takowa daidai inda suke, hartazo kan ta takwas din, mace ce yar gayu taci kwalliya sosai, makeup yaji a 

fuskarta, tana da kyau sosai ga diri, Zainab ta kalleta daga sama har kasa sannan tace “ya sunan ki?”

 Cikin gayu tace “Afreey.”

 Afreey? Zainab ta maimaita sannan tace “are you telling me Afreey ne sunanki?”

 Da sauri tace “sunana “Safeena Sani amma Afreey ake ce…….”

 Kafin ta karasa taga tayi gaba, ranta a matukar bace tai hanyar kofa.

Ramatu ce ta matso da sauri tace “Director ance ke za……”

 Kallan data mata ne yasa tai gum, kofar Director ta nufa tasa hannu zatai knocking taji yana waya “ai Ranka ya dade karka damu, zan sata a labaran da 

takeso, ahhh bakomai mune da godi……..”ran Zainab a matukar bace bude kofar Director da karfi.”

 Yana ganinta yace “to bari na kira.”

 Kashe wayar yai ya kalli Zainab yace “Hajiya kin raba musu aikin?”

 Kallansa tai tace “me kake shirin yi?”

 Name kenan?

Wacce yarinyar me take anan?

Ohhh Afreey? Am sorry dama yanzu nake shirin fada miki yar kanwar Senate Musa ne, ai kinsan shi ko?”


 Wani banzan dariya tai tace “sai a kai ya?”

“Ohh to shine take san aiki a gidan tv shine akin magana, nasan kema zakiji dadi tunda yanzu duk abinda muka je nema zamu iya amfani da ita.”


 “Yaran dayai interview a maimakonta fa?”

Wa kenan? 

 Wani kallo tamai yace “ohhhh yaran da kuka danyi fada? Naga kamar bakya sansa shiyasa nai replacing dinsa da ita, sannan shi na duba maga bashi da wata 

hanya balle ya dawo yace mun cuceshi.”


 Kamar zatai magana kawai ta fasa, gaban desk dinsa ta nufa tasa hannu ta dau biro ta jawo paper.

Kallanta yai yce “karki damu yarinyar akwai hazaka.”

Bata kulashi ba sai data gama rubutunta sannan ta tura mai gabanshi ta ajiye mai biro da karfi.

 Kallanta yai da sauri bayan ya kalli takardar yace “wani irin resignation letter? Zainab menene hakan?”

 Hannunta ta daura daya akan desk din sannan ta kalleshi tace “kai processing dan na ajiye aikina daga wannam lokacin.”

 Hankalinshi a matukar tashe ya dawo ta gabanta yce “Zainab meke faruwa haka? Kinfi kowa sanin duk inda muka kai takarda sai suce dake zasuyi aiki, me kike 

nufi damu?”

 Kallansa tai tace “dama ina da matsayi?”

 Wani irin zance ne wannan bayan kina ganin komai sai da amincewarki nake?

 Wani irin dariya tai na takaici tace “da amincewa ta? Sanda kake kawo wadanda suka maka ina sani?”

 Yace “wai akan Afreey ne? Naga yaran can ba sanshi…….”

 Ranta a bace tace “ko na soshi ko karna soshi meye nawa a ciki? Aiki yazo nema ya samu saboda iliminsa? Meya kawo zancen zabi anan? Sannan in maganar zabi 

ne zan iya sanar dakai, kaf cikin wadanda sukai interview shi ne mutum na farko da na fara tabbatar da gwaxanda da cancantarsa, sannan me? Ka koreshi saboda 

ka kawo yar uwar wani senate?”


 Wannan yrinyar da badan badan ba da……
Kallanta yai yace “to yanzu kiyi hakuri za’amai text yazo kinga sai mu dau mutum 9 kenan.”

Meye dalilin da zaisa mudau 9 bayan 8 mukai?

 Da sauri yace “Haba Zainab bazaki daga min kafa ba? Nayi laifi nayadda na dauka sai dai nima ki barta aman.”


 Shiru tai kafin tace “naji kasa amai text.”
Tana kaiwa nan taja takardar datai rubutu a jiki ta fita.

 Da hararar ya bita yace “yarinya karama ta nemi maidani kaninta.” Kwafa yai sannan ya danna ma secretary dinsa kira.

 Yana shigowa ya sanar dashi a kira Khalid.

Komawa office dinta tai ta zauna tare da shan ruwa ta rufe idanunta.

 *********

Khalid na garaje wayarsa tai kara dauka yai sai dai yanajin kiran na waye ya fito daga kasan mota da sauri, nan yace gashi nan zuwa.


 Da sauri ya nufi gida cikin tsananin farin ciki dan da har jikinsa yai sanyi ganin ba’a kirasu ba.

Wanka yai ya shirya sannan ya shiga ya sanar dasu Umma.

 Dadi agunsu Umma kamar me, nan suka hau zabgamai addu’a ya fito ya nufi tasha.


 Tayi sallah kenan tana duba wasu takardu taji knocking.

 Ramatu ce ta shigo tace “Director suna jira.”

 Okay ganinan.

 Takardunta ta mika mata tace “yi photocopy din wadannan.

 Da sauri ta amsa sannan ta juya, wayarta ta dauka ta kira Nabila.

 Nabila  ta dauka tace “Aunty dan Allah anjima muzo?”

 Ina?

Gun aikinki, sai mu dawo tare.

 Shiru tai kafin tace “shikenan.”
Tana ji suna ihu a tare ita dai ta kashe wayarta ta mike.

 Tana bude kofar ta ciki yana bude kofar ta waje.

 Kallansa tai sannan ta dauke kai ta kalli ragowar dake gun.

 Da sauri Khalid ya karaso, suma suka mimike.

Suka matso inda take, Ramatu ce ta mika musu takardun datai photocopy kowa yadau daya sannan ta kallesu tace “muje”

 Nan tai gaba suka bi bayanta zuwa broadcast room.

 A lokacin ama gabatar da shiri, haka suka tsaya sukaga yanda ake, nan suka nufi control room, nan ma sukaga yanda akeyi, da yanda ake editing da sauransu.

 Sai dasuka gama sannan ta sake yima kowa gwaji dan sai sun gama yimusu training an gwada sosai sannan zata san inda zata sa kowa.

 Juyawa tai ta nufi office dinta.

 Wani producer ne ya fito daga bakin kofa ya mika ma Khalid flask yace “plz kaima Director Zainab.”

 Amsa Khalid yai ya juya ya wuce, Afreey ce ta bishi da wani kallo mai wuyar fassarawa.

 Sai da Ramatu ta nuna mai inda zaibi yaje office dinta.

Knocking yai sannan ta bashi izini ya shiga, tana zaune a kan computer desk, ta sa glass tana aiki, bata dago ta kalli wanda ya shigo ba har ya karaso inda 

take.

 A hankali ta dago tare da kallansa, ganin Khalid ne yasa ta maida danta kan abinda take tace “ ya akai?”

Ajiye mata flash din yai a kusa da ita sannan yace “aikoni akai.”

 Kallan flash din tai sannan ta kalleshi, shima kallanta yai.

 Juyawa yai zai fita,  har yayi taku biyu dai kuma ya tsaya ba tare da ya juyo ba.

 Kallansa tai tace “me? Akwai wani abu ne?”

 Juyowa yai yce “da akwai amma yanzu babu.”

 Zare glass din tai tace “baka da abinda zaka cemin?”

 Kallanta ya sakeyi yace “no, I don’t think i have.”

 Tace “okay shikenan.”

 Glass dinta zata maida yace “da zan tambayeki how have you been? To amma energy din ki da na gani ranar interview yasa nasan bana bukatar tambayar.”

 Kallansa tai tace “Masu gida ya gida?”

 Yace “Gidan mu normal, ya naku gidan?”

 Bata tanka mai ba ta cigaba da aikinta.

 Shima bai nemi karin magana ba ya juya ya fita.

 Yana fita ya nufi inda ya barsu.

 Afreey dake tsaye daga tsakiyar corridor ya kalla, dauke kai yai kamar bai ganta ba, har ya wuceta tace “Khalid!”

 Bai juyo ba sai dai yadan tsaya, tace “Khalid!”

 Juyowa yai ya kalleta yace “Oh Safeeya!”

 Kallansa tai tace “pretending kake baka ganeni ba ko kuma dagaske kake?”

 Kallanta yai baice komai ba kawai ya juya yabar gun.

 Da kallo ta bishi cikin wani yanayi, waya taba tunani zata tsinci Khalid anan? 


Khalid ne ya koma suka cigaba da abinda suke, ransa yayi matukar baci duk juyowar dazaiyi zai ga idan Afreey akansa.


*********

Cikin tsananin murna Nusaiba da Nabila suka shiga mota, kaya iri daya suka saka, sai murna suke yau zasu fita dan sun gaji da zaman gida.

 Har suka isa suna hira kai bakace sune masu fada ba.

 Mamman ne yace “yau lalai take sallah, haryanzu ba’ai fadan gadan ba?”

Dariya Nabila tai tace “dama can wannan ce uwar neman fada.”

Nusaiba tace “ni ko ke?”

 Dariya sukai dukansu Mammab yi parking.

Nabila ce ta kira Zainab, sai data kusa katsewa ta daga, tace “Aunty munzo.”

 Ku shigo zan turo a karaso daku.”

 Cikin jin dadi suka fito.

 Suna isa sukaga wani daga kofa nan suka sanar da inda zasu je, security din yace su jira ya tambayo.

 Bai dade ba sai ga wanda zainab ta turo nan, murna kamar me suka taho suna murmushi.

 Haka suka shiga ciki.

 Kamar da wasa Nusaiba ta hango wani kamar Khalid.

 Da sauri ta juyo ta kalli Nabila tce “Nabila duba mun can kamar Uncle dina.”

 Uncle dinki? Kanin Mumy?

 Haushi ya kamata tace “yaya na to.”

Yaya? Ina kika ga yaya?”

 Ran Nusaiba a bace tace “bashi ma.”

Ta dago taga bata ganshi ba, da sauri tabau waige waige.

 Nabila ta sa hannu ta jata  tce “inka yaya ne in ma Uncle kya ganshi daga baya.”

Har suka isa Nusaiba bata bar waige ba.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button