NOVELSUncategorized

A GIDANA 39

{39}

  Khalid na kammala abinda aka sashi ya mike, ganin masu aikin rana duk sun tattafi yasa yadau jakarsa ya fito.

 Office din Zainab ya kalla, a ransa yce “wannan agoggon ko ta tafi?” Fitowa yai ya sauko kasa, yana fita daga gate yaji ance “Khalid!”

 Zabgegiyar mota dake gefensa ya kalla, Afreey ce a cikinta, kansa ya kauda ya cigaba da tafiyarsa, binshi take a hankali tace “Khalid!”

 Tsayawa yai ya kalleta yace “Safiyya meke damunki wai?”

 Magana nakeso muyi.

Kallanta yai yace “in inada ra’ayi kenan ko?”

 Nasan in bakada ra’ayin abu bamai saka canzawa, sai dai dan Allah ka tsaya muyi magana.

 Kallanta yai, ya kalli wayar hannunsa yace “minti uku na baki, menene?”

 Tana san cewa ya shigo amma tasan bazai taba shiga ba tunda maganar ma daya ta kare.

 Kallansa tai tace “ranar……..”

 Kallan daya mata ne yasa ta yin shiru, kafin tai murmushi tace “nasan duk abinda zan fada bazaka yadda ba, sai dai Allah ranar…….”

 Kallanta yai yace ” can you stop talking about that?”

 Tace “ka san fatan da nake a koda yaushe akan Allah ya hadani dakai nama bayani?”

 It doesn’t matter to me, koma me ya faru a wannan lokacin bashida amfani a gareni kinsan me nake nufi in na fadi haka

 Yana kaiwa nan yai gaba, da kallo ta bishi har sai da ya kulle.

********

 Nusaiba na shiga ta kalli Zainab tace “Aunty naga wani kamar Uncle a can.”

 Ta fada tana nuna mata inda ta ganshi, Uncle? A gidan wa kike da uncle anan?

 Nabila ce tasa dariya tace “Kanin Muny ya fara aiki anan ai.”

 Kanin ta?

 Zainab cikin mamaki ta tambaya.

Nusaiba cikin masifa tacewa “Nabila bansan wulakanci.”

 Gwalo Nabila ta mata tai gaba dasauri tana dariya.

 Nusaiba ta kalla tace ” waye Uncle?”

 Nusaiba tace “Uncle daya miki driver.”

 Uncle? 

 Nusaiba tai kasa dakai wai ita a dole kunya.

 Gaba Zainab tai ganin batada lokacin wannan shirmen, mota suka shiga sunara fada Nabila tace “in ba neman suna ba na tabbatar ko a hanya ya ganki bazai 

ganeki ba.”

 Nusaiba tace “in bai ganeni ni ba ni sai na tuna mai ai.”

 Wata dariya Nabila ta saki wanda ya kara tunzuro Nusaiba.

 Zainab ce ta kallesu tace “ya isheni haka nan, Allah yasa insaki jin bakin wata.”

 Nan suka shiru, suna hararar junansu.

**********
Washegari….


 Goggo ce ta zazzage lalitarta, naira dari ne a ciki kacal, wani irin ajiyar zuciya ta saki mai ban tausayi, ga wuta amma ko tv bata da niyyar kunnawa, 

saboda damuwar dake cikin ranta yafi karfin kallo.

 Cikin ta ne yai wani irin kara, fitowa tai tsakar gida ta nufi waje.

 Sai dai yau Adam baya ma kofar gida, haushi da takaici ya kara kamata, haka taje gun mai shayi ta sai bread na naira hamsin sannan ta koma ta hada tea, ta 

dau gwangwanin madara ta bude taga ba komai, yaushe suka siyo madarar? Milo ta bude shima taga ba komai, lalai Adam ne ya juye, ranta a tsananin bace ta sa 

sugar ta shaku ruwan buno da bread.

 Zama tai tana tunanin abinyi.

 Wayarta ta dauko da sauri tana san kiran Hajiya bilki, sai dai jitai ana ce mata batada kudi, haushi ne ya kara tiketa ta ajiye wayar ta kwanta kamar mara 

lafiya.

 Adam na zaune suna musu a babbar majalisa, soron wani abokinsu suke zuwa susa kallo suyi ta musu ana hira da shewa, kallansu yai yace “wlh Allah da gaske 

nake.”

 Kai malam karka raina mana hankali, wannan ce matar taka.”
Adam ya kalli Zainab dake jikin Tv yace “wlh da gaske nake.”

 Dariya suka sheke mai da ita, daya daga cikinsu yace “in har kai mijinta ne to ni dan gidan Dangote ne.”

 Adam a hasale ya tashi yace “wai ya zan tayi muku rantsuwa kuki yadda, da na dauko wayata wlh dana nuna muku.”

 Kallan jikinsa suka fara yi, wani yace “Malam kai ka maidamu kananan yara in bacci kakeji kai maza kaje ka kwanta.”

 Dariya suka sheke mai dashi, ranshi yai matukar baci ya fito rai a bace, ya shige adaidaita.

 Sam baima damu da kayan dake jikinshi ba balle silifas din dake kafarsa.

 Kofar tv station din su Zainab yai parking, kallan dan adaidaitar yai yace “bari na shiga na amso ma kudi.”

 Ransa a bace yace “Malam bansan wulakanci, bani kudina.”

 Adam yace “yanzu zani gun Matata na amso maka.”

Ciki yai da sauri, Security ne ya tareshi yana tambayarsa ina zashi.

 Adam yai dariya yace “baka ganeni ba? Mijin Zainab ne Adam.”

 Kallansa Security din yai sai yanzu yaga kamar sa amma meye hakan? Ya fada a ransa.

Adam ne yai ciki, duk inda yai kallansa ake ana mamakin waye wannan.


 Haka ya shigo duk inda yai kallansa ake suna gulmar shigarsa dan duk sun sanshi.

 Kan kace me zance ya yad’u akan mijin Zainab yazo, kamar an koroshi daga daji.

 Khalid na zaune yana aikin da aka bashi, zancen yazo mai, cikin mamaki yace “mijinta? Adam?” Wata yar iska ya furzar yana tunanin meya zo yi? Da sauri ya 

mike ya nufi office dinta.

 Zainab na zaune tana tattare takardun da zasu presentation a wani plastic company suna san suyi aiki dasu.

 Knocking taji, kallan kofar tai tana tunanin ya kamata ta samu secretary dan dama an bata a farko itace bataso saboda gani take westing din kudin su sukeyi 

gwara tai abinta da kanta.

 Izini ta bada ya tura kofar ya shiga, yana shiga Khalid na shiga corridor din.

 Mutane ya gani ana leke ana gulma, juyawa yai ya koma ya zauna.

 Tsananin mamaki ne ya kamata har ya shigo bata ce mai komai ba.

 Adam yana ganinta yai murmushi yace “Honey!”

 Karasowa yai inda take yana cewa “Yaushe raban dana ganki.”

 Kallansa tai tsaf sannan tace “Me kake anan?”

 Honey wallahi ganinki…….

 Fuskarta ce ta canza sosai bacin rai ne ya bayyana a cikinta karara, yatsa ta nuna mai rai a bace tace “don’t you dare call me with that name.”

 Tsoro ne ya kamashi, dan yanda yaga yanayinta ya canza gaba daya sai yaji ya kasa magana.

 Kallansa tai bayan ta mike tace “Uban me kake min agun aikina?”

 Ho….Zainab……

 Cikin tsawa da fada tace “me ka daukeni? Wulkantani kazo yi ko mutuncina kazo ci.”

 Kai ya shiga girgizawa da sauri yace  ” ba haka bane wlh, bansan ya akai ba na ganni a bakin nan.”

 Wani murmushi tai tare da daga gira daya ta bacin rai tace “ka dauka bansan me kazo yi bane? Kazo ne ka ci mutuncina ka nunawa mutane bama tare yadda zan 

zama abin kwatance da wulakanci a cikin mutane.”

 Shiru yai jikinsa duk yai sanyi, tace “ba laifinka bane, kome kai laifina ne da ban sa an kulleka ba bayan abinda ya faru.”

 Komawa tai ta zauna tace “fita!”

 Juyawa yai jiki a sanyaye kamar an mai duka, haryakai kofa ya juyo yace “Ki taimaka min dana mota.”

 Kallansa tai yace “adaidaitar dana shiga ban biya ba.”

 Tace “banaji wannan ya dameni, ka fita ko sai na sa an fitar dakai?”

 A hankali ya bude kofar ya fita, suna jin an bude kofa yan gulma kowa ya juya, ana kallan yanayinsa kowa da gulma dake cinsa.

 Adam na fita suka shigo, daga gefen Khalid suka tsaya suna dariya, wani yace “wannan anya tana bashi abinci ma?”

 Dariya wani yai yace “dama duk wanda ya auri wannan ai ya auri rashin kwanciyar hankali”

 Afreey dake kefensu tace “mijinta ne?”

Ramatu tace “eh.”

 Cikin mamaki Afreey tace “amma yazo a haka?”

Dariya sukai wani yace “ina kwanciyar hankali da alama daren jiya duka tamai.”

Khalid wanda ransa yakai matuka gun baci yana dannewa ji yai wani yace “kai harna tausayamai, wannan da alama ko abinci sai ya tambayeta yake ci.”

Desk dinsa ya daka da karfi wanda yasa kowa kallansa, murmushi ya musu yace “am trying to see how strong i am.”

Kallan mamaki suka mai zasu cigaba da gulmar sukaji yace “Ahhh ni yaushe ma akace za’ai meeting din?”

 Ramatu ta kalli agoggo tace “bata fada mana ba, wazai tambayo ta.”

 Da sauri kowa ya watse kai kace korarsu akai.

 Ramatu ta kalli Khalid tace “ko zaka tambayota?”

 Mikewa yai ba musu.

 Afreey tai shiru tana tunanin yanayin daya faru a wannan lokacin, tabbas dan a tsaya da maganar ya daki desk, meye nashi a ciki?

 Knocking yai, ta bashi izini.

 Bata dago ba sai daya maida kofarya rufe.

 Dagowa tai ta kalleshi, tace “ya akai?”

 Karasowa yai kawai taga yaja kujerar dake gabanta ya zauna.

 Sake kallansa tai tace “ya akai?”

 Kallanta yai kamar zaiyi magana sai kuma yai shiru, murmushi tai tace “kaganshi?”

 Hmmm

Murmushi tai tace “it seems like kowa ya zama busy saboda hakan.”

 “Are you okay?”

 Kallansa ta sakeyi tadan karkatar dakai kadan tace ” kai da ka saba ganewa sai ka duba ka gani, am i okay?”

 Dan matsowa yai yana kallanta, juya kai tai gefe saboda batasan kallan, komawa yai ya zauna yace “you are not.”

 Da sauri ta kalleshi tace “mene?”

Yace “then ke kina tunanin u are?”

 Tace “sosai, meka daukeni? Kana tunanin karamin abu kamar wannan zai sani damuwa?”

Dan hannunsa yasa ya shafi wuyansa, harararsa tai tace “kana nufin zai sani kenan?”

 Yanzu ma baice mata komai ba sai dai ya mata kallan eh.

 Haushi ne ya kara kamata ta hade fuska tace “naji ya sani, jeka kacemusu bayan lunch xamuyi  meeting din.

Okay yce sannan ya mike, haushi ne ya kara dan kamata ganin ya mike hankali a kwance tace “mikomin ruwa a fridge.”

 Juyowa yai ya kalleta, alama tamai daya miko mata, kallanta yai sannan ya bude fridge ya dauko ya zo gabanta ya ajiye, har ya juya tace “saura cup.”

 Kallanta ya sakeyi sannan ya dauko yazo ya ajiye mata, harya sake juyawa tace “ohhh ga wani file can a saman shelf daukomin.”

 File? Ya fada yana kallanta, tace “eh.

Dauko mata yai yazo gabanta ya ajiye yana kallanta.

 Juyawa yai tace “Ohhhh bana san shan ruwan nan zo ka siyomin fanta a shagon kasan layi.”

 Takowa yai yazo inda take, tana guntse dariyarta ta dauko 1000 ta mika mai, amsa yai sannan ya kalleta yana juya kudin sannan ya mika mata.

 Kallansa tai tace “na meye?”

 Yace “Ohhh bakya san ruwa ya kamata kije ki siyo fanta.”

 Fuska ta tsuke tace “kana nufin na fita na siyo?”

Kudinta yakara mika mata yace “ba wannan a cikin aikina.”

 Tace “in babu senior dinka a gun aiki tasa ka by right kuma dole kayi.”

 Dan ajiyar zuciya yai yace “by right zanyi amma in har bani da abinyi kenan.”

 Ya ajiye mata kudin sannan yace “yanzu na fahimci you are okay.”

Kallansa tai tace “Sam baka biyo halin Umma da Abba ba.”

 Shima kallanta yai yace “kema baki biyo halin Dady ba.”

 Wani kallo tamai tace “bakinka baya rasa abin fad’a ne?”

 Yace “in har naki bai rasa ba.”

 Hade rai tai tace ” mene?”


 Bai bata amsa ba ya juya ya ya fita.

 Yana fita ta kalli kofa, sannan ta kalli kudin.

Khalid na fita ya samu kansa da dan murmushin da baisan daga ina ya fito ba.

Afreey dake nesa a tsaye ce ta kalleshi sannan ta tako inda yake.

 Kallanta yai bayan ya hade fuska yana neman wucewa.

 Tace “menene tsakaninku?”

 Kallanta yai kamar zaiyi magana sai  kawai yai gaba.

 Shiru tai tana kallan office din Zainab.


********

 Adam na fitowa mai Adaidaita ya cakumeshi, yace “ina kudina?”

 Adam ya kalleshi yace “dan Allah kayi hakuri yasin ficika bana magani.”

Ficika?

 Adam da sauri yace “eh wlh.”

 Kallansa yai bayan ya sakeshi ya kalli layin gani mutane ta ko ina yace “ba komai, na yafema kana da yanda zakai ka koma?”

 Da sauri Adam yace “a’a.”

 Nan Yace “muje na maidaka.”

Godiy Adam ya shiga yi harya shiga motar, suna tafe yanata tunanin abinda Zainab tamai, zuciyarsa duk ba dadi gashi sama da kasa ya nemi Sadiya dan ya ci 

mutuncinta ya rasa.

 Suna zuwa lungun mai adaidaita ya tsaya ya cakumo Adam ya jawoshi waje.

Da sauri Adam yace “Lafiya?”

 Naushin daya sakarmai ne yasa shi faduwa kasa, gefen bakinsa ne ya fashe ya kalleshi zaiyi magana ya jawo shi ya kara kaimai wani naushin.

 Yazo mai na uku Adam ya mike yafece a guje…….


Ni kaina gudunsa yasa na kasa binsa????????????‍♀

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button