NOVELSUncategorized

A GIDANA 40

{40}


 Agoggon dake manne jikin bango ta kalla ajiyar zuciya tai sannan ta tattara takardun dake kan desk dinta sannan ta mike ta fito.

 Tasa hannu zata murda kofar taji wani a cikinsu nacewa “kuna tunanin zata iya zuwa? Yanda mijin nan nata ya kunyatata?”Dariya taji wani na cewa “da alama neman silhu yazo yi, tunda mukaga takai wannan lokacin dakyar ta iya zuwa.”

“Yoo ina kunya zata barta tazo.”

 Khalid na jinsu sai dai baice komai ba, kofa ta bude da iya karfinta.

 Kallanta sukai a tare, kallansu tai sannan ta karasa ta zauna.

 Takardun hannunta ta watsa jikin dogon table din meeting din.

 Dukansu sunyi gum kowa na kallanta, Afreey kam gaba daya hankalinta nakan Khalid wanda ke zaune.

 Kallansu tai sannan tace “da alama kun samu abin tattaunawa tunda gashi nayi late amma it seems no one notice that.”

 Shiru sukai, kallan kowa ta farayi tana tambayarshi abinda yai daga zuwansa har wannan lokacin.

 Ganin dukansu sunyi shiru yasa Khalid ya kasa cewa ga abinda yai.

 “Bakuyi abinda ya kamata kuyi ba amma kowanenku ya iya shiga maganar da bata dameshi ba?”

 Kasa sukai da kansu, haka ta musu bayanin abinda za’ai sannan batare da ta sake tambayar kowa wani abu ba tana gamawa ta hada kayanta ta mike, juyowa tai 

ta kallesu tace “sannan wanda yazo bani da hadi dashi kamar yanda banida hadi da d’aya daga cikinku.”

 Gaba daya baki suka sake har ta rufo kofar sannan suka fara kallan juna, Ramlatu ce ta mike ta fito daga meeting room din.
Afreey ta kalli Khalid wanda ke zaune bashi da alamar tashi.

 Waya ce tai kara da sauri wani ya daga, Zainab tace “a cikin rookie din nan, kace mutum daya ya fito muje Plastic Company.”

 Tana kaiwa nan fa kashe wayarta.

 Kallansu yai, yace “mutum daya ya shirya zasu fita da Dire……”

Ai kafin ya karasa wadanda ba sababbin dauka ba sun bar gun, Afreey ce tace “me za’ai?”

 “Bansani ba tadaice yanzu.”

 Shiru sukai, wannan yace cikinshi na ciwo wannan yace toilet zaije.

 Khalid ne yace “bari naje.”

Da sauri Afreey tace “bari ni naje.”

 Kallanta yai yace “kinyi submitting report dinki ne?”

 Kasa tai dakai ya juya ya fita.

 Zainab wacce dama da zata taho yau dakanta taja motar saboda tasan akwai inda zata.

 Knocking yai ya shiga, kallansa tai sannan ta mike ta dau jakarta batace komai ba tai hanyar kofa.
Ganin haka yasa shima ya fito.

 Gaban motarta suka je ta mika mai key sannan ta shiga ta zauna, yayi mamakin data zauna a gaba kenan tasan ba a matsayin driver zai ja ta ba kenan?

 Shiga yai suka dau hanya bayan ya tambayeta inda company din yake.

 Kallansa tai taga yanda ko magana bai sake yi ba tunda yaji inda zasu, duk da tasan ba magana ce dashi ba amma at least ta dauka zai tambayeta abinda ya 

faru dazu.

 Kallansa tai tace “wannan had’a ran fa?”

 Bai kalleta ba yace “ni?”

 Ya fad’a tare da dan kallanta, tablet dinta na hannunta tana duba slides na presentation dinta tace “eh”

 Baice komai ba ya cigaba da tafiya, kallansa ta sakeyi tace “haushi kaji na had’aku duka na muku fad’a?”

 Kallanta yai yanzun ma ba kallanshi take ba, gangarawa gefen titi yai ya juyo ya kalleta kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa.

 Itama kallansa tai tace “fadi, ba shi bane?”

Yace “as a director wacce ake respecting kina tunanin dan kin mana fad’a wani abin ne? As we are all your subordinate?”

 Tace “then?”

 “Ba hurumina bane I don’t think inada damar magana.”

 Murmushi tai tace “kai din? Tun yaushe kake magana akan abinda ba huruminka ba?”

 “Hakan ne dalilin dayasa na daina daga dazu.”

Dazu? Kenan dan nayi maganar rabuwar aurena da Adam ne ya saka?

 Kallanta yai baice komai ba, tace “bakai kace na fada ba?”

 Ni? Ya tambaya cikin mamaki, tace “eh muje banasan African time.”

 Jan motar yai yana cewa “yaushe?”

 Tace “dana aikeka ka siyomin abu me ka cemin?”

 Bata jira yace wani abu ba ta fara fadamai abubuwan da za’ai fadamai abinda zaiyi agun.

 Shima bai kara neman ji ba dan shidai yasan basuyi wannan maganar ba.

Har suka isa bai sake magana ba itama ganin bashi da niyyar magana tana gama mai bayani tai shiru.


******
Kan kace me labari ya karade gaba daya tv station dinsu.

 Tunda Ramatu ta fadawa Director Kabir haryanzu bai ce komai ba dan gaba daya hankalinsa ya tashi.

 Sai can ya daure yace “me ya rabasu?”

 Tace “bansani ba nima.”

 Shiru yai ransa a matukar bace yace “yanzu in abu ne wanda zai jawo mana matsala da zarar ‘yan jarida ko mujalla sunji labari shikenan mun shiga uku.”

 Hankalinsa a tashe ya kori Ramatu ya dau waya ya kira Zainab.

 Tana kokarin shiga company din wayarsa ta shigo, tasan maganar da zai mata, saboda tasan daga sanda ta bude baki tai maganar tafi kowa sanin abinda zai 

biyo baya, ba abinda ta tsana a rayuwarta irin ta zauna cikin mutane tana yaudararsu, tunda ta dawo daga Abuja take zargin kanta da yaudara da karya tunda 

duk kowa kallan matar Adam yake mata, mexai faru a sanda wani yaji daga waje? Bata kara jin haushin kanta na boyewa ba sai da sukai magana da Khalid ta 

fahimci menene aikinta.

  Haka ta wuce ciki bayan ta kashe wayarta.


*********

Goggo na share falo saboda ta kwana biyu ko sharar ma batada lokacin yi saboda damuwa, yaukam tana kwance taketa jin kanshin miyar dage dage, gaba daya 

yawunta ne ya gama tsinkewa, ganin abin na damunta ne yasa ta mike ta hau shara.

 Tana bakin kofa tana kwashewa sai ga Adam.

 Tsallakawa yai ya wuce, ta ajiye abin sharar ta kalleshi tace “wai ni sai yaushe zaka dinga sallama in zaka shigo guri ne?”

 Karasa wa yai ya zauna akan katifa  yace “ni abinda ke damuna ya isheni dan Allah karki kara mun da wani.”

Juyowa tai rai a bace tace “gidan uban wa ka kaimana madara da milo?”

 Kallanta yai, da sauri tace “meya sameka?”

 Ta fad’a tare da tasowa da sauri zuwa inda yake, kwanciya yai yace “ki bari kawai Goggo saura kadan a halakani, daga shiga adaidaita ba kudi”

 Kallansa tai tace “ina kaje? Ki meya kaika shiga mota ba kudi?”

Gun Zainab……

Zainab?

Da sauri ta kalleshi tace “bakada hankali?”

 To ya kikeso nayi, ni gaba daya wannan zaman ya isheni, sam abokaina basa darajani, da duk inda naje girmamani ake yanzu ko matsayin magana ta gaskiya ma 

bani dashi, ni na gaji wlh.

 Kallansa tai kamar ta makeshi sai dai kanshin dage dage ya gama sa karfinta ya tafi, tace “wato kaidai wlh ban taba ganin mutum wanda baya nazari irinka 

ba, ko uban me Zainab ta gani anan harta aura ni bansani ba.”

 Fuska ya hade yace “koma meta gani shine silar jin dadinki kema.”

 Mikewa tai tace “ni banida lokacin haukarka, yanzu ka mike ka fita ka nemo mana na abincin rana.”

A ina zan nemo? Ko ana rabo a makota ne?

 Wani kallan takaici tamai tace “eh duk gidan da ka gani kaje kace kazo amsar rabanka.”

 Dariya yai jin zafin bakinsa ne yasa yace “Goggo mekila daukeni me?”

 Sai na fada? Akai a shashashu ma kaine sarkinsu.

 Ransa ne ya baci ya kwanta baice komai ba, tace “billahi lazi tashi zakai kasan yanda zakai muci abinci dan yunwa nakeji kamar me.”

 Nimafa yunwa nakeji, ina nasan yanda zamuyi?

Sai ka dau kayanka kalai kasuwa ka samo mana kudi.

 Tab kayan dana ajiye bansan batasu shine zan siyar?

Tace “dole ka siyar kuwa.”

Mikewa yai ya shiga daki ya sauke labule.

******

Khalid shiru yai yana kallan yanda Zainab ke tafiyar da Presentation dinta, shi kuma yana danna mata slides din, gaba dayan mutanen gun sunyi shiru suna jin 

yanda ta ke watso musu ideas wanda duk wani wanda ke gun tabbas sai yayi sha’awar yi.

 Duk tambayoyin da suka jefo mata cikin dabara da jan ra’ayi take basu amsa wannan yasa Chairman din Company din amincewa a take a gun, nan Khalid ya 

mikamai takardar contract itama ya mika mata daya sukai signing sannan ya amsa yai switching suka sakeyin signing.

 Cikin jin dadi Chairman din yace “am looking forward to this project.”

Cikin confidence dinta tace “you will never regret your decision.”

Nan aka tafa sukai sallama suka fito.

 Tana shiga mota ta sha ruwan dake hannunta sannan tasa hannunta akan goshinta ta lumshe idanunta.

 Khalid ya shiga yaja, a hankali ta kalli agoggon jikin motar tace “lokacin tashina yayi, bari na ajiyeka na wuce gida.”

 “Bari na ajiyeki sai na wuce.”

 Bata musa ba ta dau waya ta turama Director Kabir text na hoton contract din da sukai, sannan tadaura da sauran maganar mayi gobe.


  Ganin contract din da zasu samu uban kudi yasa yace to Allah ya kaimu.

 A kofar gidanta yai parking, Bala ya bude ya shiga da ita.

 Kallansa tai tace “nagode.”

 Bakomai, ya bude motar ya fita.

 Yana fita daga gate suka gagaisa da Bala sannan ya wuce, yana tafe yana tunanin dole yana bukatar sake dagewa, dan yau ya fahimci bai maida hankali ba ko 

kadan, duk da ba abinda ya karanta ba kenan anma yasan in ya maida hankali sosai komai mai yiwuwane da izinin Allah.

Zainab har ya fita bata mike daga zaunen da take ba, haka kawai ta samu kanta da jin haushin yanda ya mata, tana ganin shi zai rakata ta dauka yanasan ya 

mata maganane amma sai ya nuna bashida ra’ayin hakan?

 Meye nawa a ciki? Kar ya tambaya din, kowa ya sha xamansa.

 Muryar Nabila taji daga gefen ta.

Murmushi tai sannan ta tuna hutunsu ya kusa karewa gashi bata nemi babbar mai aikin da Dady yace ba.

 Ahhh da alama tana da abubuwa dayawa a gaba.


*********

Goggo tadan leko, su Asabe ta gani ana tacin shinkafa da dage dage, tace “Asabe nikam kin san waya iya kitso a nan kusa?”

 Asabe ta kai loma tace “Karimatu ta iya anan makota take.”

 Goggo tace “Allah sarki, nagode.”

Kallan yaranta dake cin abinci tai tace “oh anatacin abinci ne?”

Asabe tace “eh, ya akai?”

Dariya Goggo tai tace “bakomai, nima inzo in daura dan ganin kunacin abinci ya sani jin yunwa.”

Asabe ta kalli yaranta biyu mata dake cin abinci tare, ga danta namiji a gefe wanda ya mike yace “ni nakoshi.”

 Asabe cikin gatse tace “ko zaki d’ana wannan kafin ki daura? Dan banda wani sai wannan da babangida ya rage.”

Ga mamakinta ganin Goggo tai zuruf ta mike tazo ta amsa tana cewa “bari na dan taba, haka kawai yunwa taxomin yanzu.”

Asabe ta tabe baki a ranta tace sanda kuke cin tsire a daki, ku soya dankalu ai ko kwaya baki taba ba ko ‘ya’yan mu ba.

Ita dai Goggo ta shige daki, tana shiga ta cinye, haushi ya kamata tace “ai da sai ka rage dayawa, na rasa meyasa yara ke da uban ci ina laifin suci kadan, 

wani sa’in sai ka rasa ina suke kaiwa.”

Adam ne ya fito yana neman fita yaganta tana sud’e hannu, da sauri yace “Goggo kinsamo mana abincin ne?”

 Kwanon ta turamai tace “eh gashinan ci.”

Yace “wannan ai bakomai, ina nawa?”

 Wani kallo tamai tace “kasan Allah? Idan baka fita ka saida kayanka ko dako kayi ba, ranka ne zaiyi matukar baci.”

Dako?

Yanda yai maganar a zabure yasa tace “to fadamin inba jikinka ba uban me kake dashi.”

Dariya yasa yace “nine zanyi dakon? Adam din? Mijin Zainab?”

 Mikewa yai yana cewa “zanje indawo ki samarmana abin ci.”

 Haushi ne ya kamata ko amsa ma bata bashi ba.

Yana fita majalisa suka tsareshi, ina hoton? Nasan ai yanzu ka dako.

 Kallansu yai ya zaro wayarsa.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button