A GIDANA 4
Haske Writers Association馃挕
Shafi na hudu
Adam cikin mamaki yace “Khalid!”
“Eh nine.” Adam ya zauna a bakin gado yace “ya gida khalid? Inatajin ba dadi dama ban amshi numberka ba.”
“Is okay, maganar aikin nan.”
Idanu Adam ya zaro kamar yai dan ihu amma sai yace “eh tana nan? Kana so ne?”
Khalid ya matse hannunsa saboda jin ba dadi da yakeyi, yace “eh, sai dai zan fara duba inda zan zauna da albashi da sanin yanayin lokacin aikin da sauransu.”
Adam da sauri yace “kar kaji komai, ai kawai in dai ka shirya kazo gobe saboda litinin tanada aiki, ba wani matsala.”
Cikin mamaki Khalid yace “ba matsala kamar ya?”
“Eh in kazo goben ma tattauna, amma ba wani abun ka kirani gobe in xaka taho zan turo ma da address, abinda kawai yace kenan ya kashe wayar da sauri.” Wata irin kara ya saki wanda su kansu dake falon sai da sukajishi.
Zainab ta miki da sauri ta nufi cikin dakin, yana ganinta ya maida fuskarsa, cikin mamaki ta kalleshi tace “Honey lafiya?”
Murmushi yai sannan yace “bakomai dama munyi waya da Kwaro ne shine yace zai fara aikin.”
“Kwaro?” Ta tambaya cikin mamaki.
Kin mantashi?
“Ohh friend dinka?”
Da sauri yace “eh.”
Kallan mamaki tamai ta matso kusa dashi tace “wai da gaske abokinka ne zai zama driver na?”
Hannu yasa ya jawota ta zauna kan cinyarsa yace “neman aiki yake sosai, da alama yana cikin wani hali, kinga ba dadi na cemai kar yai bayan ya kirani akan yana san aikin.”
Idanunsa ta kalla sannan tace “amma gani nake bai dace na kamar.”
Karki damu, a yanda kike din nan ma nasan ba dadewa zaiyi ba zaku rabu, dan banaji zaku jitu da halayensa.”
Wani irin murmushi tai sannan tace “kasan haka kace yazo?”
Karkace kai yai yace “I feel bad for him.”
Shiru tai kawai batace komai ba, ajiyar zuciya yai kamar wanda yake cikin wani halin wanda yasata kallanshi, yace “matsala daya, banaso ya dinga kalleminke, shiyasa nake neman manya magidanta.”
Harararsa tai cikin wasa tace ” banda wanda akemin a tv?”
Ahhhh, ya dafa kai sannan ya kwanta akan gado yace “shikenan ni an gama duk kallemin matata.”
Mikewa tai tace ” zolayar ta motsa kenan?”
Mikewa yai shima yana dariya yace “gobe zaizo, sai dai bansan ko yanada gun zama ba.”
Da sauri ta kalleshi tace “sai ya nema ai wannan ba damuwa ta bace.”
Dariya yai yace “bari dai yazo goben muji.”
******
A bangaren Khalid kuwa yana kashe waya yai shiru yana maimaita kalaman Adam, kafin ya mike ya nufi cikin gida dan sanar dasu Umma tafiyar fa gobe ce.
Umma na zaune akan tabarma kusa da Abba, suna hira.
Yana shigowa tsakar gidan Umma tace “Khalid dan halak, muna maganarka sai kaga.”
Murmushi yai sannan ya karaso yana cewa “Su Amir ba’a dawo ba?”
Tace “ba dadewa zaka jisu, dan lokacin tashin nasu yayi ai.
Zama yai daga gefe yace “Abba ya jikin?”
Abba cikin sakin fuska yace “kasani yau inajin wani karfi, duk da ba sana’ar da nake fatan kayi bane ka samu a kalla dai nasan zaka samu abinda zaka taimaka mana ka taimaki kanka har a hankali kazo kai aure, wannan tunanin yasa naji yau jikin nawa garau.”
Kallansa kawai yai sannan ya dan murmusa duk da abin bai kai kasan ransa ba, Umma ce tai saurin cefewa da cewa “Nikam kasan yar gidan kyauta?”
Ya fahimci me take nufi sarai amma sai cewa “Zahriyya datai aure?”
“A’a Habiba wacce ta gama makarantar secondary bana.”
Yace “ohh wannan yarinyar? Badai harta gama makaranta ba?”
Umma tace “ta gama wlh shiyasa dama nace…….”
Eheeem ya isa haka nan, abinda Abba yace kenan wanda ya sata yin shiru.
Abba ya kalli Khalid yace “ko zaka zauna a gidan kawunka Idris? In har gurin zama zai wahalar dakai a kanon?”
Kallan Abba yai sai dai shikam baisan zaman gidan nan sam, shiyasa lokacin da yake makarantar Buk duk abin duniya ya dameshi shi yasa ya koma cikin hostel yake dan zaman wani shagon ana biyansa ga kuma wanda Abban yake turamai ya samu yake biyan na hostel dan sam baya san gidan nan basu da tarbiyya ko kadan, sai dai a lokacin cema Abba yai kawai yafisan can saboda karatun dare.
Abba ya kalleshi yace “ya akai? Bakasan can din ne?”
Khalid yace “a’a bari goben in naje muka gama zan shiga can din.”
Umma tace “ah gobe ne? Da wuri haka?”
Yace “yanzu mukai waya dashi, sai dai ban sani ba ko in naje goben zan dawo ko kuma sai juma’a bandai sani ba sai naje can din.”
Abba yace “masha Allah ba laifi ai.”
Khalid yai shiru kafin yace “Abba!”
Abba ya kalleshi cikin kulawa, yace “na fadawa Salmanu zaizo da yamma ya dauki laptop dina, zai saida ita in yaso sai ya baku kudin a samu a rage wasu abubuwan kafin Allah ya kawo yanda za…….”
Katseshi Abba yaida cewa “a’a kul, na fada maka ba tun yau ba in har ba kudi ka samu zaka sai wata ba karna kuskura naga ka saidata, bayan duk abin karatunka a ciki kakeyi, sannan kace zaka sai data?”
Khalid ya kalli Umma wanda itama bata yadda da shawarar ba, zaiyi magana su Amir suka shigo da gudu.
“Kun daina gudun nan ko kuwa?”
Da sauri suka daina dan sun san halinshi.
Asiya na biye dasu, duk saida suka gaishesu da gida, Asiya tace “Yaya! Ya salmanu na sallama dakai.”
Khalid ya mike yai waje.
聽 A yanda yaga Salmanu ne yasa hankalinsa ya tashi, Salmanu na ganinsa ya matso kusa dashi, idanunsa sunyi jaa da alama ma har hawaye sun zubar, Khalid cikin mamaki dan bai taba ganinsa haka ba yace “Salmanu menene? Meya faru?”
Da alama baima san ta inda zai fara magana bane dan duk a rikice yake.
Khalid ne yasa hannu biyu ya riko kafadarsa ya girgizashi yace “Salmanu? Menene? Rasuwa akai?”
Salmanu ya zubamai ido kamar wanda baya hayyacinsa yace “Wai ansa auran Nazifa dazu.”
Gaba daya ya kasa fahimta yace “bangane ansa ranarta ba, ba dakai aka saba kenan ko me?”
Salmanu wasu zafaffan hawaye ne auka zubo mai yace “Khalid kwana biyu dama duk bansan meke damun Nazifa ba da mamanta, har yayenta ma, dan duk sanda naje zasucemin ko bata nan, ko tai bacci, ni duk ban kawo komai a raina ba saboda duk garin nan kowa shaida ne akan yanda muke san juna, yarinyar nan tun tana primary…..”
Khalid yace “na sani nasan wannan, ni bangane an sa rana ba.”
Salmanu ya goge kwallarsa yace “kanar yanda kaji din nan haka yanzu ina dawowa daga kano aka fadamin, ina zuwa gidansu yayanta yake fadamin, wai Alhaji Badamasi.”
Khalid ya fahimci kwanan zancen, wato sunga kudi, sai dai ba’ama Salmanu hallaci ba, kusan shekara kenan yana ta faman hada lefe dan so yake ya mata lefe na fitar kunya amma ynzu a mai haka,m? Bayan tun tana primary hartakai secondary komai shi yake mata, hatta provision in zata koma skul shi yake mata.
Ran Khalid yakai matuka gun baci wanda takaici ya kamashi yace “yanzu wani irin cin mutunci ne wannan?”
Salmanu ya kalleshi cikin karayar zuciya yace “taya zan iya rayuwa ba Nazifa?”
Haka ya juya dan yace yana san kadaicewa y tafi, Khalid yabi bayansa da kallo, shi yasa fa shi sam harkar soyayyarnan bata gabansa, karshe ma shi bai yarda da ita ba.
Haka ya shiga daki yana hada kaya cikin takaici.
***********
Wajen karfe 11:30
聽 “Wallahi bazanyi wanke wanke ba sai dai ke kiyi ni shara zanyi.”
“To ni bazanyi wanke wanken ba nima shara nakeso.”
Fadansu ne ya sa Zainab ta farka dan cikin bacci taji ana fada.
Mikewa tai ta kalli Adam wanda da alama baijisu ba,聽 fitowa tai suna tsaye a falo suna fada Goggo na zaune tana kallo ko kulasu batai ba, hankalin ta ma sam baya kansu.
Zainab na rufe kofa suka juyo sauri suka kalleta, kallansu tai tace “mekenan?”
Nusaiba tace “Aunty…….”
Ku wuce duk kuyi komai tare, wai sai yaushe zaku girma da fada ne?”
Nabila zatai magana, Zainab ta kalleta.
Da sauri sukai shiru, kitchen suka nufa kowa fuska a hade.
Zainab ta kalli Goggo tace “Goggo kina kallansu amma bazaki hanasu ba?”
Goggo ta kalleta tace “ni? Ina na isa? Ai ni ba a bakin komai nake ba a gidan nan, yara sunzo gidanki ai sun fini iko da gidan.”
Zainab kallanta kawai take sai dai kalaman sun bata bata rai sosai, tace “Goggo me yasa wani sa’in in kina magana sai ma dinga gani kamar magana kike fadamin?”
Goggo ta mike tace “magana? A ina? Bayani kawai na miki, sai dai in ke kika fassara, ni ina na isa na fada miki magana?”
Zainab zatai magana, kawai ta fasa dan ta kula ranta ne zai baci, in kuma ranta yabaci to lallai da matsala, juyawa tai kawai ta shiga ciki.
Goggo ta bita da kallo tace “wannan da badan mune a karkashinki ba wlh da kece a kasana dasai na koya miki yanda ake lallaba uwar miji.”
Tai tsaki sannan ta zauna ta cigaba da kallanta tana dariya.
Zainab kam daki ta wuce, wayarta ta dauka missed calls ta gani kala kala daga gun aikinta, da sauri ta kirasu, nan aka sanar da ita air advertising din da suka dade suna nema ne ya taso, sannan an kammala musu website din da suka sa a canza musu,tazo suyi meeting.
Da sauri ta shiga toilet tai wanka ta fito, ta hau shiryawa
********
Khalid kam karfe goma yai sallama da gida bayan ya samu a daren jiya ya saida wayarsa ya nemi karama mara internet, yaba su Umma kudin saboda lamari sannan ya bada dubu biyu a kara ba masu bashi, da wannan yai sallama dasu akan zaije ya dawo a yau in ya samu hali.
Har ya shiga mota yana tunanin abinda akawa Salmanu wanda ya bata mai rai matuka.
Address din da Adamu ya turomai jiya da yamma ya dinga dubawa聽 ganin ya kusa isa gidan yasa ya kirashi a waya.
*****
Adam na bacci yaji motsinta a toilet, ohh cikin layin bacci ya duba wayarsa, mikewa yai ganin yasha bacci, yana zama wayar Khalid na shigowa.
Da sauri ya dauka yace “kwaro!”
Khalid yace “Adam gani nan na kusa isowa, in nace gidan Journalist kawai shikenan?”
Adam yace “eh sai ka iso.”
Da sauri ya kashe ya mike daga kan gado, fitowatai daga toilet da sauri ta kalleshi a tsaye tace “ka tashi?”
Yace “eh, tace “taimaka plz ina shiryawa ka dan dubamin email din nan.”
Ta dau wayarta tana mikamai, amsa yai yace “gun aiki zaki?”
Tace “eh.”
Amsar wayar yai ana karanta mata, da sauri take sa kayan, tana gamawa ta gyara fuskarta, daidai nan ya gama ta amsa tace “thanks Honey.”
Kiss tamai sannan tace “i have to drive shiyasa nace ka karantamin tun anan, sai nai tunani a hanya.”
Yana kokarin sanar da ita Khalid din yanzu zaizo ta dau jaka ta fita da sauri, biyota yai yana cewa “Honey dama…….”
Kallansa tai tace “kar ka damu zan samu abinci naci acan, tnz.”
Da sauri ta wuce kitchen, ta kalli Nusaiba da Nabila tace “Allah yasa naji labarin kunyi fada.”
Baki suka rufe, tare da cewa “adawo lfy.”
Da sauri ta fito ta kalli Goggo tace “Goggo na tafi.”
Tace “yau fa lahadi.”
Tana tafe tana cewa “abu ne ya taso mu director’s ne kawai zamuyi meeting.”
“Darastas??? Me kenan?”
Adam ya girgiza kai yai waje.
Tana fitowa waje shi kuma yana turo kofar gate din.
Kallansa tai sannan shima ya kalleta.
Adam da ya fito ne ya kalleshi shima.
Fuska dauke da mamaki tace “Who?”
Khalid zaiyi magana Adam ya dawo gabanta yace “Khalid ne.” Khalid? Cikin mamaki ta kalli Adam, da sauri cikin magana mara sauti yace cinye duu… kwaro.”
Key din hannunta ta cilla mai ya cafe tace “drive.”
Khalid ya kalleta cikin rashin fahimta, wucewa tai cikin mota ta bude kawai ta shiga.