NOVELSUncategorized

A GIDANA 5

*Haske Writers Association*馃挕

*Shafi na biyar*
 Khalid ya kalli Adam wanda ya gunste dariyarsa,daga cikin mota tai knocking din glass din motar, tana rike da tablet dinta tana duduba abubuwan da sukai discussing waccen meeting din, Adam ya kalli Khalid yace “sai kun dawo ma tattauna.


 Ya shige ciki da sauri, Khalid ya nufi jikin motar sannan ya bude mazaunin gaba ya shiga tare da tada motar.

 Bai mata magana ba itama haka batabi ta kanshi ba, mai gadi ne ya bude gate suka fita, suna fita daga gidan yaja gefen titi yai parking.

 Sunyi minti biyar a haka saboda ita dube dubenta kawai takeyi, ganin shiru kamar ba’a tafiya yasa ta dago ta kalli waje, cikin mamaki ta kalleshi tace “ya naga ba’a tafiya?”

 Bai juyo ba yace “bansan ina zamu ba.”
“Ai sai ka tambaya, saboda sauri nakeyi.”
 Shiru yai baice komai ba wanda hakan yasata dan jin haushi tace ” muje Gamji Tv station.”

 “Bansan inda yake ba.”

 Da sauri ta kalli agoggo taga tana bukatar hanzari.
kallansa tai sannan ta bude motar da sauri ta dawo inda yake a zaune.

 Kallanta yai itama ta kalleshi tace “am sorry but sauri nake kwatance bazai yiwu ba, can you please go that side?” Ta fada tana nuna mai dayan gun.

 Fitowa yai ya zagaya sannan ta zauna a gun, da gudu taja motar, tana kallan agoggo.

 Juyawa yai ya maida kanshi waje yana kallan hanya, sai dai kasan ransa gaba daya tunani yakeyi, wani irin aiki ne wannan? Ba’ai bayani? Salman ne ya fado masa, dan tsaki yai wanda shikanshi baisan yayi ba.

 Karaf a kunnenta, kallansa tai cikin mamaki gani tai hankalinsa ma bai kanta, tsakin na menene? Ta fada a cikin ranta, wanda abin ya dan mata zafi, dan bata fahimci me tai ba balle a mata tsaki haka.

Gaban Gamji tv tai parking, fitowa tai kawai ta bude baya ta dauko kayanta dake baya, kallansa tai tace ” bansan ko zan dade ba, in nai 1hr ban fito ba ka koma gida in na gama zan kora Adam sai yama magana.”

 Ta juya kawai ta shige cikin building, mamaki ne ya kamashi ya kwantar da kansa akan kujera, idsnunsa ya rufe a hankali.

 Wayarsa yaji tana kara ya zarota a cikin aljihunsa, ganin Abba ne yasa ya daga da sauri.

 Bayan sun sake gaisawa Abba yace “munji baka kira ba ko baka isa bane?”

 Yace “na isa dazu.”
“Kaje gidan?”  
Eh kawai yace tare da saurin cewa “ya jikin?” 
Abba ya fahimci baisan maganar da alama ko ba shi kadai bane hakan yasa yace “da sauki, anjima mayi waya.” Ya kashe wayar, Khalid yai shiru yana kallan wayar dan to baisan me zai cema Abba ba in ya tambayeshi ko ya ake ciki? Bayan shi kansa baisan ya ake cikin ba.

  Yana nan a zaune yana yan tunaninsa jefi jefi yana kallan agoggon wayarsa.

*******

 Zainab tana shiga ta wuce office din meeting dinsu, suna zaune suna tattaunawa ta shiga.

 Tana shiga ta samu guri ta zauna, dan daga director din sai ita a matsayi, tana zama ta amshi takardun proposal din da akai accepting tana dudubawa, nan ta shiga bayani tare da kawo yanda za’a cin ma manufar, gaba daya kowa yayi shiru yana sauraran jawabinta, har ta kammala sannan tace “ya suke gani?”

 Nan kowa yai naam da abinda ta kawo dan dama indai agun harkar aikinta ne ko director din da ita ya dogara saboda tsabar sanin aikinta datai da kuma darajashi datai, nan suka gama taron akan abinda tace shi za’ai, ta mike zata fita ne director din ya mata magana.

 Dawowa tai ta zauna tare da kallansa.
“Zainab naji Ramla tayi laifi ayi hakuri a sassauta mata.”

 Kallansa tai idanunta tsam tace “ni director kai ka kawota ne?”

 Da sauri yace “ni kuma? Interview taci aka bata aiki.”

 Murmushi tai kafin tace “banajin ranar danai interview naganta a ciki, kafi kowa sanin inada rike mutum duk yanda naima interview zan ganeka balle wanda yaci.”

 Director yai dariya cikin zolaya yace ” yo inbanda abinki dani fa akai interview din nan akai audition duk nasan wadanda sukaci sai dai kin manta ta ne.”

 Murmushi ta sakeyi dan ta fahimci neman karewa yake da alama shi ya kawo ta ko daga sama dashi ne.
Tace “Ah Alhamdulilah tunda dai ba yarinyar ka bace.”

 Ransa ya sosu da maganar me take nufi da yarinya? Sai dai ba yanda ya iya da Zainab saboda itace ta kawo cigaban da suke dashi yanzu, itace ta jajirce ta maida gidan tv dinsu ya zama abinda ya zama, inba ita yasan komai ya wargaje, amma da badan haka ba da…….
 Kallansa tai tace “maganar Ramla ka cireta daga mai dauko rahoto dan inba haka ba zan koreta da kaina, ka maida ita wani bangaren.”
Bata jira amsarsa ba tace “zan wuce inba wani abin.”

 “To shikenan zan duba inda ta dace.” Abinda ya iya fada kenan, ta mike ta fito daga office din, tana rufe kofa tai dan ajiyar zuciya na takaici, haka kawai ga mutanen da sukaci ta bada list dinsu a kan su sukaci amma tazo ta tadda a cikin mutum goma da kana dauka mutum hudu ne kadai aka ba aikin ragowar shidan ba ci sukai ba aka basu, gwada su biyar din ma sunyi interviewe faduwa sukai amma ita wannan Ramlan ba wanda ta ganta sai ranar first day din sabon ma’aikatan.”


 Agoggon hannunta ta kalla, hawanta kusan biyu kenan ta san ya tafi, hakan yasa ta shiga office dinta tare da kiran number Adam.

 Shikam Adam tana fita ya shiga yai wanka ya tafi majalisa, suna zaune suna hira wayarta ta shigo.

 Mikewa yai ya matsa gefe, yana ji suna tsokanansa yaran Hajiya zata bada aike ne?

 “Honey kin taho ne?”

 Tace “a’a kayima Abokinka magana ya dawo ya daukeni.”

 Cikin rashin fahimta yace “ya dawo ne?”

 “Kana ina?” Tambayar data jefeshi da ita kenan, sam batasan majalisa dan tasan gulma kawai akeyi, cewa yai “naje siyoma Goggo maganin zafi ne.”

 Ayya, to bari na kira Nabila.

 Kashe wayar tai ta kira Nabila, mamaki ne ya kamata da Nabila tace mata ba’a bataji alamar shigowar mota ba, harta kara dubawa tace ba motarta a gidan.
 Wayarta ta daga ta kara kiran Adam tace “baya gida fa.”

 Adam yace “inata kiran wayarsa kuma a kashe.”

 Fitowa harabar gun tai inda suke ajiye motoci amma bata ganshi ba, cikin bacin rai tacema Adam badai ya gudu da motar ba?

 Shiru Adam yai yana nazari, bafa haka khalid yake ba ya tabbatar sai dai san rai irin na dan Adam sai cewa yai “ah haba?”

 Zainab cikin dan zafin rai tace “badai bakasan halinshi ba?”

 Shiru Adam yai duk da yasan ba halinshi bane amma sai cewa yai “na sani amma kinsan mutanen yanzu in aka rabu sai su can……..”

 Kashe wayarta tai saboda yanda taji ranta ya baci matuka, sam batasan in ranta ya baci ta cigaba da magana dan zata iya fadan abinda bai dace ba wanda daga baya zai iya sata dana sani.

 Rai a bace ta fito wajen station din, ranta yakai matuka gun baci, tabbas sai tasa an nemo mutumin nan duk inda ya shiga kuwa.

聽 Tana fita taga motarta a gefen station din, tsaya tai cikin mamaki sannan ta karasa gun tana kallan motar.

 Yana zaune a mazaunin driver yana dadana wayarsa.

 Kai ta juya gefe tare da jin ba dadi na zargin datai ba tare da ta bincika ba.

 Juyawa tai ta zagaya inda take zama sannan tai knocking din glass din, madannin bude motar ya danna ta bude ta shiga, baice komai ba tana zama ya tada mota suka hau kan hanya.

 Shiru tai batace komai ba sai dadana tab dinta takeyi, shikam ko juyowa baiyi ba tukinsa kawai yakeyi.


 **********

Adam kam tana kashe waya yai shiru cikin mamaki yace meke faruwa? Ba yanda za’ai khalid ya gudu, to ina ya shiga?

 Da sauri ya musu sallama sannan ya ja motarsa ya nufi station dinsu.

 Yana isa ya shiga ciki, yana shiga ya hadu da wani wanda yana ganinshi ya ganeshi matsowa yai ya gaisheshi, Adam yace “Zainab fa?”

 “Ta tafi dazu.”

 Kai ya jinjina sannan ya juya tare da kiranta a waya.

 Tana zaune cikin mota ya kirata.

 “Honey Kina ina? Nazo bakyanan.”

 A hankali tace “ina hanya, kaje ina?”

Yace “nazo daukanki mana.”

 Da sauri tace ” na sameshi a waje ai mun taho.”

 Sai data fada ta kalleshi kadan, karya gane zargin da sukamai.

 Shikam baimasan metake yi ba, jitai yace “left or right?”

 Kallan hanya tai sannan tace left, tace “Honey sry ka taho gida.”

 Kashe wayar yai yana cewa “nimadai kwai soko ko me nake anan?”

聽 Yana shiga mota ya tuna karyar dayai da sauri ya kira Goggo, itakam tana zaune tana kallo batamasan yana kira ba.

 Haushi ya kamashi ya cilla wayar kujerar dake gefensa matsalar Goggo kenan, tana can tana tainannan kallanta batamasan yana kira ba.

******

 Khalid left or right? Abinda kawai yake ce mata kenan in yaga ya kasa gane inda suka biyo dazu, suna shiga cikin harabar gidan ta fito tana kokarin shiga ciki.

 Mamaki ya kamashi yace “Excuse me.”

 Tsayawa tai tare da juyowa sannan ta nuna kanta alamar ni?

 Yeah.

 Haka yace mata wanda yasa ta kara kallansa batace komai ba.

 Kallanta yai yace “lokaci na wucewa inada abubuwan da zanyi sorting a yau din nan, and it seems like bakida niyyar yimin bayanin yanda aiki na yake da abubuwan da ya kamata nayi da sauransu.


聽 “Am sorry amma you have to told me saboda insan abinda ya kamata nai kafin dare yai, ba’a gari nake ba, inasan komawa.”

 Gaba daya jitai ma ta rasa bakin magana, yau take ganin ikon Allah, yana mata magana kamar itace take aiki a karkashinsa?

 Sannan Excuse me?

 Meya dauketa? 
Ko dan tana matar abokinsa yana tunanin wulakantata?
Harda tana tausayinsa tana ganin Adam yaci zarafinsa ashe shima dan rainin wayau ne?


 “Excuse me, naji kinyi shiru.”

 Excuse me? Again?????


聽 Ranta ya baci, kallansa tai cikin bacin rai sai dai yanda yake kallanta da jiran tamai magana yasata juya kanta abokin Adam ne, cool down…..

 Bude kofar da akai ne yasa ta kalli kofar, Nusaiba ce ta fito da gudu ta rungumeta, kallan Khalid wanda ke tsaye ta tsaya tana yi, Zainab ta zare ta sannan ta kalleshi tace ” bari Adam ya karaso sai kuyi magana.”

 Haka kawai tace ta shige ciki.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button