A GIDANA 42
{42}
Kamalu ya kalla da sauri bayan ya matso kusa dashi, yace “me ya faru zai ban wannan uban kudin sannan yai hira dani?”
Kamalu yace “Da alama tambayarka yake sanyi akan matarka.”
Da sauri ya kalleshi yace “akanta?”
Goggo ta fito da sauri tace “akan Zainab zaiyi hira dashi? Meyake san ji?”
Kamalu da sauri yace “bansani ba nima.”
Ganin yanda Goggo ke kallansa yasa yai saurin yin waje.
Kallan su Asabe ta da suka leko, ta kalli Adam tace “wuce ciki.”
Shiga yai ya zauna yace “Goggo me kike tunani suke san ji?”
Kallansa tai tace “meke faruwa wai?”
Shiru yai cikin rashin sanin abinda ke faruwa shi kansa yace “bansani ba wlh nima Goggo amma dubu talatin haka kawai?”
Shiru tai tana nazari, kafin ta kwace complementary card din dake hannunsa tasa a lalitarta, da sauri yace “Goggo.”
Tace “ka bari inyi nazari.”
Dan baki ya tabe sannan ya jawo abincinsa ya cigaba daci, shiru Goggo tai tana tunani.
*******
Kashe wayarta Afreey tai sannan ta dawo cikin office ta xauna, producer ne ya shigo ya nemeta data zo ta shiga cikin shirin da za’ai a wannan lokacin.
Kallanta sukai dukansu dan tunda aka daukesu har yau ba wanda ya fara gabatar da wani shiri.
Zainab ce ta mike bayan ta gama nazarinta, office din Director Kabir ta nufa wanda tun shigowarta ya aiko yana kiranta.
Shiga tai bayan an bata izinin shiga sannan taja kujera ta zauna.
Kallanta yai itama ta kalleshi, dauke kai yai yace “kinyi sorting matsalarki?”
Tace “banida wata matsala da zanyi sorting.”
Kallanta yai fuskarsa ta bayyana bacin rai yace “Me kikeso mutane su daukemu? Kinsan kananan maganganun da ake akan ki?”
Kallansa tai ba tare da tace komai ba, ya cigaba “ance kunyi fada hartakai ga saki, sai dai dayake kece kike rike da auran korarsa kikai ya bar miki
gidan, a cewar wasu ma kece kika gaji da auran kika sakeshi.” Cikin d’an daga sauti yace “me kike so mutane su daukemu a matsayinki na idan gidan tv din
nan?”
Itama yanzu fuskarta dauke take karara da bacin rai tace “dan ina aiki anan sai akace ban isa na samu matsala a rayuwarta ba? Meye hadin harkar aiki da
rabuwar aure na? Mun rabu ya tafi inda zai zauna sai hakan ya jawo matsala?”
Ransa a bace yace “kinsan ba haka nake nufi ba kema ai.”
Tace “am sorry amma ban fahimci menene hadin aikina da rayuwata ba.”
Takardun hannunta ta turamai gabansa tace “ga wad’an nan ka duba kasa hannu, zanzo na amsa gobe.”
Tana kaiwa nan ta mike ta fita, cikin kuluwa yabi bayanta da ido, ai yanzu tunda dai ta bashi ideas kala kala na yadda zasu cimma manufarsu na kusan shekara
hudu zuwa biyar tabbas wannan karan ko da bala’i sai ya koreta, sam ya gaji da yanda kowa yake mai kallan a karkashinta yake kowa kallan wanda baisan komai
ba yake, ko meeting suka shiga kowa abinda Zainab tace kawai yake bi ba wanda ya damu da nashi ra’ayin.
Zainab na shiga office dinta ta runtse idanunta tare da kwantar da kanta akan desk dinta, wayarta ta dauka tama Khalid text.
“Ka samu inda yake?”
Ganin ba reply yasa ta maida idanunta ta rufe ranta na kara baci, jin alamar shigowar sako wayarta ne yasa ta bude ido da sauri ta dauka Khalid ne ya mata
reply.
“_Ha Ha Ha! Ya kike ji? Gashi kema rayuwa tana neman yin juyi dake?_”
Kallan number tai batama santa ba sai dai murmushi ne ya bayyana a fuskarta tace “it seems I have alot of enemies” Maida idanunta tai ta rufe cikin kunar
zuci.
Khalid kam yana can suna ta aikin editing sam bai kula da wayarsa ba sai wajen lunch da suka gama ne ya fito, yana daukan wayarsa yaga sakonta, har zai
mata reply kawai sai ya danna call tare da d’an fitowa daga dan corridor.
Jin bata d’auka bane yasa ya kashe sannan ya koma ciki.
Afreey dake tsaye ne ta bishi da kallo har ya koma, haka kawai jikinta ya bata Zainab yake kira.
Ranta a matukar bace ta fito daga Station din ta shiga motarta.
Waya ta d’auka ta kira Giss, yana d’auka tace “ya kiraka?”
Yace “tun dazu nake jiran kiranshi harynzu bai kira ba.”
“turon Address dinsa.” Haka kawai tace ta kashe wayarta.
A kofar gidansu Adam ta tsaya, kallan unguwar ta shiga yi tare da tabe baki, cikin sa’a sai ga Adam ya fito yana sosa cikin sumarsa, kallo daya tamai ta
gane dan ta kara ganinshi sanda yaje gun Zainab.
Horn din motar ta danna sannan ta sauke glass din inda take zaune.
Kallan motar yai cikin santi yake kara kallan motar,yarinyar dake zaune a ciki ya kalla, tasha ado sosai kamar yanda ta saba, sam bai ganeta ba harya
karaso, ya cire hannunsa daga kansa tare da dan dafa motar yana kallanta yace “wa kike nema?”
Murmushi ta sakar masa sannan tace “wali walawa baka ganeni bane?”
Kallanta yai cikin mamaki kafin yace “Afreey?”
Murmushi ta sakeyi yanzu kam har hakoranta ne suka bayyana tace “shigo.”
Cikin jin dadi ya bude motar ya shiga ya zauna sannan ya kalleta yace “ikon Allah, Afreey dana ki……..”
Jan motar datai ne yasa ya kalleta yace “ina zamu?”
Batace komai ba har sai data bar lungun ta hau kan titi sannan ta ganganra gefen titi tai parking.
Kallansa tai tana murmushi tace “me kake a wannan unguwar?”
Dariya yai yace “me nake kuwa inba zama ba?”
Baki ta tabe tace “Shekaru dayawa.”
Juyowa yai ya kalleta gaba daya yce “Afreey yaushe rabo? Ban taba tunanin zan kara ganinki ba.”
Bai jira tace komai ba yace “Khalid fa? Kin sake ganinshi.”
Kallansa tai tace “me kake tunani?”
Dariya ya saka sosai yace “ai yasin kin ganshi, wai haryanzu dai? Na d’auka ai an wuce gun.”
Murmushi tai tace “wuce gun? Tadan sauke ajiyar zuciya tace “Ahhhh bansan ya zanyi na wuce gun nan ba.”
Dariya ya sakeyi yace “ya akai kika san inda naka?”
Juyowa tai ta zubamai ido, da sauri yace “yahkuri bansan wannan kallan kinsani.”
Murmushi ta sake sannan tace “ina matarka?”
Matata? Kinsan Zainab ne?
Kai ta daga mai alamar eh sannan tace “kun rabu ne gaba daya?”
Shiru yai yana kallanta, tace “taimakonka zanyi”
Taimako?taya?
Tace “ Taimakonka zan ta dawo gareka.”
Zabura yai da sauri yace “taya?”
Kun rabu gaba daya? Uku kai?
Da sauri yace “a’a”
Tace “then?”
Shiru yai yana tuna uku yai, amma ya zaiyi? Shidai wlh auransa yake so.”
Kallanta yai yace “biyu ne, amma taya zaki taimaken.”
Shiru tai tana kallansa tace “Zainab tasan Khalid ne?”
Dariya yasa nan ya sanar mata ai shi yai recommending dinsa ta daukeshi driver, yana dariya yace “na dade rabona da Khalid ko sanda naje gidansu gun
Zainab ban sameshi ba.”
Idanunta zaro tace “bangane ba? Gidansu?”
Dariya yai yace “to uwar kishi taimakonta yai a ranar, Zainab na sona haryanzu ni nasani, bazasu taba jituea da Khalid ba kinsan halayensa ita kuma bazata
dauka ba.”
A ranta tace love bai maida ta ba dai.
A fili tace “ meya rabaku?”
Kallanta yai sannan yace “bazan iya fad’a ba.”
Tace “bai damen ba koma menene, sai dai in har kana san ka dawo da ita sai dai ka d’aura mata laifi ka samu abu kace ita tai maka wannan ne zaisa a fara
tausayinka ita kuma mutane zasu fara zagin halayenta, balle dama can mutane dayawa basan halayenta suke ba, kaga hakan zaisa tai tunanin koma maka, dan ta
kare aikinta.”
Shiru yai yana nazari kafin yace “ni ba abinda tamin, me zai sa ince tamin?”
“Bakasan ta dawo ma kenan?”
Da sauri yace “ina so mana, sai dai Zainab ina ganin ko za’a kasheta bazata……” shiru yai bai karasa ba.
Kallansa tai tace “To mai zai hana ka fito cikin hira ka zubar da hawaye kana neman ta yafema ku maida auranku? Wannan zaisa mutane tausaya ma kaga za’a
fara zaginta in akaga taki maida auranta, wasu zasu fara aibata zaman da take ita kadai wannan zai sa ta dawo ma, na tabbatar yanda takesan aikinta bazataso
wani abu yasa ta rasa komai ba.”
Shiru yai yana kallanta yace “Taya zan so a zagi Zainab?”
Fuska ta hade tace “tunda bakasan a zageka sai ka hakura da ita.”
Da sauri yace “wannan ne bazan iya ba”
Enveloped ta mikamai ya amsa tare da budewa, check ne na dubu d’ari, idanu ya zaro cikin tsananin mamaki ya kalleta yace “na meye?”
Tace “Taimakon ka nai sai kaima kai kokarin taimakon kanka, nima duk sanda na nemi taimakonka akan Khalid you have to help me.”
Shiru yai kafin yace “shikenan an gama, nagode sosai Afreey nagode nagode.
Yanda yake mata godiya ne yasa tai shiru tana kalansa, dubu daya ta mika mai tace “ka hau mota.”
Amsa yai ya fito taja motarta ta tafi, baki ya sake yana kallan motar har ta kule.
Wani alheri ne yake faruwa dashi haka? Da alama Allah ne ya dubesu.
Wani irin tsallen dadi yai, ai da kafa ya taka a hanya ya tsaya gun mai balango ya siyo na d’ari biyar ya siyo lemo ya taho gida cikin nishad’in da kai
kace talauci aka yanke mai.
Goggo kam mamaki ne ya hanata ma cin balangon sosai, sai kara kallan check din take zuciyarta na kara sanyi, kallan Adam tai tace “shawara ta biyun tafi
kaga ai ba mutuncinta kaci bako?”
Da sauri yace “haka na gani, ai gaba daya na rasa farin cikin da nake ciki.”
Dariya suka sa cikin jin dadi, Goggo kam wani irin nishadi takeji, kallansa tai da sauri tare da tsuke fuska tace “ba uku kacemin kayi ba?”
Yace “haka na dauka amma yanzu dana nutsu na tuna biyu nai ranar ma dan bana hayyacina ne.”
Cikin jin dadi tace “haba? Shine baka fad’a min ba? Bari nai maza na fara had’a kayanmu yanda daga an kammala komai mu koma, yan bakin ciki naga yanda
zasuyi.”
A tare suka sa dariya, Adam a ransa yace “in na dage biyu nai ai dole ta koma tunda ba aurene da ita na, ko takardar ta dauka sai nace ba ni na rubuta ba.”
Kallan Goggo yai shima yasa dariya cikin jin dadin abinda ya samesu.
Tana kwance akan doguwar kujera har lokacin tashinta yai batama sani ba dan baccin dabatai ba daren jiya shi ne ya dauketa, da yake yau batada amfani ba
wanda ya bi ta kanta sai gulmarta kawai da ake.
Khalid kam ganin ya kira sau uku bata dauka ba kawai ya share, lokacin tashinsa nayi ya duba yaga duk yan aikin rana ma sun tafi, mikewa yai ya dau jakarsa
yana kokarin fitowa.
Juyawa yao ya kalli office dinta, ganin wutar ta a kunne ne yasa ya nufi office din.
Knocking yai, kamar a mafarki taji knocking, a hankali ta bude idanunta, cikin hanzari ta mike hankali a tashe.
Kallan agoggo tai sannan ta bada izini.
Khalid ne ya bude kofar ya shiga, kallansa tai da sauri ta kauda kanta gefe tana tunanin da alama fuskarta duk tayi abin bacci.
Khalid ne ya kalleta yace “bakyajin dadi ne?”
Bata kalleshi ba tace “I don’t know what’s wrong with me.”
Yana tsaye a gun yace “maganar gidan, nama wanda yai posting din a instagram ya turomin address din.”
Juyowa tai da sauri tace “can you send it to me?”
Wayarsa ya dauko ya tura mata sannan yace “zan wuce.”
Harya juya tace “Ammmm….”
Tsayawa yai sannan a hankali ya juyo ya kalleta, kallansa tai itama sannan tace “Can you help me?”
Yanayin yanda ya canza kallan da yake mata ne yasa ta juya kai, tace “i just feel like Director Kabir akwai abinda zai shirya akai na, i made a mistake
dana bashi duka plans din danai, wannan karan they will try to use this against me.”
“But how can they do that? Bayan ba laifinki bane?”
Mikewa tai tare da d’aukan jakarta kusa dashi ta nufo, tace “Dole na nemo abinda zan kwaci kaina dashi, dukansu na saman nan basona suke ba.”
Kallanta yai yace “Do you have to do that?”
Tace “ko na rufe bakin Adam tunda suka san maganar sai sun dinga tuno abubuwa, i know they don’t like me amma banyi zatan wannan abin zai sa suyi tunanin
janshi haka ba.”
Kallanta kawai yake baice komai ba, kallansa tai tace “wannan kallan fa? Yanzun ma cewa zakai lefinane?”
“Maybe.”
Takaici ne ya kamata ta bude kofar ta fita, ga mamakinta ganintai ya fito shima kafin ta rufe office din taga yana neman tafiya.
Rufe Office din tai sannan ta taho, yana sauka daga kan steps din dazai sada ka da kasa, jitai yace “Do you ever think about that?”
Itama bata kalleshi ba tace “what?”
Yace “dalilin dayasa dul wanda ke tare dake bai xaune dake zuciya d’aya.”
Kasa daga kafarta tai balle ta sauka, shiru tai batace komai ba wanda hakan ya sashi ya juya ya kalleta.
Ganin yanayinta ne yasa yace “Don’t mind me.” A ransa yace Khalid meke damunka dasan fadan abinda bai dameka ba?
Daurewa tai ta kalleshi tace “can you drop me?”
Baisan sanda yadan murmusa ba yace “a matsayin wa?”
Tace “d’an Umma.”
Murmushi yai yace “then you have to change your tune, in za’a miki abu you have you have to differentiate between favour and order.”
Ita kanta samun kanta tai da murmushi tace “meyasa kake san kamin gyara akan duk abinda nai.”
Kallanta yai a tare sukace “I don’t know.”
Murmushi ya sake ya kalleta tace “i know haka zaka ce.”
Bai ce komai ba ya karasa sauka, itama sauka tai.
Afreey dake zaune cikin mota ta dunkule hannunta tana wani irin hucci na tsananin kishi.
Shiga tai ta zauna a gaba kanta dan kanta ciwo yake da alama baccin datai mai nauyi ne yasata, Khalid yazo shiga yaga Afreey a motarta tana hucci, ido ya
zuba mata yana kokarin yin nazari akan ta, Zainab jin shiru yasa ta bude idanunta, ganinsa tai ya zuba ido yana kallan abu, juyawa tai ta kalli inda yake
kallo.
Afreey ta hango, kallansa tai sannan ta kalleta.
Fitowa tai daga inda take ta nufi inda yake, bani key din.
Kallanta yai, gani tai ya mika mata ba musu, wani takaici ne ya kamata kawai ta shiga motarta rai a bace taja.
Khalid ne ya nufi inda Afreey take ya bude inda take zaune yace “Safiyya!”
Kallansa tai bakimta na rawa saboda tsananin kishi.
Yace “will you stop that?”
Me?