NOVELSUncategorized

A GIDANA 41

{41}


  Nuna mana, kallansu yai yace “nawa kuka sa.”

 Dariya sukai nan kowa yasa aljihu, yana nuna mai kudin dake aljihunsa, ido suka zubamai suna san ganin hoton.



 Bude musu hotonsa wanda sukai shida Zainab bayan auransu kadan, baki suka sake suna kallo, cikin hadara yace “yanzu kun yadda?”

“In kuma a hanya ka ganta kuka d’au hoton fa?”

Cikin bacin rai yce “ to wannan fa?” Nuna musu wanda sukai ya rike kafadarta yai.

 Idanuwa suka firfito dashi, cikin mamaki yace “ku bani kudin”

Ba musu haka kowa ya mikamai abinda ke aljihunsa, baki ya washe cikin jin dadin ganin ya hada dubu uku da dari biyar daga nuna hoto.

Kamalu yace “bani wayar na kara gani.”

Mikamai Adam yai tare da hard’e hannu ya zauna yana girgiza kafa irin sarkin nan.

 Kamalu ya faki idanunsu ya tura ta whatsapp dinsa, sannan ya mika mai wayar.

Suna rabuwa ya daura hoton a instagram tare da cewa ko kunsan wanene mijin Zainab Aliyu Tahir? Sannan ya daura wani wanda sukai shida Adam.

 Ya dan rufe fuskar Adam da hrt emoji kan kace me hoto ya fara yad’uwa a instagrams, whatsapp da kuma facebook, kowa yana san ganin mijin.

 Dariya yasa ganin yanda yake ta kara samu followers gashi anata tambayashi ya nunashi.

 Kamalu cikin jin dadi ya kara rubuta, ko kun san Zainab da Mijinta basa  zaune a gida d’aya?
Ai kan kace me ta ko ina gulmar abin ake, ko ina ka leka maganar kenan.

 Zainab kam batasan me ake ba dan bata whatsapp bare instagrams gwara facebook tana shiga taga labarai, bare su Nabila wanda ta hanasu da kanta acewarta su 

bari sai sun gama skul.

Da safe ta shirya ta nufi office, sai dai tana shiga taji ana gulmarta, bata wani bi ta kansu ba dan tasan maganar jiya ce suke kara riritata.

 Khalid wanda ke rike da wayar Afreey yana kallan hoton data zo nuna mai ya kurawa hoton ido dagowa yai  ya kalleta yace “inada magana dake.”

 Kallansa tai sannan ta bi bayansa ba tare da tace komai ba.

D’an dakin da suke cin abinci ya shiga, kallanta yai yace “menene hakan?”

 Tace “ina na sani nima, ganinshi nai tun jiya yana yawo shiyasa na nuna ma.”

 Idanunta ya kalla sannan ya kauda idansa, dan matsowa tai tace “Khalid tun jiya dana ganshi nake tunanin nasanshi, sai dai na kasa gasgatawa, Ba Adam awala 

bane?jiya dayazo na ga fuskarsa.”


 Kallanta yai, baice komai ba, dariya tai tace “Dagaske Adam ta aura kenan?”

 Fuska ya hade yace “Dariyar me take nufi?”

 Guntse dariyarta tai tace “ina mamaki ne dan ban taba kawowa Adam bane, yanzun ma na tambaya ne……..”

 Kallanta yai yace “koma menene aranki karki kuskura ki soma, nasanki sarai nasan akan wani ra’ayi nake ba abinda bazaki iya yi ba.”

 Kallansa tai tare da hade fuska tace “shaidar da zakamin kenan?”

Ba haka kike ba?

 Kallansa tai tace “kasan shekara nawa nai ina nemanka?”

 Wani kallo ya mata tace “Khalid plz ka bani dama na  gyara barnar danai a baya, bansan meye tsakaninku da ita ba amma kai kasan bazan taba hakura da abinda 

nake so ba, dan haka in har ba abinda nake zargi bane tsakaninku ka bani dama.”

 Kallanta yai kawai baisan sanda yasa dariya ba, ya shafi kansa sannan ya kalleta.
Zainab wacce tazo daukan cup ne ta kallesu tacikin glass din kofar, dariyar dataga Khalid  nayi ne yasa ta tsaya tana kallansa, shiru tai kafin ta juya 

tabar gun.

 Khalid ne ya kalli Afreey kamar zaiyi magana kawai ya wuce.

 Zainab taje shiga office dinta taji muryar Director Kabir taji yace “Zainab!”

Juyowa tai ta kalleshi, yace “inada magana dake.”

 Kallansa tai sannan ta nufo office dinsa, tana shiga ta zauna, kallanta yai sannan ya juya mata da laptop dinta saitinta, kallan hotonta dana Adam tai, 

sannan ta kalli rubutun kasa, da sauri ta dago ta kalleshi, fuskarsa a hade take, wanda bata taba gani ya hade mata rai ba yace “meya rabaku dashi?”

 Kallansa tai tace “kome ya rabani dashi wannan personal matter dina ne.”

 Personal? Wannan shine personal? Yai maganar cikin fada.

 Kallansa tai tace “me kake nufi? Nina sashi yai kenan ko me?”

 Ko ke kika sa shi ko ba ke bace alama ce ta kin kasa controlling dinsa, kinsan daga daren jiya zuwa yanzu mutane nawa ne suka kirani suna tambayata abinda 

ke faruwa? Akarshe sai wayata na kashe?”

 Kallansa tai abin takaici tana kokarin magana taga an kara posting din wajen gidan dasu Adam ke ciki a kasa ansa “ko kunsan nan ne gidan da Zainab ta kori 

mijinta yake zaune shida mahaifiyarsa? Me kuke tunanin ya mata?”

 Comment ne suka fara bayyana ta ko ina, Director Kabir ransa a matukar bace ya rufe laptop din da d’an karfi yace “bazan yadda da abinda zai kawo 

dakushewar gidan tv din nan ba, dan haka ki gaggauta gyara komai, in ba dan ke nace bama da korar wanda yai zanyi.”

 Kallansa tai idanunta suka fara yin jaaa, mikewa tai ta fito ta nufi office dinta ranta a matukar bace, farcenta ta shiga karza dayan farcenta dashi tana 

tunanin abinyi.


Can yamma bayan la’asar ganin gaba daya yau ta kasa yin komai dan dama haryanzu bata amshi shirinta ba tunda ta dawo, tana so ta gama gyagyara matsalolin su 

kafin nan.

 Wayarta ta dauka ta kalli number Adam, ranta na kara mugun baci, waya ta dauka ta kira staffs room, ana dagawa tace “akira mata Khalid.” Tana kainan ta 

kashe.

 Khalid wanda ya zauna yana harhade takardun da za’ai shiri dasu gobe ne ya kalli Ramatu datace ana kiranshi.

 Mikewa yai yazo fita, Afreey ce ta kalleshi fuskarta cike da kishi da takaici, baibi takanta ba ya wuce.

 Zainab na zaune akan kujerarta tana kara kallan abinda ke faruwa ta facebook, tare da kokarin bude account na instagram dan ganin abinda ke faruwa sosai.

 Knocking Khalid yai sannan ta bashi izini ya shiga.

 Kallansa tai bayan ya karaso ciki tace “kana instagram?”

 Kallanta yai dan ya fahimci ta gani kenan, shiru yai yana kallanta, sannan ya girgiza kai alamar a’a.

idanunsa ta kalla bayan ta kauda nata idan ne tace “it seems like kaima kaga abinda ke faruwa.”

Uhmm ya fada tare da d’an daga kai

 Shiru tai kafin tace “before reporter’s su tare Adam suyi hira dashi i have to do something.”

 Kallanta yai yanzu kam baice komai ba, dagowa tai cikin dauriya tace “Bantaba tunanin Adam zaimin haka ba, duk da ynda muka rabu amma atleast na dauka zamu 

rikema juna sirri.”

 Kallansa ta karayi tace “zaka iya dubomin inda yke zama?”

 Kai ya daga alamar to, samun kanta tai da jin haushin yanda yaki mata magana bayan yanzu ta ganshi yana dariya da Afreey koda yake dama tasan maza duk daya 

suke daga sunga mace yar kwalliya magana ta kare.

 “Barshi kawai, na kula bakada niyyar yi, just pretend you haven’t heard anything from me, jeka kawai.”

 Ga mamakinta gani tai ya juya, cikin kufula tace “tafiyar zakai?”

 Juyowa yai yace “I thought that’s what you said?”

 Ranta a bace ta mike tace “yaushe ka fara yin abinda nace?”

 Bata jira amsarsa ba tace “in magana ce dakai ka fito ka fada, just be your self.”

 Shiru yai yana kallanta kafin yace “abinda aka riga aka batashi banaji magana zata gyara shi.”

Zama tai sannan ta Kalleshi  tace “me aka bata?”

 “Hotuna sun riga sun shiga wayoyin mutane da dama, sannan kowa a matsayin mijinki yake daukansa, inhar bake zaki……..”

 Da sauri zatai magana ta zubar da juice din data zuba a cup akan laptop dinta duka ya zube a jiki.

 Da sauri ya karaso kusa da ita, zama yai a kujerar da ke gabanta sannan ya ja laptop din.

 Da sauri yace “tissue.”

 Kallansa tai zatace yana can taga yana miko mata hannu alamar ta bashi.

 Kallan tissue din dake kan shelf tai sannan ta kalleshi, d’aga laptop din yai yana kallanta ganin bata da alamar daukowa.

 Kallansa tai kamar zatai magana sai kuma ta nufi inda yake.

 Ranta a bace ta dauko tana tunanin tunda take an taba sata miko abu? Mikamai tai ta hade fuska sosai.

 Baibi ta kanta ba ya amsa ya fara goggewa, sai dai ganin ya shiga ciki yasa ya kalleta yace “inada screwdriver?”

 Eh, dan bani.

 Kallansa ta sakeyi tace “yana can.”

 Kallanta yai yace “taimako fa nake?”

 Tace “ko taimako kake a kasa na kake na dauko tissue yanzu sai ka dauko kaima”

 Kallanta yai kawai sai taga yasa murmushi, fuska ta daure sosai tace “meye?”

 Yace “badai ba’a tava saki dauko abu ba?”

 Kauda fuskarta tai ta dan matsa daga kusa dashi tare da zama a d’aya kujerar tace “how do you know?”

 Sake murmushi yai yace “rike wannan to, dan inba haka ba wanda ya shiga sake shiga zai.”

 Kallansa tai tace “wai sai dai ka sani aiki?”

 “Ko na tafi?”

 Cikin hade rai ta amsa tare da kauda kai, ina yke?

 Tace “can.”

 Can ina?

 Ya tambaya yana sake kallanta, haushi ya kara kamata tace “dawo ka rike na dauko.”

 Da saninsa dan ya gani komawa yai ya amsa ita kuma ta mike fuska a daure ta dauko, da karfi ta ajiye a gabansa.

 Yazo dauka ta janye tace “kana san cemin baka ganshi ba?”

 “In na ganshi mexaisa na dawo?”

 Harararsa tai tace “ya akai nake ji kamar da saninka?”

 Hannunsa ya mika mata yace “kin tabbatar ba ra’ayinki bane yasa kike jin hakan?”

 Mikamai tai da karfi, amsa yai ya fara kuncewa.

 Kallan abinda yake tai sannan tace “karasa maganar ka ta dazu.”

 Bai kalleta ba yace “ki sanar da komai da kanki, even though it will get harder at first, amma atleast ba wanda ya isa ya shiga miki bincike tunda kin riga 

kin rufe bakinsu.”

 Nayi wannan tunanin amma in yan jarida suka nemishi suka tambayeshi dalilin rabuwar mu fa kafin nai magana da kaina? Ko kuma suka nemi yarinyar fa?

 Dagowa yai yace “Raziyya?”

 Ganin yanda ta kauda kai yasa yace “Raziyya bazatace komai ba, am sure dan da dama ba cutar dake tazoyi ba, sannan bazataso tayi abinda iyayenta zasuji 

ba.”

 Wani kallo ta mai sannan tace “da alama kasanta sosai tunda harkasan abinda zatai da wanda bazatai ba, ko da yake wanda ya tsaya yana dariya da wace bai 

dade da saniba meye bazai ba.”

 Kallanta yai duk da bai fahimci kalamanta ba amma yasan magana take gasamai, mikewa tai tana neman komawa daya bangaren, da sauri yace “rikemin wannan.”

 Kallansa tai ranta a bace tace “naki na rike.”

 “Tunda taimako nake zan iya tashi nima.”

 Tace “jeka kafi ruwa gudu.”

 Dagowa yai ya kalleta yace “ gaskiya ce bakyaso a fada?”

 Gaskiya? Hakan shine gaskiya? Hannunta ta daura akan desk din tace “ace ma gaskiyar kake fada kai baka iya magana cikin sanyi ba?”

Kallanta yai idanunsa na cikin nata yace “na iya.”

“Ni kadai kake ma kenan?” Ta fada tana kallansa

 Kallanta ya sake yce “Ummm”


Haushi ya kamata tace “Then why?”

 Mika mata keyboards din yai sannan yace “I don’t know.”

 Amsa tai ta ajiye akan desk din sannan tace “you don’t know?”

“Hmmm I don’t know why”

 Komawa tai daya bangaren ta zauna tare da dauke kanta daga inda yake.

 Cigaba da gogewa yai yna cewa “in na samoshi zaiji abinda zaki cemai?”

 Shiru tai kafin tace “I don’t know”

 Yasani sarai ramawa tai hakan yasa ya kalli agoggo karfe 6 ce ta buga.

 Shiru sukai ya karasa gyarawa sannan ya mike yace “zan nemo inda yake, i will send you the address.”

Harya kai bakin kofa ya juyo ya kalleta yace “amsar da kike nema tana gunki, trust your self”


Dagowa tai ta kalleshi, juyawa yai ya fita.

 Kofar ta zubawa ido shiru tai tana tunani, meyasa da bata taba neman taimako agun wani duk runtsin da zata shiga kuwa, harsai ta samo yanda zata warware 

komai, amma yanzu me yasa take san jin ta bakin Khalid?


 Kallan screwdriver da tissue din tai sannan ta kalli laptop din.


*****

Yana kokarin fita yaji Afreey tace “sai yanzu ka dawo?”

 Juyowa yai ya kalleta cikin mamaki yace “baki tafi ba?”

 Kallansa tai tace “kace bakomai tsakaninku.”

 Kallanta yai dan baisan sanda ya fadaba kuma baiga dalilin amsawa ba.

 Wayarta ta mikamai bani number Adam, kallanta yai yace “kimai me?”

 Ince ya maida matarsa.

 Ido ya kura mata sannan yace “Please Safiyya, karki soma yin wani abu, I don’t know what you are thinking amma koma meye a ranki i ask you to please stop, 

in kuma har kikai abinda zai sa mutane shiga matsala saboda ra’ayinki i will never forgive you.”

 Yana kaiwa nan ya juya ya fara tafiya, ranta ne ya kara baci tace “in ka aureni ka yafemin.” Ta fada cikin kishi.


 *******
Da sauri Raziyya ta mike zaune tana kara kallan hotunan, kafa tasa ta ture hannun Jamil da yake shafa mata mai a daya kafar, cikin takaici tace “bai saketa 

ba kenan ko me?”

 Kallanta Jamil yai yace “na dauka kin tabbatar bazata dauki raini ba?”

 Tace “haka na dauketa da alama nice nake mata kallan jaruma.”

 Hoton ta kurawa ido ranta a bace tana huce.

 Yace “yanzu me zakiyi?”

 Tace “kome zanyi sai nayi dan Allah sai auran nan ya rabu.”

 Shiru Jamil yai kafin yace “nifa inaga akwai abu a kasa, in ba haka ba me zaisa ta koresu?”

 Shiru tai tana tunani kafin tace “fita ka nemomin inda zan sameshi.”

Kallanta yai yace “yanzu?”

 Wata muguwar harara tamai tace “dazu”

Mikewa yai da sauri ya fita.

 Cikin kuluwa ta cilar da wayarta gefe.

********

Washe gari da safe

Goggo dake tajin dadin kudin da suka samu dan jiya shinkafa da miya tai itama yau kuwa indomie suka dafa da kwai soyayye, ta kalli Adam tace “ashe dai d’an 

nawa jarumi ne ban taba tunanin daga fita xaka dawomin da makudan kudi ba.”

Cikin isa da mulki ya kai lomar indomie yace “ai ki bari kawai, daga nuna musu hoton auranmu nida Zainab suka cake min kudina.”

 Shiru tai tana tunani, karfa abin ya jawowa Zaimab matsala? Sai dai can tace koma menene ai ita taja data bamu gida ai duk da ba haka ba kome ya sameta 

muma ba hannunmu a ciki.

 Kallan Adam tai zatai magana sukaji ana magana a tsakar gida, kallansa tai tace “wanene?”

 Loma ya karayi sannan ya leko yace waye?

 Kallansa mutumin yai Kamalu yace “shine.”

 Adam ya kallesu cikin rashin fahimta, mutumin cikin jin dadi ya mikamai hannu yace “d’an jarida ne ni sunana Aliyu Giss ma’aikacin gidan tv na Farin gani.”

 Adam ya kalleshi yace “sai akai me?”

 Dan Jaridan yace “muna bukatar yin hira dakai ne in har ka amince zamu baka dubu talatin kudin yin hira dakai.”

 Da sauri Adam yace “dubu talatin”

Goggo dake daki ta leko da sauri tace “dubu Talatin?”

 Yce “eh.”

Kallan Goggo yai itama ta kalleshi.

Mikamai complimentary card dinsa yai yace “inkayi shawara kamin waya da number nan.”

Adam y amsa hannu na rawa, Aliyu Jiss ya juya ya fita, waya ya daga ya kira wata number yace “Hajiya mungode da taimako.”

Kashe wayar yai cikin jin dadi, dan dama sun dade suna bakin cikin aikin da Zainab take da d’aya gidan tv din wanda sun tabbatar saboda itane suke ta samun 

cigaba wanda a yanzu su har mantawa ma ake da su.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button