NOVELSUncategorized

A GIDANA 6

*Haske Writers Association*馃挕

Shafi na shida
   Duk yanda yaso karya nuna bacin ransa amma wannan lokacin ya kasa, mekenan? Dan yana neman abinyi shine zai zama wulakantace? Ai ta tsaya taji mezaice.


聽 Zainab kam tana shiga ta tsaya a jikin kofa sannan tace was i mean? To mezance? Yanata wani cemin excuse me, ko suna nane hakan ai sai haka, juyawa tai taga bataga Nusaiba ba.

 Nusaiba kam tsayawa tai cak ta kasa dauke ido daga kansa, can ta hangota zaune kusa dashi ta sa kanta a kafadarsa tana bacci.

 Sam baima kula da ita ba sai dayaji an bude kofar, Zainab ta kalleta tace 鈥渕e kike anan?鈥�
Gaba daya Nusaiba batama san tana yi ba, jin magana ne yasa ya kalli gun, sai yanzu ya kula da yarinyar dake tsaye agun.
 Zainab ta kalleta sannan ta kalli inda take kallo, hada ido suke wanda Khalid yai saurin kauda kansa, Zainab tasa hannu ta juyo da ita saitinta tace 鈥渓afiya?鈥�

 Nusaiba tace 鈥淎unty kamar mafarki nake ko?鈥�

 Kallanta tai sannan tace 鈥渕afarki anan?鈥�

 Nusaiba ta daga kai tana wani irin murmushi, Zainab ta ja hannunta suka shiga ciki.

 Khalid waya ya dauko ya kira number Adam, Daga can Adam yana tafe yana shan kidansa, parking yai a gaban wani shago ya shiga ciki, shago ne dayake ta ganinsa satin nan da alama ba鈥檃 dade da budeshi ba.
 Shiga yai yana kallan kayan dake cikin shagon, shago ne na kayan sawa, na mata dana maza.

 Haryana kokarin fita yaga wani takalmi, wanda ya dau hankalinsa, dawowa yai da sauri ya daga takalmin, duba size din da yake sakawa yi ya nufo gun biya yana kokarin bada kudin ta nufo gun rike da wata riga ahannunta, abaya ce rigar, duk rigar jikinta tayi kacha kacha.

  Mikama mai biyan kudin tai, kallanta yai sannan ya kalli Adam yace 鈥渄ubu goma ne.鈥�

 Adam ya mikamai katinsa ya biya, hankalinsa a kwance.

 Haryadanyi gaba yaji yana cemata 鈥渄ubu biyu.鈥�

 Kallansa tai tace 鈥渕alam dan Allah kabarmun dubu daya da dari biyar wlh jakata aka sacemin duk kayana dana taho dashi, dubu biyun nan dake jakata su kadai gareni.鈥�

 Kallanta yai yace 鈥渒iyi hakuri hajiya amma ba shagona bane.

 Harzaj juya ya dawo ya mika katinsa, ba tare dayace komai ba, mai shagon ya kalleshi yace zaka biya?
Adam ya juya kai, nan ya sa pin dinsa ya biya ya juya yai gaba.

 Da sauri ta biyoshi tana cewa 鈥淢alam! Malam!鈥�

 Adam sai dayaje gaban mota ya juyo matsowa tai da sauri tace 鈥渘agode, ka taimakeni, zuwa na kenan garin kano aka sacemin kayana gaba daya……..鈥�

 Wayarshi datai kara ita ta katseta? Daukan wayar yai ya shiga mota ya ja yai gaba.

 Khalid ya?

 Daga can Khalid yace 鈥淎dam dan Allah kana ina?鈥�

 鈥淕aninan a hanya yanzu zan karaso.鈥�

 Khalid yai ajiyar zuciya baice komai ba.

 鈥淲ani abin ya faru ne?鈥�
Ya fada a ransa yana cewa yasa ai Khalid bazai taba jurar halin Zainab ba wannan aikin nasu ya basu wata daya in anyi nisa.

 鈥淣o sai kazo.鈥�
Adam yace okay, ya kashe wayarsa, yana tafe yana shan kidansa, hankalinsa a kwance, tunowa dayai da Goggo ne yasashi kara sauri, yasan kila ma ta fada, mai yakaishi tsayawa a shagon can? Sam yama manta abinda ke gabansa.

 *******

Zainab kam suna shiga ciki ta makama Nusaiba harara tace 鈥渒in gama mafarkin?鈥�

 Nusaiba ta kalleta ta matso kusa da ita kamar zata shige cikinta tace 鈥淎unty wanene dan Allah?鈥�

 Zainab ta kalleta tace 鈥渨a?鈥�

 Nusaiba ta kalli window tana nuna mata Khalid dake tsaye yana waya.

 Zainab tace 鈥渕enene damuwarki dashi?鈥�

 Kara rike ta tai tace 鈥淎unty dan Allah ina gama secondary ku aurar dani, ku bani shi.鈥�

 Kallan mamaki Zainab ta mata  kafin ta girgiza kai tace 鈥淣usaiba da alama kin samu matsala.鈥�

 Tai ciki tana cewa 鈥渋na Nabila?鈥�

 Tana daki, Zainab ta wuce cikin dakin nasu.

 Nabila na zaune akan gado tanajin an bude kofar ta boye abinda ke hannunta da sauri.

 Zainab ta maida kofar ta rufe sannan ta nufo inda take, Nabila ta kalleta tace 鈥淎unty kin dawo?鈥�

 Zainab ta matso bayanta tasa hannu ta zaro abinda ta boye, littafi ne na makaranta ta bude cikin litaffin tare da girgizashi.

 Hoto ne ya fadi daga cikin littafi, Zainab zata dauka Nabila tai saurin daukewa ta boye.

 Mika mata hannu Zainab tai tace 鈥淏ani.鈥�

 Nabila ta kalleta idanunta suka ciciko, Zainab ta hade rai tace 鈥渂akiji ba?鈥�

 Jiki a sanyaye Nabila ta mika mata hoton, tana amsa ta juya baya hoton, sai dai me? Gaba daya yanayin fuskarta ne ya canza, idanunta suka canza, a hankali ta dago ta kalli Nabila wacce hawaye suka zubo mata.

 Zainab ta zauna kusa da ita, ta zuba mata ido cikin tausayawa.
 Nabila ta share hawayenta tace 鈥淎unty.鈥�

 Zainab ta sa hannu ta karasa goge mata hawayen sannan ta kalleta tace 鈥渂adai haka kikeyia makarantar ba?鈥�

 Kai ta girgiza da sauri alamar a鈥檃 sannan tace 鈥渘a dade Allah banyi ba.鈥�
 Zainab tai murmushin yake tace 鈥渒afin mutanen gidan wu gane, ki tashi ki ware, ina mai bakin tsiwar tawa take ne? Ina mara hakurin nan da neman fada yakene?鈥�

 Nabila tasa dariya tace 鈥渒ai Aunty.鈥�

 Zainab tace ba haka bane?

Nabila tana dariya ta mike tai waje.

 Shiru Zainab tai a dakin, tare da kara kallan hoton hannunta, raunin datake boyewa nata kar a sani shine ya nemi tasowa, hannunta ne ya fara rawa da sauri ta mike tare da bude windown dakin dan tasha iska saboda zuciyarta tayi nauyi.

 Wani nannauyan ajiyar zuciya ta saki tare da kallan waje, Daga can gefe ta hangoshi tsaye yana waya, Excuse me! Excuse me!

 Abinda ta tuno kenan, ko baka san sunana ba ai sai kawai kai maganar da kakesan yi Excuse me din na menene? Taja dan gajeran tsaki tana neman zuge window din taga ya kalli gefe, sai kuma taga ya dan daga hannu kadan ba wani alamar sakin fuska hannun dai yadan daga.

 Da sauri ta fito daga dakin ta nugi falo, Nusaiba!

 Abinda ta fada kenan, Nusaiba ta kalleta da sauri, sannan ta zuge labulen windown.

 Zainab ta kalleta, da sauri ta boye a bayan labule tace 鈥淎unty gaisheshi kawai nai.鈥�

 Nabila wacce tana fitowa kitchen tai ta zubo abinci tace 鈥渒aryane kafeshi tai da ido wanda inaji daga nan sai daya kware.鈥�

 Zainab duk yanda taso ta hade rai sai datai dariya tace 鈥渞uwa yakesha kenan?鈥�

 Nabila tace 鈥渆h mana.鈥�

 Nusaiba ta sa dariya harda faduwa tace 鈥淜anwa uwar hadi, wlh andaiji jiki.鈥�

 Nabila ta kalli Zainab tace 鈥淎unty wanene?鈥�

 Zainab tace 鈥渙h bakimasan me ake cewa ba kike shiga abinda bai shafeki ba, ni ina Goggo ne?鈥�

 Nabila tace 鈥渢a tafi siyo anko wai ita da kawayenta……..鈥� ta karasa maganar tana dariya.

Nusaiba ma dariya tasa tace 鈥渨ai anko, ina Goggo ina anko?鈥�

 鈥淢eye naku a ciki? Kunga ku kiyayeni da wannan bakin naku.鈥�

 Jin karar gate ne yasa Nusaiba ta bude labule, Oh Uncle, ko ina yaje?

 Hala majalisa, Nabila ta fada tare da zama.

 Shiru Zainab tai tana tunanin abinda yace mata, ciki ta wuce kawai ta shiga daki, alwala tai kawai ta sa hijab ta tada sallah.

*****
  Adam na parking ya matso gun Khalid dake jiransa, hannu ya mikamai suka gaisa yace 鈥淜waro ya?鈥�

 Khalid yace 鈥淎dam please ka daina kirana da haka.鈥�

 Dariya Adam yai yace 鈥淭o Kwaran danbatta shikenan?鈥�

Khalid ya fahimci rainin wayau ne shiyasa bai tankashi ba yace 鈥渟o nake naji me da me zandinga yi saboda in san yanda zan tsara komai.鈥�

 Tsara komai? Kaida kazo aiki? Abinda Adam y fara kenan a ransa amma a fili yai dariya yace 鈥渄a farko dai sai kayi hakuri dan Hajiyar akwai fada kamar…..鈥� yamai rada a kunne, wanda nima banjisu ba.

 Sannan ya dago yace 鈥� abu na biyu gaskiya aiki ne ya ganka saboda journalists ce babba wacce kuma take uwar aiki wato agoggo kenan, dan ko na kasa da ita sun kawo report na abinda suka dauko wani abin bata yarda dashi harsai taje da kanta ta gani, ta tantance, sannan sau da dama takan je gurin da kanta dan rashin yarda da aikinsu, tafisan ayi a gabanta.

 To kaga duk wannan lamari kaine zaka dinga jelar kaiwa da dawowa, sannan sukan tafi wani garin dan dauko rahoto ko kuma meeting nasu na yan gidan tv da sauransu.

 Abu na karshe tana fita karfe bakwai da rabi na safe ta dawo karfe shida na yamma, sannan daga gun aikin tana yawo sosai.鈥�

 Khalid ya kalleshi sannan yace 鈥� nagane, weekend fa kamar yau?鈥�
Adam yai dariya yace ai kai bakada hutu dan wannan bansan kai na nawa bane a wadanda ta kora wani da kanshi ma yake gudu saboda wahala.

 Khalid ya kalleshi yace 鈥渘i ba wannan bane damuwata, abu daya nakeso in fada, zan fara aikin nan ina naiman nawa aikin, da zarar na samu aiki zanyi resigning.鈥�

 Adam yana dariya yace 鈥渂akimai sai dai fa karka manta neman aiki yanzu a kasarnan sai da hanya, waya sani ko in ka daure Hajiya ta nemar ma.鈥�

 Ba karamin sosa mai zuciya wannan kalaman sukai ba, murmushi yai yace 鈥渘i Adam wani aiki kake ne? Naga har weekend kamar kaima kana aiki?鈥�

 Ran Adam ya baci wanda ya bayyana a fuskarsa, kallansa yai yace 鈥渕enene?鈥�

 Khalid yace 鈥渂akomai kawai dai tambaya nai naji kamar rannan kacemin kai matarkace mai kudin ko? Ita take baka, haka dai kamar naji, amma sai nake tantama dan nasan yanda kake da san kai abu da kanka kamar bazaka yarda ka zama mijin Hajiya ba.鈥�

 Fuskar Adam ta murtuke sosai yace 鈥渕e kakesan cewa ?鈥�

 Khalid yai dariya yace 鈥渕e zance kawai cewa zanyi ko dayake mijin Hajiyar ma matsayi ne.鈥�

 Adam ya washe baki yana dariya yace 鈥渟osai ma dan banaji irinku zasu samu.鈥�

 Khalid yace 鈥渟osai, bare kuma ni kasan bansan a bani, bari na wuce zanje Cafe ne.鈥�

 Adam sam bai fahimci magana ya fadamai ba yace 鈥渁 ina zaka dinga kwana? Muna da dan daki, ya fada yana nuna wani daki can dake gefe, da sauri Khalid yace 鈥淪aida safe.鈥�

 Ya mika mai key, haryayi gaba ya dawo yace 鈥淪orry Adam me nene salary dina sannan yaushe za鈥檃 dinga bani?
 鈥淎m sorry but inasan sani ne dan na san yanda komai yake tafiya.

 Adam yace 鈥済obe in kazo zata baka contract din sai ka sa hannu, dan nima bansan yaushe take biyansu ba.鈥�

 Khalid ya mika mai hannu sukai sallama ya tafi.

 Yana fita yabi kofar gidan da kallo, tabbas dole ya kara zake dantse ya nemi aiki dan bazai iya jurar wannan aikin ba.


 *************

 Wajen karfe 9 na dare ta shigo dakin yana zaune yana latsa waya ta shigo, kwanciya tai tare da rufe idanunta, kallanta yai yace 鈥渢un dazu nakeso kizo muyi magana kiji yanda mukai da Khalid.

 Kallansa tai sannan tace 鈥淒azu kaje majalisa ne?鈥�

 Da sauri yace 鈥渁鈥檃 takalmi naje siyowa.鈥�

鈥淢eyasa kamin karya to kace kaje siyoma Goggo magani?鈥�

 Yace 鈥淪orry honey lokacin ina bank ne banasan yin doguwar magana.鈥�

 Ido ta kuramai, sumbatarta yai yace 鈥渂anace miki na daina zuwa ba? Ko baki yarda dani ba?鈥�

 Murmushi tai ta rungume shi tace 鈥渒aima kasan duk duniya kai kadai ne namijin dana yarda dashi.鈥�

 Kanta ya shafa yana fada mata yanda sukai da Khalid, kallansa tai tace 鈥淗oney are u sure wannan mutumin zai yi? Nifa sam hankalina bai kwanta dashi na, sai naga kamar ma fada yakemin.鈥�


 Dariya sosai Adam yai kafin yace 鈥淵au wacece wannan anya Zainab ce?鈥�

 Tace 鈥淎llah ni yau saura kadan ma na koreshi.鈥�

 Adam yace 鈥渂a fada yake miki ba haka maganarsa take, kinsan a skul sam bashida friends na kudakud? Duk wanda kika gani dashi to fa morarsa yake, saboda iliminsa ne yasa muke juremai, sai daga baya kowa ya gane haka yanayin maganarsa yake.鈥�

 Zainab tadan tabe baki tace 鈥渟ai kace shi kadai ne bashida friends.鈥�

 Adam yace 鈥渒e da shi akwai banbanci, ke kece bakyasan friends din, shi kuma mutane ne bazasu iya jurar halinsa ba, kinsan daga farko kowa ya dauka dan mai kudi ne?鈥�

 Murmushi tai tace 鈥渨hy?鈥�

 Nan ya fara bata labari hartai bacci.


 Wajen karfe uku ta farka a zabure, addu鈥檃 ta shiga yi ta kalli Adam wanda ke kwance yana bacci, mikewa tai ta fito falo, kofar dakin su Nabila ta bude, suna kwance suna barcinsu wanda hakan ya sata murmushi.

Dauko hoton dazu tai ta zauna a falo tana kallanta? A hankali tai murmushin dayafi kuka ciwo tace 鈥淢amana…..鈥�

 Nabila wacce taji sanda aka rufe kofa itace ta bude kofa, kallan Zainab tai da sauri ta taho gunta ta rungumeta.

 Zainab ta kalleta tana hawaye ta rike hannun Nabila tace 鈥淣abila ba abinda ake miki?鈥�

 Nabila tana kuka tana cewa 鈥渒ema Aunty kinsan bazan bari ba.鈥�

 Zainab ta daga kai tana murmushi tace 鈥渘a manta My boss ce.鈥�

 Nabila tai shiru cikin yanayin damuwa, Zainab ta kalleta tace 鈥淢aman Nusaiba na takura miki ne?鈥�

 Tace kema kinsan ni, Aunty karki bari Uncle ya miki abinda Dady yama Mama, shi yasa sam nikam banaji zan iya aure har na mutu, Aminiyarta, a kullum……鈥�

 Ya akai kika sani?
Tambayar da Zainab ta jefe ta dashi kenan tare da mata kallan zargi.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button