AMANA TA CE Page 31 to 40

don tasan yana da zuciya sosai haka sukayita rayiwa abunu tausayi.
Abangaren ammar kuwa kasuna tafiya dai2 har yayi customer a kwai wata hajiya datake yawan sayan kayan salad da fruit agunsa da vegetables har sun saba wataran kam yarta take turowa tasaya agunsa hakan dai yaci gaba da dana’arsa, auta ko sai rama take kulum in yasata a gaba yana tambayanta tace bakomai haka zai gaji ya kyaleta.
* * * * *
Zaune yake a gaban kayan fruits wata bakar HONDA CRV TA cike da nuna isa da gadara take taku tun daga nesa mutane ke kallonta sabida ta tafi dasu ga ta da kyau tafiya take kamar bazata taka kasa ba kai daga ka ganta kasan naira ya zauna ma iyayenta da fatarta sannu a hankali ta tsaya tana kallon yar fruits don ita bataga wanda mum tace tazo gunsa ba har taxo zata juya ta hango wani dogon saurayi fari mai kyau tamkar sharukan kalo daya za kamasa ya tafi da tunanin mace don daga ka gansa kasan baragon namiji bane kuma mijin nuna ma sa’a ne kasa kyafta idonta tayi akansa shiko bai ma san anayi ba wai kunu a wani gida, ko tan tama babu shine Ammar din da mum take sayan kaya a gunsa, woow amma guy din ya hadu matsalar daya ne rashin naira sai da taji wani mai saida fruit na gefen ammar yana cewa hajiya kaya za a baki kafin ta dawo tunaninta a gadaran ce ta isa gun ammar tace aslm ya kk tambaya nake wai wani shi ammar fiska ba yabo ba fallasa yace eh nine ammar din lfy cikin isa tana satan kallonsa tace hajiya Maryam Alkali ne ta aiko ni wacce take sayan kaya a gunka yace ok ina jinki nan tace wai ka hada mata kaya kamar yanda take saya nan Ammar ya hada mata kaya masu kyau ta bude jaka ta dauko kudi ta basa tsabagen kallon da take masa ta yarda posd din ta garin mayar wa jaka bata sani ba sai da ta bar gurin zuciyarta cike da tunani ammar har ta tada motarta ammar yaga poss ya bita amma ina tayi nisa nan ya budr sai yaga ID Card dinta da dunanta Munayshat Alkali nan yaga complement card dinta da address dinta da sauri ya tsari mai mashin ya bi bayanta.
1 To masu karatu danso musan wacece Munayshat? Kuma wacece Hajiya Maryam Alkali?
2 Shin munayshat son Ammar takeyi zai amsa kuwa to ya rayuwan auta zai kasance
Kubiyo Yar gidan JARAWA don jin yanda zata kaya taku a kulum mai kaunarku Yar Mutanen Kardam.
®WISDOM HAUSA WRITERS
Rash Kardam
[7:38PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Ganin tayi nisa yasa ya bi bayanta da gudu sukeyi da mai mashin amma ta musu nisa sai da sukaje G R A adjacent da government house naga naga sun nufi wani katon kwalta ne a shimfede kafin suka iso kofar wani hadadden gd harda security a kofar ginan tun daga kwanar shiga gidan zaka ga arubuta Hajiya Maryam Alkali house, da manyan zane, nan ya sallami mai mashin ya basa N100 kudin mashi mai gadi suna ganinsa suka tashi nam sukace wajen wa yazo yace gurin wacce tashiga da mota mai gadi yace ka bar gurin nan bazaka shiga ba nan suka fara iskanci ma ammar ransa har ya baci ya juya zai tafi sai daya mai gadin yazo ya tambayesa nan yace wacce ta wuce da mota yanzu baka mai gadi yace ai gidan nan masu tuka mota suna da yawa nan ya sake duba sunan yace Munayshat ok lfy dai ko yace lfy wa za a ce mata nan yace ace Ammar mai kayan fruits nan security ya shiga nan yayi karo da Aunty Mamu a falo ga Kausar a gefenta nan yace Aunty wani ne yazo gun munayshart wai Ammar mai sayarda fruit nan hajiya maryam ta fadada murmushinta ayya ammar lfy daiko yace eh wai abu yakawo ta nan aunty mamu tace kaje ka shigo dashi, kausar mikewa tayi ta nufi kitchen don dauko mult mai sanyi tasha,
Bayan ya koma ya shigo da ammar gasky gdn ya tsaru a kwai naira a gdn sosai don ya hadu iya haduwa da sallama suka shiga cikin falon da yasha blues da yellow da bakin labule ga kujeru luntsuma luntsuma suma colours din blue yasha gyara ga kamshin da yake tashi ya duka ya gaida ta nan yace shaidata mata yarta tazo sayan kaya gashi ta yar da poss dinta nan tayi godiya ta karba hauwa mai aiki ta kira tace ta kawo masa abinci yace ya gode hajiya ta bata rai ammar ae mun zama daya ka dauken tamkar uwa a gunka cikin jin dadi yayi godia hauwa ta kawo masa zobo daman shi ma aboci zobo ne ya sha kayan hadi nan ya dauka ya sha gashi da sanyi nan ya wani lumshe ido alamar jin dadi,
Kausar ta fito rike da malt a hannunta tun da ta nufo falo ta hangi wani hadadden saurayi ajin karshe ga kyau sai da ta furta woow a zuciyarta nan take taji ya tafi da ita amma jin kai ta danne ta shigo da sallamarta dake ita tana da hankali sosai ta gado halin Aunty Mamu ne gefen mum dinta ta zauna cikin isa tace masa sannu da zuwa yauwa yace a takaice dai2 nan munayshart ta shigo cikin wasu matsatsun kaya riga da wando na English wears tayi kyau sosai don suna da kyau ba laifi sai dai matsalar rashin gashi don sai da ta hada dana doki tun da taga ammar tashiga wani yauki tana karairaya wanda shi bai san tanayi ba ma nan Mamu ta bata poss dinta nan tace la ban lura ba ko da ta bude taga kudinta ba a tabasu ba 80k ne a ciki don harda zonen gwal dinta da yakai 60k aciki kirar dubai sai daukar ido ya keyi nan tace lah mum gsky na da AMANA kiga ga kudi kusan 80k ga zobe na nagode duk da nasan koda bata sukayi banda wasu matsala amma gsky da kanuna naji dadi nan ya mike da nufin tafiya cikin sanyin murya yace hajiya zan tafi tace angode kausar kam kasa motsi tayi sabida zakin muryansa amma dake ita tana da kamun kai ga jan aji shiyasa take buyewa har ya kai kofa Aunty Mamu tace Ammar in bazaka damu ba ina son zan tambayeka cikin ladabi yasoma takowa ya dawo in da ya zauna ya sake zama kansa a kasa ammar dan Allah ina son kafadan gsky waye kai daga ina kake don daga alamar baka dade da fara sayar da fruit ba don na dade ina zuwa gun bana ganinka san nan yanayinka baiyi kama da wahala ba a kwai wani boyayen sirri atare da kai cikin nutsuwa ya daga fuskansa nan suka hada ido da munaysharr da ke wurga masa shu’umin kallo Kausat ma kallonsa ta keyi ajiyar zuciya yayi kafin ya sake sukiyar da kansa cikin nutsuwa ya fara magana.