ABBAN SOJOJI BOOK 2 COMPLETE

Fitowa parlor dinsa yayi yasamu wuri saman sofa yazauna hannunsa ruƙe da wayarsa, sai lokacin yake dana sanin rashin daukar su hosana da jahad hoto ya ajiye acikin wayar shi koya samu na rage kewarsu, yana cikin wannan tunanin wayarsa ta soma ruri karatun kur’ani Ne ringin tone dinsa duba sunan daya bayyana a screen dinsa yayi nan take sunanABUSUFYANya bayyana muraran,
Cikin hanzari ya ɗaga ya kara a kunnansa “Assalamu Alaikum Uncle Sufyan yau an tuna dani ne”?
On ther other hand ABUSUFYAN yace “Ko da yaushe cikin tunawa nake yi dakai Omar, nayi trying number dinka dazu baya shiga, kuma na jaraba ta RAFAYET tana ringing amma bai ɗaga ba,’
Omar yace ” Kash ! rashin sani ɗazu ne na kashe wayar muna aiki ne shiyasa,”
Abusufyan yace “Dama inaso na maka magana ne About wannan yaran da goggon katsina ta ƙaƙabamun a matsayin ya’ya na”?
Murmushi Omar yasaki kamar yana agabansa yace “Ae ko ɗazu da safe ta kira ni awaya, kusan kullum ne sai ta mun Complain akan ƴa’ƴan abusufyan ɗinta,’
Abusufyan yace”Allah sarki, Nima tana kira na tana mun complain akan nasa ka mayar mata da ya’yana wuri ta, ynx ina yaran suke ne? Ya tambaya yana jiran amsa
Omar yace “A gidan general ishaq suke da zama, can na kaisu,”
“Ina iyayen su suke ne”? Ko yan uwan matar ishaq din ne? Ya tambaya
Omar yace “A’a Uncle yaran fa basu da kowa kamar yadda suka sanar mun, na haɗu dasu ne a asibiti cikin mawuyacin hali tagwaye ne baza su wuce 17years ba Suna buƙatar taimako,
Ajiyar zuciya abusufyan yasaki kafin yace “Meyasa ba zaka dawo dasu nan ba cikin abuja kusa da kai ba”?
“Uncle kaima ka sani, zaman su anan bazaiyi yu ba, maza ne mu duka duk ba wannan ba AMMI bazata ta6a lamuntar wani bare ya zauna acikin jinin ta ba,especially su da suka kasance basu da asali,’ bayani yake masa tamkar yana agabansa
ɗan gyaran murya abusufyan yayi kafin yace “Listenin to me OMAR! kana da kyakkyawar niyya akansu, inaso ka kaddara aranka cewa waɗannan yaran jinin ka ne, kasanya wa ranka cewa Ƴa’Ƴa na ne, ya’yan ƙanin mahaifin kane ABUSUFYAN ina so ka basu kulawa Omar ! Dan Allah kada ka bari su wulaƙanta kayi mun wannan alƙawarin…….
Jikin Omar ne yayi mugun sanyi jin abun da Uncle Abusufyan ke faɗamasa, yanayin sautinsa da yadda yake yin kalamansa haƙiƙa ya ta6a Zuciyar Omar sosai, tunani omar yashiga yi aransa har sai da Abusufyan yace”Naji kayi shiru OMAR,”
Cikin sauri yace “Insha Allah Uncle i wll take care of them more than u think, nima inajin su araina sosai Uncle, ina ƙaunar yaran har cikin raina,
yana iya jiyo sauke ajiyar zuciyar Abusufyan alamar hankalinsa ya kwanta kuma yasamu natsuwa da bayanin Omar,
ABUSUFYAN yaci gaba da cewa “OMAR! INA SO KA DAWO DA YARAN NAN GIDA NA DAKE ANAN SU CI GABA DA RAYUWA, KA SANYA MUSU SECURITY TARE DA MAI AIKIN DA ZATA KULA DASU, INA SO SU RAYU ACIKIN GIDA NA, KAYI MUN WANNAN ALƘAWARIN!!!”
runtse ido Omar ya ɗanyi yana jinjina kalaman Uncle din nasa daga bisa ni yace “Insha Allah Uncle zanyi komai kake so, zan dawo dasu nan acikin gidan ka kamar yarda kake so,”
Sun jima suna waya kafin daga bisa ni su kayi sallama, ya ajiye wayar yana mai tunani iri-iri aransa, yana ji aransa in ya ɗauke su hosana daga gidan aunty babba tamkar baiyi mata adalci ba don ya Lura tana son yaran kuma sun saba dasu anya kuwa zai iya cika alƙawarin Uncle Abusufyan Na dawo dasu hosana cikin Abuja da zama!!? ????
Yana cikin wannan tunanin Sehrish ta shigo da sallama, batare da ya ɗago ya kalle ta ba ya amsa mata sallamar, sam ransa ajagule yake uncle dinsa ya ɗan ruɗa masa brain ɗinsa
Tray na a hannunta ƙarasawa tayi tare da gaishe shi “ina yini ya Omar,” ƙiris ya rage omar ya ɗago ya kalle ta saboda Voice dinta tayi mashi kama da ta JAHAD, amma yabar Abun a matsayin muryar mai aikinsu ne ya koma masa ta Jahad Saboda kewarsu da yayi sosai
Amsa mata yayi da cewa “Lafiya lou”
Ajiye masa tray din tayi mai dauke da food stuffs dinsa asaman table Din dake a front dinsa sannan ta juya takama hanyar fita tana jiyo shi yana furta “ngde,”
Sauƙin kan MARSHAL OMAR yana matuƙar burgeta, babu ruwan shi ba kamar SGR ba, yana da IZZA ta wani bangaren kamar abinci muddin takai masa sai tayi saving ɗinshi, amma Omar sam baya buƙatar wannan kawai daga an kaimasa shi yake zuba abunshi yaci,
Saukowa tayi down a lokacin har su Twins da kanal yusuf Sun hallara suna cin dinner dinsu, tayi mamakin ganin babu Abbansu da junaid may be yana a part dinsa azmee takai masu acan
Gaishe su tayi gaba ɗaya suka ɗan dago suna kallonta, Kanal yusif ya amsa mata da sakin fuska amma Ayaan da jahan kuwa sai dai suka bita da ido,????
Har bugun zuciya take ji in ta gansu cikin hanzari ta shige kitchen ta shirya ma SGR dinner ɗinsa ta fito ɗauke da tray ahannu ta nufi hanyar upstairs dinsa,
Da sallama ta shiga palor dinsa baya aciki, ƙarasawa tayi ta ajiye masa kayan abincin saman table dinsa, sannan ta ɗan dakata ko zai fito amma shiru babu alama,
. yanke shawarar zuwa bedroom dinsa tayi a bakin ƙopar shiga ta tsaya sannan tayi sallama, daga ciki taji ya amsa mata ƙasa ƙasa kafin ya bata permission ɗin shiga ciki,
A hankali ta zura ƙafa ta shiga ciki jikinta na ɗan kerma Hango shi tayi daga shi sai bathrobe ajikinsa kwance abaje saman gadonsa, alamu sun nuna cewa baiji ma da fitowa daga wanka ba, ya kwanta gajiya ce tayi masa yawa, idonsa na’a lumshe yace “Wanene ne,”
sehrish tace “mai aiki ce dama dinner ne na kawo maka yana a palor naga baka fito ba,
Jim yaɗanyi kafin yace “Tea kawai nake buƙata,akawo mun nan,’
Amsa mashi tayi da toh, sannan ta fuce ta koma palor dinsa ta ɗauko kayan tea din dake acikin tray din da ta ajiye anan sannan ta shigar masa dashi,
har gab da gadonsa ta ajiye masa saman madai-dai cin table din dake a wurin ta matsa masa dashi jikin gadonsa,
bin shi tayi da kallo saboda bai buɗe idonshi ba kuma baiyi yunƙurin tashi ba, yayi wani fresh dashi,
Ganin alamun fa zai iya zarcewa da bacci yasa tace “Na kawo maka Tea ɗin,”
“I knew,” ya bata amsa, jinjina kai tayi ashe yasan ta kawo ɗin, wahalar tashin ce kawai yake ji, kusan 15 mins sannan ya ƴunkura ya miƙe tare da sauko da ƙafafunsa ƙasa, rigar iya guiwar ƙafarsa ta tsaya, saukin yasa shorts daga ciki amma chest ɗin shi a buɗe yake fari kal,
Zuba mishi ido tayi tana kallon ikon Allah wani irin bacci ne ke fusgar shi, ga uwar yunwa yana ji, ji take tamkar ta bashi tea ɗin abaki yasha, cikin sauri ta haɗa masa tea ɗin a cup ta ɗan tura masa agabansa tace “gashi nan,’
buɗe blue eyes ɗinsa yayi a hankali sannan yakai hannu daker ya ɗauki cup ɗin yakai bakinsa yana ɗan kurba da zafinsa, ya sha ba laifi kusan sau biyu tana ƙara masa yana shanye wa,
Bayan ya kammala tace “kayan dinner ɗin fa na mayar dasu”? Ta tambaya cike da jin tsoran amsar da zai bata,
“In akwai fruits ki haɗo mun,” ya faɗi tare da mayar da jikinsa ya kwantar akan pillow,
Tattara kayan tea ɗin tayi sannan ta fuce dasu ta ajiye su a tray din dake ɗauke da warmers na abincin sannan ta ɗauke shi ta fita dashi kitchen ta shiga ta ajiye su, sannan ta ɗebo mashi fresh fruits acikin fridge,
A plate ta zuba mashi su sai da tafara yayyanka mashi su sannan, tana ƙoƙarin fita suka ci karo da Haroon tsaye abakin ƙopar kamar aljani,
Da ƙarfi ta furta “A’uzu billahi minashshaiɗanin rajim,’
Haroon ya fashe da dariya tare da cewa “Ni ne shaiɗan ɗin, ko kin ga ƙaho akaina ne?
“Eh,” ta bashi amsa,
Yatsina fuska yayi yana bin jikinta da kallon frm up to down kafin yace “Haɗaɗɗiyar Sura,”
tace “Tubarkallah masha Allah,”
Murmushi yaɗanyi kafin ya kuma cewa “ki dai bi ahankali naga kamar zakiyi rawar kai Kada kici ka zaƙewa mana domin kuwa har yanzu fa baki da wani matsayi acikin gidan nan, duk inda za’aje adawo bakya wuce ƴar aiki, sannan na lura kina shisshige ma wancan ifritun ko? to inaso ki sani wancan dashi da dutse duk ɗaya suke indai agame da feelings ne, mace bata gabansa koda zai kula matan ma bana tunanin irin ki, ae ma zaren ba kalar yadin bane iska ce kawai zata wahalar da mai kayan kara………
tun da yasoma magana idon sehrish suka soma ciccikowa da kwalla amma bata bari hawayen sun zuba ba, ganin zai bata mata lokaci yasa ta bi ta gefensa ta fuce da sauri, tana jiyo dariyarsa sam tarasa gane ma haroon, batasan mai ta tsone masa ba,
time ɗin da tashiga bedroom ɗin SGR samun shi tayi yana ta faman sharar baccinsa alamu sun nuna cewa ma tunda tasa ƙafa ta fuce ya fara baccin, tsayawa tayi akansa tana kallonshi hannunta na riƙe da fruits ɗinsa,
Yayin da idonta Suke cike da hawaye saboda kalaman haroon ita kanta tasani tabbas SGR ba tsaran yinta bane kwata-kwata bama haɗi, jinjina kanta tayi aranta tace “nasani kafi ƙarfina nesa ba kusa ba, kuma nasan cewa kafin ni akwai wanda suka ruga ni faɗawa wannan tarkon bila adadin, Amma inaji araina babu wadda zata soka dan Allah kamar yadda nake sonka, tun bansan ya kamannin fukarka suke Ba, da sunanka kawai nakamu da tsananin ƙaunarka kuma zan cigaba da addu’a akan hakan koda bazan ci nasara ba aƙarshe…Ana ahabbuk kasiran BABBAN YAYA………❤????
Wani irin juyi SGR yayi har sai da Sehrish ta ɗan tsorata gudun karya farka ya ganta, gyara kwanciyar shi yayi, yadda yake sakin numfashi anatse yana bacci ba ƙaramin tafiya yayi da ita ba,
Ajiye fruits ɗin tayi saman table sannan ta matsa a hankali cike da fargaba ta janyo lallausan blanket ɗinsa jikinta na ɗan kerma ta samu ta hayo dashi jikinsa ta lullu6a masa har zuwa neck ɗinsa,
Murmushi ta ɗan saki ganin ta kammala batare da ya farka ba, juyawa tayi ta tattaka izuwa inda makunnin hasken ɗakin yake ta kashe mashi shi, nan take ɗakin ya soma kyalli yana bada wani irin haske har sai da ta ɗan razana, ashe furnitures ɗin dakine masu wannan sparkling light ɗin launi daban daban suke badawa, aduk time ɗin da aka kashe hasken ɗakin Yayi dark gaba ɗaya su kuma sai su soma bada nasu hasken mai launuka, fuska ɗauke da murmushi sehrish ke kallon wannan ikon Allan Bin su take yi da kallo tun daga Bed ɗinsa da bedside table ɗinsa, drawer ɗin da ke ɗauke da mirrow jerin wurin Closet ɗinsa gaba ɗaya sun ɗau hasken nan, sai taga ya ƙara yi mata kyau sosai,
Lalla6awa tayi ta koma inda yake kwance tana kallon fukarshi yadda eye lashes dinsa suka fito radau zira zira dogaye kasancewar idon na’a rufe, sun kwanta luf,
Addu’ar bacci tashiga yi mashi saboda tasan cewa bai samu damar yi ba ayarda ya kwanta ɗin nan agajiye ta jima sannan ta ɗan tattofa masa ajikin bargonsa, kamar karta bar ɗakin haka take ji
(Nace ba mai zai hana kawai ki kwana anan Ehen ????)
hannu tasa ta ɗauki Kayan marmarin dake acikin plate ɗin sannan ta fuce dashi bakowa a babban falon Dama tun fitowar farko da tayi duk sun kammala dinner ɗinsu sun shige cike aranta tace “Allah sarki su fawan hada rashin su yasa yanzu basu cika haɗuwa atare suna cin abinci ba ko zama a palor suna fira, ko yaushe zasu dawo? Duk da ina tsoran abunda zasu ce in suka ganni a
Matsayin mace, Especially fawan nasan halinsa sosai baijin magana shine ya ta6a bani horo harna galabaita,” ta ƙarasa zancen zucin nata , bedroom ɗinta ta wuce da fruits ɗin saboda dama itama bata ci komai ba, asaman gadonta ta zauna tsakiyar gadon ta lankwashe ƙafa tana shan fruits ɗin tass ta shanye su sannan ta ajiye plate ɗin asaman side drawer ɗinta, dama empty yake tunda ta rotsa ma haroon fitilar saman shi akai, bata sake ajiye komai asaman wurin ba,
sauko wa tayi tashiga toilet saboda bata yi sallar isha’e ba, alwala tayi sannan ta dauko hijab ta zura bayan ta shimfiɗa carpet ta gabatar da salla,
Tana gama wa ta naɗe carpet ɗin ko addu’a bata tsaya yi ba, ta tura su cikin wardrobe sannan ta haye saman gadonta taja bargo ta kwanta daker tayi addu’a kafin bacci 6arawo yayi awon gaba da ita……………..(Shin ko kun lura cewa Sehrish ta manta dasu hosana da jahad bakamar da ba? hmmmmm rayuwa kenan baka ta6a sanin asalin ya mutun yake sai yasamu wurin zama koya samu abun duniya nan zaka ga zahirinsa????)