ABBAN SOJOJI BOOK 2 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 2 COMPLETE

_______________SEHRISH____________

Around 8 Ta farka kai tsaye kitchen ta wuce har time ɗin rigar jiya ce ajikinta da rolling ɗinta, a kitchen ta samu Azmee harta kusan kammala breakfast din gaba ɗaya, bayan tayi sallama ta shiga suka gaisa da junan su, Daga bisa ni azmee tace “Ina fata jiya kin kai ma SGR dinner ɗinsa ko? don na shigo na taras da kayan abinci a warmers ko ta6a su ba ayi ba,’
Sehrish tace “Na babban yaya ne, Jiya bai samu yaci ba dana kai masa, Tea kawai yasha daga baya yace mun yana buƙatar fruits, shine kafin naje na kawo masa har bacci ya ɗauke sa,’
Jinjina kai azmee tayi tare da cewa “Allah sarki da alama jiya sun sha aiki ne that’s why harya gaza cin abinci, Yanzu bari na shirya miki breakfast ɗinsa ki kai masa da sauri saboda nasan dole ya tashi da yunwa,’
Sehrish ta amsa mata da Toh, ta tsaya tana jiran ta shirya mata kayan breakfast ɗin nasa,
Shiru tayi tana tunano maganar da HAROON ya faɗa mata jiya, akwai abunda ya tsaya mata arai take son fitar dashi
“Aunty azmee dan Allah me ake nufi da ZAREN BA KALAR YADIN bane? ta tambaya tana kallom azmee dake shirya abinci cikin warmers asaman kitchen drawers din dake jere,
Ba tare da ta juyo ta kalle ta ba tace “idan aka ce Zaren ba kalar yadin bane, a tunani na ana nufin kamar abunda bai dace da wani ba, a misali kamar ace kina son wani wanda yafi ƙarfin ki nesa ba kusa ba, bari na baki wani misali ma kamar yanzu ace mace tana Son Namiji wanda ya kasance hamshaƙin mai kuɗi ne ko mai mulki ga ilmi ga kyau gashi prominent dae, ke kuma ace kin kasance ƴar talakawa ce koma kina aiki a ƙasan shi baki da duk wani abu daya mallaka da zaku zo ɗaya dashi kin ga kuwa ba sa’an yin ki bane,wannan shi ake nufi da Zaren ba kalar yadin bane……’
Jinjina kai sehrish tayi aranta tana cewa “Wato abunda haroon yake nufi kenan hmmm,”
Sannan a fili tace “To Aunty azmee me ake nufi da cewa ISKA NA WAHALAR DA MAI KAYAN KARA,!”?
Har sai da azmee ta ɗanyi dariya jin wannan, ɗan gyaran murya tayi kafin tace “Kamar mutun ya yi ta wahalar da kansa akan abunda bazai ta6a samu ba, yanzu in mutun ya sanya kayan kara ana iska shin kayan zasu zauna ne batare da sun tarwatse ba?
Sehrish tace “Eh hakane kuwa,”
“Yawwa ma’anar kenan, mutun yasanya wa ransa abunda bazai ta6a samu ba, kin ga zai tashan wahala ne,”
ta ƙarasa maganar tare da cewa “Zo ki ɗauki breakfast ɗin ki kai masa na kammala,”
ƙarasawa sehrish tayi ta ɗauki tray ɗin duk jikinta yayi sanyi ga me da abunda Azmee ta fassara mata yanzu, amma taci alwashin duk runtsi duk wuya zata jaraba Soyayyarta Agare shi ba fashi ????

Fuce wa tayi ta miƙi hanya kamar daga sama taji muryar haroon a kunnanta yana cewa "ƴar Shila barka da safiya fatan kin kwana cikin ƙoshin lpy, 

Shiru tayi bata bashi amsa ba, yana tsaye ruƙe da ƙugu daga shi sai gajeran wando ajikinsa,
Ci gaba da magana yayi “Dole kisha ƙamshi baby, an fa samu Freedom dole a hura hanci, hallau dae bari na ƙara tunasar miki, shisshigi da kutsi ba zai kai ki ga cin nasara ba akan wancan Babban kayan da ki ke hari, ke bama shi ba ko junaid dana ga kina shisshige mawa wlh yafi ƙarfin ajin ki, kwara ma ni zan iya yin maneji na lalla6a ki mu rufa wa juna asiri, ke ƴar aiki ni kuma ɗan masu gida Fantsararre,,,
takaici ya hana ta cewa komai wuce wa kawai tayi upstairs,
Tun da ta nufi part ɗinsa take jin tashin ƙamshi ya gauraye ko’ina Har cikin hancin ta direct masu daɗin ƙamshi,

Bayan tayi sallama tashi ga, babu kowa a palor ɗinsa ƙarasawa tayi ta ajiye masa tray ɗin asaman table ɗinsa, tsayawa ta ɗanyi don ta jira fitowarsa,

Tana cikin tsayuwar nan wayarsa da ya bari asaman hannun Sofa ta soma ringing da ƙarfi har sai da sehrish ta ɗan yi firgit da ido, kai idonta tayi a inda wayar take hada sa hannu tana dafe kirjinta, matsawa tayi a ƙoƙarinta na ta ɗauki wayar takai masa,
Adai-dai time ɗin yafito cikin sauri Don ya ɗauki wayar saboda Kira ne mai mahimmanci agare Sa yasan dashi
Jin motsin mutun yasa sehrish ɗagowa takai ido a kansa, aikuwa a tsananin firgice ta ɗanyi wani sauti tare da yin Hanzarin juyawa cikin tsananin farga ba,
Sam baisan da mutun ba, fitowa yayi daga shi sai ɗan pant a jikinsa gaba ɗaya halittar jikinsa ta bayyana,
bin bayan ta yayi da kallo mamakin sa ganin yarda ta razana kamar taga wani dodo, wuce wa yayi yasa hannu ya ɗauki wayarsa sannan ya shige ciki yana amsa kiran a kunnansa,
Juyo wa sehrish Tayi jin alamar ya koma ciki sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, gaba ɗaya duk ta firgice ta gigice ta tsorata da yanayin da tagansa,????????????ABBAN SOJOJI????????????

????The Father Of Soldiers????

Story & Written
By
BOSS BATURE

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·Episode 13-14•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·

LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ® ✍️
───────────────────────
{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.

Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.} ✏️✏️✏️
_(✪)___

Tsawa tayi tana faman sauke ajiyar zuciya, after some minutes sai gashi ya fito jikinsa sanye da jeans da t-shirt, hannunsa ruƙe da wayarsa ya samu wuri ya zauna saman Sofa, cikin sauri sehrish ta gaishe shi “Barka da safiya, fatan ka tashi lafiya,” a tunaninta bazai amsa ba amma sai ji tayi yace “Alhamdulillah Am well,” murmushi ta ɗan saki, kafin ta shiga haɗa masa Tea a cup mai ɗan xafi ta tura masa agabansa, hannu yasa ya ɗauka yakai bakinsa yana kur6arsa a hankali, ci gaba da saving ɗinsa sehrish tayi, kamar daga sama taji yace “Meyasa jiya ba’a kawo min fruits dana buƙata ba”!?
Murya na rawa sehrish tace “na same ka kana bacci ne lokacin dana kawo maka,” ta ƙarasa maganar tana kallon fine face ɗinsa,
Bayan wasu mintina ya kuma cewa “daga yanzu inaso a rinƙa kawo min Coffee or Tea wit fruits around 12 pm,”
Cikin hanzari ta amsa mashi da cewa “Insha Allah,” jinjina kansa ya ɗanyi yayin da yake ci gaba da cin pancakes ɗin data haɗa masa da Zuma,
tsayawa sehrish tayi tana jiran ya kammala ta zuba mashi wani abun,
Wayarsa dake ajiye a gefensa ta soma ringing cikin sauri takai hannu zata cirar mashi tissue ya goge hannunsa adai-dai lokacin shima ya miƙa hannunsa zai cira karaf suka haɗa hannunsu cikin na juna ???? zaro ido sehrish tayi cikin tsananin jin tsoro tana ɗan kallonsa,
Shi kuwa bin hannun Yarinyar yayi da kallo sam ba’a yi masa irin haka amma yayi mata Uziri ne saboda da alama batasan ko shi wanene ba, gata kuma ƙaramar yarinya,
“Am sorry,…’ sehrish ta furta aɗan tsora ce yayin da ta janye hannunta, shi kuma ya ciri tissue ɗin a natse yace “Don’t repeat that mistake again,”
Cikin sauri tace “Insha Allah,” goge hannunsa yayi sannan ya ɗauki wayar ya ɗaga kiran tare da karawa a kunnansa, taso taji mai zai ce acikin wayar amma sai dai kash cikin wannan harshen taji yana magana wato Espanol da alama yafi jin yaren sosai ko kuma shi ya taso yana ji,
Zuba mashi ido tayi tana kallon shi tun daga shafaffen cikinsa har zuwa saman wide Chest ɗinsa haɗaɗɗiyar ƙira, maganar haroon ta tuna dayake cewa Zaren ba Kalar yadin bane Iska ce kawai zata wahalar da mai Kayan kara, tabbas kuwa yayi gaskiya amma in ta tuna wannan karin maganar da ake Cewa DUK KYAN TAKALMI ƘAFA CE ZATA TAKA SHI sai taji wata irin natsuwa tazo mata, tana tunani tana ci gaba da kallon fuskarsa yadda yake Moving pink lips ɗinsa yana magana tamkar baison yi, da kuma yarda yake faman lumshe sexy blue eyes ɗinsa ba ƙaramin Yanayi yake jefa ta ba,
“Allah yasa bada budurwarsa yake waya, koda yake aunty azmee tace baya soyayya, To Allah yasa dai bada mace yake waya ba,” ta faɗi acikin zuciyarta saboda ganin yarda yake ta faman lumshe idonsa kamar wanda ke waya da mace cikin shauƙi,
tana cikin yi mashi wannan kallon ƙurullan nata ya kamata, adai dai time ɗin ya ɗan ware idonsa direct suka sauka kan na sehrish dake faman Zuba masa ido tana kallonsa abunda ya tsana arayuwarsa ba, sam bata lura daya kamata ba saboda idonta na akan Sumar kansa, har sai da ya ɗanyi gyaran Murya cikin sauri ta wurga kwayar idonta kan tashi aikuwa har sai da ta ɗan Razana ganin ya aza idonsa acikin nata Unexcepted,
ƴar harara ya wurga mata sannan yace “Stop looking at me, i don’t like,’ ya faɗi tare da cigaba da yin wayarsa,
Sunnar da kai sehrish tayi cikin jin kunyar Kamatan da yayi tana masa kallon kurulla, amma wannan hararar daya sakar mata ba ƙaramin kashe mata zuciya yayi ba, ya jima yana wayar kafin ya kammala ya ture ta gefensa, sehrish ta cigaba da saving ɗinshi harya kammala cin breakfast ɗin nasa sannan ta tattare komai ta fuce dasu kitchen ta ajiye agefen Kitchen sink yadda in tadawo wankewa kawai zatayi,
Daker ta iya fitowa daga kitchen ɗin saboda taga duk sun Hallara suna yin breakfast, tunkarar su tayi gabanta na faɗuwa saboda ganin hada HAROON zaune ga kuma Twins duk suna zazzaune, tunkan ta isa junaid na ganinta yasoma sakin murmushi kamar gonar Auduga, sallama tayi masu suka amsa sannan ta kalli Abbansu wanda keta faman sakar mata murmushi tace “Ina kwana Abba, fatan kun tashi lafiya,” Abban nasu yace “Alhamdulillah My Only daughter, yanzu nake tambayar azmee take cemun kin shiga kaiwa Babban yayanku Abinci,”
“Eh hakane,” ta bashi amsa sannan ta juya ta kalli sauran ta gaishe dasu duk suka yi tsit sai kanal Yusif daya ce “Ae nayi tunanin bazaki gaishe da yayyen naki ba, yanzun nan nayi fushi dake,”
Murmushi sehrish tasaki tana mai mamankin hali irin na kanal Yusuf sam bakamar na sauran ba,
“Samu wuri ki zauna mana,” Abbansu ya umarce ta kujera taja ta zauna zuciyarta na ɗar ɗar, tana a jerin inda Abbansu yake gefensa junaid daga shi sai ita, a ɗayan side ɗinta kuwa haroon ne tabbas tasan dole ya hantare ta, ga kuma AYAAN Da JAHAN da take facing ɗinsu duk ta tsargu saboda tasan halinsu suna jere tare da kanal yusif,
azmee da kanta tayi saving ɗinta acikin plate ta buɗe saving dish ta zuba mata Chicken pper soup
Sannan ta haɗa mata da Cofee acikin Cup☕ Sehrish ta kalli azmee tare da cewa “nagode aunty amzee”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23Next page

Leave a Reply

Back to top button