ABBAN SOJOJI BOOK 2 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 2 COMPLETE


Tuni sun kammala aikin su na dinner, har sun kammala jerawa a dining Kowa ya bama cikinsa an ware, yanzu gidan ya ragu ba laifi kasancewar tun week ɗin daya wuce aka tura mutun Huɗu Aiki, Irfan jabeer, khaleed da Fawan duk basa nan, yanzu wanda suka ragu Acikin gidan Haroon, twins, junaid, Sai Marshal Omar da Sgr duk da basu cika zama cikin gidan ba suma, always working saboda suna bada gudummuwa sosai shiyasa koda yaushe suna headquater ɗinsu don ana buƙatarsu sosai game da insecurity ɗin qasar tamu, kasancewarsu kwararrune a6angaren aikin soja dama sun kasance international Armies, kowace ƙasa aduniya suna bada gudummuwarsu wurin kame tantirai sune maganin ƴan Iska, shiyasa sunansu ya shahara a faɗin duniya duk inda suka je, ansansu girmamasu ake gani kamar kamar me (Tiger da Lion) Kenan ba wasa ????????????

SEHRISH
Shiga bedroom ɗinta tayi Wurin isha prayer, duk ta rame kamar ba Reeshi ba, alwala ta ɗaure a toilet, ta shimfiɗa sallaya, ta gabatar da salla, bayan ta kammala ta naɗe hijab da sallayar ta tura a wardrobe ɗinta, komai nata a slow take yinshi saboda rashin kwarin jikinta da fargabar da take fama dashi na Haroon,

Haye wa tayi saman gadonta tare da janyo pillow ta rungume tunani kala kala a ranta, hawaye ne suka soma gangarowa daga idonta sbd tuna yadda haroon ke ta6a jikinta, hannu tasa tana share su, daga bisa ni tayi lamo tana tunanin duniya,
Tana cikin wannan halin taji an kwankwasa ƙofa, shiru tayi bata Yi magana ba cike da tsoron waye ke mata knocking, ji tayi an sake buga ƙopar muryar na rawa tace “wanene”?
Muryar junaid taji yana cewa “Sehrish ni ne,”
Ajiyar zuciya tasaki jiki na rawa ta sauko tare da karasawa wurin kopar ta buɗe,
Gabanta ne yayi mugun faɗuwa ganin haroon hankali tashe tace “Kaineeee !!!!” a tsorace tayi maganar jikinta na rawa,.
Fashewe da dariya haroon yayi tare da wuce ta yashi ga ciki yana cewa “ƴar shila ni ne, ae nasan bazaki buɗe ba shiyasa nayi maki muryar junaid don na lura kuna good time dashi,’
juyowa tayi tana bin shi da kallo a razane,.
“Me ya kawo ka”!?
“Abunda yasa ba kawo ni, Yau nazo ne ayi ta taƙare, Haƙƙina nake son ki bani,”
Cikin shessheƙar kuka sehrish tace “Me kake nufi wai !!! Wani haƙƙi ka ke dashi akaina? Dan Allah kabarni nayi rayuwata cikin salama !! Ka rabu dani mana !!
ta6e baki haroon yayi tare da cewa “Na amince zan rabu dake, amma bisa sharaɗi ɗaya”? Ya faɗi yana kallonta fuska a ɗaure, a lokacin tadawo tsaye front of side drawer ɗinta tana facing ɗinshi,
Gabanta na faɗuwa tace “Menene shi”? Cikin sanyin murya tayi maganar
Haroon yace “Your Virgin!! shine abunda nake so,and if u do so i wll be out of ur life”
Fashewa da kuka sehrish tayi cikin tsananin jin ƙunci da raɗaɗi aranta, tuni zufa tagama wanko mata kamar wadda aka tsamo daga cikin ruwa, tsanar haroon take ji kamar kamar me, tarasa amsar da zata bashi sai faman kerma take,
A tsawace haroon yace “Ke !!! Ki amsa mun kin amince ko baki amince ba”!?
A Firgice tace “Na’amince” ita kanta batasan ta bashi amsar ba saboda tsoratar da tayi da tsawarsa,
Wani irin shu’umin murmushi haroon yasaki, bin shi da kallo tayi ganin yasa hannu yana zare belt ɗin wandonsa, tuni ta runtse ido ganin gashin jikin shi, bakomai ya faɗo mata arai ba fa ce Sgr shine namijin da take so tafara kasancewa dashi arayuwarta bata buƙatar wani namiji in ba shi ba, shi take so ta mallakawa komai nata muddin ta mallake sa,
Jiki na rawa ta zura hannunta ta baya, taci sa’ar damƙar fititalar Kwan dake gefen gadonta, kafin haroon ya ɗago ta daddage da iya ƙarfin ta na ƙarshe ta ɗago da fitilar dake hannunta ta kwaɗa masa a tsakiyar kai !!!!! Ji kake KWASSS !!! A razane haroon ya ɗago jin saukar fitilar kafin yayi wani yunƙuri tuni Sehrish tabi ta gefensa ta watsa da gudu sai cikin toilet ta datse ƙopa sosai, ta sulale daga jikin ƙopan zuƙunne tana kuka don tasan dole haroon ya ɗauki matakin abunda tayi masa,
Ba ƙaramin buguwa haroon yayi ba, don wurin harya fashe Ae kuwa rai a tsananin 6ace yace “Ke don ubanki ni kika fasa ma kai”?
Sehrish dake acikin toilet murya cike da kuka tace “Ba dai ubana ba sai don Uban Mai zagi !! Fasiƙi ɗan iska insha Allah bazaka ta6a cin nasara akaina ba, sai Allah ya nuna maka iyakarka, wulaƙantacce kawai ƙazami mai warin baki,”
Tuni idon haroon sunyi jawur kamar garwashin wuta, ransa yayi mugun 6aci bai ta6a tunanin yarinyar zata iya mayar masa da martani ba, amma sai gashi yau ta zage shi tass,
“Bazan ƙyaleki ba, sai na wulaƙanta rayuwarki ba dai kina acikin gidan nan ba kuma zaki fito ba, zamu haɗu ne wlh,” Ya faɗi tare da tunkarar hanyar fita yana mayar da belt ɗin wandonsa daya fara cirewa,.(ba’aci nasara????)
Sehrish batayi shiru da bakin ta ba taci gaba da cewa ” Ta Allah bata ka ba wlh !! Mugu azzalumi mummuna kawai, da wasu idanuwan ka kamar na Mujiya ni ina kokwanton Cewa anya kai Jinin Abban sojoji ne !! Sbd duk ƴa’ƴansa ba Fasiƙi irinka,”
Jinjina kai haroon yayi kawai yana huci, ya tura ƙopar ɗakin ya fuce,

Wani sabon kukan ta sake fashewa dashi, tana faɗin “wayyo Allah na nasan haroon baxai ƙyale ni ba, nashiga uku……..’
Jiki na rawa ta miƙe ta nufi wurin bathroom cabinet ɗinta, akwai wasu Chemicals dake ajiye cikin toilet ɗin masu illah ga jikin mutun tamkar poison suke, ta riga ta yankewa kanta shawarar kwara ta kashe kanta ta huta da fitinar haroon,
Hannunta har kerma yake yi, wata ƙaramar roba ta ɗauko mai ɗauke da chemical ɗin, buɗe murfin tayi yayin da idonta ke zubar da hayawe, bakowa ya faɗo mata arai ba face Hosana Jahad, junaid, Aunty azmee uwa uba Burin ranta, yanzu shikenan duk zata rasa su? Zata mutu tabarsu?
Runtse idonta tayi aranta tana faɗin “bani da wata manufa face wannan, kuyi haƙuri ku yafe mun bazan Iya cigaba da rayuwa a wannan duniyar ba mai cike da tashin hankali, ban ta6a cutar da kowa ba, amma gashi wani nason cutar da rayuwata …………………”
Cikin sauri ta shiga zazzaga hodar abakinta

A dai dai lokacin Motocin Sgr da marshal Omar suka shigo cikin gidan atare jiniyarsu ta karaɗe ko’ina har cikin kunnan Sehrish
Zuciyarta ce taji tayi wani irin bugu, nan take kuma zuciyarta tace “Yanzu kin amince ki mutu baki cika burinki ba!? ke fa musulma ce ! Kin kuma son hukuncin wanda ya kashe kansa da gangan!!
Runtse idonta tayi hawaye na zuba, fuskar sgr kawai take tunawa da fuskar su hosana da jahad,
“Ina son sake sashi a idona,” ta furta da wani irin sound, nan take tayi wurgi da robar chemical ɗin dake hannunta, cikin hanzari ta shiga amayar da wanda ke bakinta agaban basin, fanfo ta kunna tashiga kuskure bakinta da hanzari ta kora aman, sannan ta wanke face ɗinta ta fito,
tana tafiya zuciyarta na ƙara bata ƙwarin guiwa da cewa “Saboda wani shashasha zaki halaka kan ki, share hawayenki sehrish kina da damar rayuwa, wani banza bai isa ya tarwatsa miki burinki ba,”
Gyara jikinta ta shiga yi saboda tana son zuwa kai mishi dinner ɗinshi shi da Omar don ta son da yunwa suka dawo, duk da tana tsoran kada suci karo da haroon a fitarta,
dama riga da wando ne ajikinta, gashin bakinta kawai ta manna, ta gyara hular kanta da mayafin da take naɗe hular dashi, bayan ta kammala ta buɗe kopan cikin fargabar ta fuce,.
Ko’ina haske fauuu gidan cikin sanɗa ta wuce kitchen taji sanyi aranta ganin babu kowa,
Cikin hanzari ta shirya ma Omar nasa a tray, a palor ɗinsa takai masa babu kowa aciki alamar yana cikin bedroom ɗinsa, ajiye masa kawai tayi ta fuce, izuwa kitchen ta sake shirya wani a tray sannan ta wuce upstairs part ɗin BABBAN YAYA

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23Next page

Leave a Reply

Back to top button