ABBAN SOJOJI BOOK 2 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 2 COMPLETE

ta shi ga fiddo su tana duba su, kafin tasanya hannu cikin basket ɗin da tazo dashi ta ɗauko robar ruwa, ta buɗe ta bayan ta ciro maganin ta miƙa ma hosana tare da ruwan tana kar6a tana sha, haƙiƙi su Hosana da jahad ba ƙaramin kwanciyar hankali suka samu ba, saboda sun ga tausayinsu ƙarara a fuskar Hafsat kuma da alamun zasu samu sauƙi ta 6angarenta,
Shin Ya maganar matar da ta ba Hafsat miliyan shidda don ta zubar mata dasu Jahad? Kuna ganin zata fasa wannan aikin ko kuwa? ????

AUNTY BABBA ????

Sam ta gaza samun natsuwa hankalin ta ba ƙaramin tashi yayi ba ganin yarda hafsat ta fara damuwa da twins ɗin da OMAR ya kawo, tabbas dole ta ɗauki mataki akan hakan, kuma haryanzu tana akan bakanta na sai tasa an zubar mata dasu Hosana da Jahad,
Tabbas dole na ɗauki mataki akan hakan
tayi maganar tare da dakatawa daga zirga zirgar da takeyi acikin ɗakin nata, fitowarta kenan daga wanka, ta zumbula doguwar rigar Buba ta Material, hannu takai ta ɗauki wayarta dake ajiye saman stool dake agaban mirror,
cikin hanzari ta shiga contact ta dannawa wata number kira wadda tayi saving ɗinta da BABA ALAMU
Nan da nan kiran yashiga wayar ta soma ringing zuwa wani lokaci mai numbar data kira ya amsa wayar,
Cikin sauri tace “Assalamu Alaikum,”
daga can 6angare wata murya kakkausa ta gawurtattun ƴan iska ta amsa mata da cewa,”Hajiya Laila manyan gari, ashe kuna neman mutane? Ae nayi tunanin daga in da amfanin mutun ya ƙare a wurinki yazama shara……’
dakatar dashi Aunty Babba tayi da cewa “Baba Alamu ! mu aje wannan gefe, wlh ina cikin tsananin damuwa ne, tunawa dakai yasanya na kira ka domin nasan kai kaɗai ne zaka iya yi mun wannan aikin…..’ ta ɗan dakata tana jiran amsar da zai bata ,
Baba Alamu yace “Ae dama ke ba’ki ta6a neman mutun sai in buƙatarki ta taso, tun da ansan muna da amfani ae a rinƙa ɗan kiran mu ana bamu hasafi don tafiya tayi kyau ko?, yanzu dai faɗa mun me kike so in aiwatar kawai ! Wa kike so akashe miki har lahira? Ko wa kike so In Naƙasa Miki kasusuwansa ajefar bayan Duniya?????

Dariya aunty babba tayi cikin jin daɗi tace “Yawwa Mutumina, dama nasan kaine kawai zaka iya share mun hawaye na, abunda ke faruwa wani ƙanin Mijina ne wlh ya tsinto wasu ƴan mata tagwaye ya kawomin a gida na, na tsani yaran nan ko ganin su bana son yi, saboda zasu tarwatsamun target ɗina abunda nakeso kawai so nake kazo ka ɗauke su Ka fitar mun dasu daga gidan nan ka kai su can bayan gari ka jefar mun dasu Can cikin ƙurmin daji wanda zasu rikice su gaza gane hanyar da zasu fita daga cikin shi,”????
tamkar tana agabansa haka take masa bayani tana faman cizon la66a, ????
fashe wa da dariya baba Alamu yayi daga bisani ya tsagaita yace “Ƙaramin aiki kenan, ni nama yi tunanin wani za’a kashe maki ne yanzun nan mu kai shege lahira, amma tun da wannan ne kada ki samu damuwa, yanzun dai bana nan kinsan naje lagos ƙarƙashin gada amma maƙo mai zuwa bi iznil lahi, aikin ki zai kammalu, ƴan Canji kawai zaki tanada “
Aunty Babba tace “in dai wannan ne an gama, zanyi maka biya na musamman babban kaso mai tsoka,
Baba Alamu yace “Shikenan sai kin jini, da zarar na dira kaduna zan zo da rugwagwar mota ta na kwashe Maki Sharar azubar abayan gari,’????

Jinjina kai aunty babba tayi har wani sauke ajiyar zuciya take yi jin burinta zai cika na kawar da su Jahad,
Sun jima suna waya da baba Alamu kafin daga bisa sukayi sallama, ta ajiye wayar saman mirror tana cewa “Yanzu abunda ya rage mun shine, na dakatar da Omar don nasan zai iya zuwa yace zai tafi dasu na lura da hakan I ave to do something ❗‼ ………!????wani irin shu’umin murmushi tasa ki, saboda plan ɗin da ta tsara,


Sai wuraren bayan Sallar La’asar sannan dr yayi discharge ɗinsu daga asibitin kamar yadda hafsat ta buƙata don bata son zaman su a asibitin gudun kada Omar yayi musu Dirar Mikiya, duk da dr yaso ya ƙara ma hosana Jini amma ta hana hakan sai dai tayi alƙawarin cewa zata mai do ta asibitin Next time,
A hankali take driving ɗinsu acikin motar, hosana na’a a back seat kwance sai faman sharar bacci take yi, yayin da jahad ke agefen hafsat dake driving, adai-dai wani Store ta tsaya da motar, sannan ta kalli jahad tace “Ki kula yanzu zan dawo,”
Jahad ta amsa da cewa “Toh Aunty”
Shiga cikin wurin tayi bayan wasu mintuna tafito hannunta ruƙe da leda, ta buɗe motar ta shiga miƙa ma jahad ledar tayi tace “Ruƙe wannan a wurin ki,”
Amsa jahad tayi ta ƙanƙame ledar a hannunta, sannan hafsat taja motar suka tafi gida kai tsaye,
Bayan tayi parking suka fito daga motar daker jahad tasamu hosana tafarka ta ruƙe hannunta suka nufi ciki hafsat na biye dasu, sai faman jin fargabar haɗuwa da Aunty babba suke yi,
Aikuwa suna shiga suka same ta zaune a babban falon saman sofa tana faman danna wayarta,
tana ganinsu ta miƙe tsaye tare da cewa “Sannun ku da dawowa, Allah sarki hosana da jahad kuyi haƙuri ban samu damar zuwa asibiti ba na dubo ku, Ya jikin naku”? ta faɗi cikin nuna tausayin su,
ai ba su jahad da hosana ba hatta hafsat tayi mamakin jin abunda Momyn nata tace lokaci guda ta canza tamkar ba ita ba, tsayawa sukayi suna kallonta baki asake,
Ganin hakan yasa aunty babba ƙarasawa ta ruƙo hannun kowannan su , sannan cikin sanyin murya ta wanda yayi nadama tace “Haƙiƙa nasan na cutar daku sosai, Allah ma ba zai yafe mun ba, tabbas jiki na yayi sanyi, nayi danasanin abun da na aikata muku dan Allah kuyi haƙuri ku yafe mun……..’
Hawaye ne suka soma saukowa daga idon aunty babba fuskarta duk a yamutse tana kallonsu,
cikin mamaki hafsat tace “Shin mafarki nake ko gaske!? Mom are u serious about what are u sanying? Ko dai kin sha wani abu ne bayan na fita? kece dakan ki kike danasani hada neman gafara a wurinsa?
ɗago ido aunty babba tayi tare da kallon hafsat tace “Shin ni ba mutun bace kamar kowa daba zanyi laifi na nemi gafara ba”? na zauna nayi wani tunani menene riba ta idan na cuci waɗannan bayin Allan? Allah fa dakansa ya haramta ma kansa zalunci kuma ya haramta shi atsakanin mu, kuma yace kada muyi zalunci, amma ni na kansance mai son zuciya……….’
Sam ta kasa ƙarasa maganar saboda shessheƙar kukan da tafara, juyawa hafsat tayi ta kalli jahad yayin da ita kuma jahad idonta na akan Hosana wadda ke kallonta, gaba ɗayansu mamaki ne ke ɗawainiya dasu, shin taya zasu gasgata tuban da Mommyn hafsat tayi? Anya ba wata ƙullalliya bace?
“Naji kunyi shiru baza ku yafe mun bane? In har baku yafe mun ba bana ji zan iya bacci adaren nan,”
Cikin sauri Jahad da hosana suka haɗa baki wurin cewa “Aunty mun yafe miki, Allah ya yafe mana gaba ɗaya,”
Murmushi Aunty babba ta saki tare da sa hannu ta haɗa su duka ta rungumesu ajikinta, tana faman ci gaba da basu haƙuri akan kuskuren da tayi masu na jibgarsu da tayi,
Jikinsu duk yayi mugun sanyi, gaba ɗaya kwalwarsu ta rikice sun rasa gane dawa zasu YARDA? SHIN HAFSAT ko MOMMYNSU? Taya hakan zaiyiyu ace lokaci guda sun canza musu izuwa mutanen kirki masu tausayin su?
Bayan aunty babba ta janye su daga jikinta ta mayar da idonta kan na hafsat tace “daughter daga yau inaso ki ɗauke su tamkar ƙannen ki, ni kuma insha Allah zan ɗauke su tamkar nice na haife su, zan basu duk wata kula daya dace uwa tabawa ya’yanta, “
Murmushi hafsat tasaki tare da cewa “Insha Allah mommy as from now hosana da jahad sun zama ƴan gida, zasuyi rayuwar ƴanci acikin gidan nan, babu wanda zai sake cutar dasu acikin mu,”
Jinjina kai aunty babba tayi sannan tace “ina so daga yanzu su koma ɗakin Ladi mai aikin mu da kwana,”
Hafsat tace “a’a Mommy, mattress ce kawai acikin ɗakin, gaskiya ni nafison su dawo bedroom ɗina da kwana yadda zanfi basu kulawa,”
Aunty babba tace “hakan ma yayi, yanzu yakamata ku shiga ciki ku huta, sannan hafsat ki taimaka ma hosana tayi wanka da ruwa mai ɗumi ko taji daɗin jikinta,
Hafsat tace “insha Allah mommy,” sannan ta mayar da idonta kansu hosana tace “mu shiga ciki,” hannun su cikin na juna suka bi bayan hafsat har izuwa cikin bedroom ɗinta,
Da taimakon hafsat hosana tayi wanka ta canza kayan jikinta izuwa doguwar riga mara nauyi, bayan ta kammala hayewa kawai tayi saman gadon hafsat, tana jiran zuwan jahad wadda ta shiga toilet yin wanka itama, Ajiyar zuciya kawai hosana ke saki amma tana jin fargabar canjin da su ka gani wurin hafsat da Mommynta, sam bata amince dasu ba, kuma taci Alwashin muddin YA OMAR yazo ƙafarta ƙafarshi sai ta bishi, ????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23Next page

Leave a Reply

Back to top button