ABBAN SOJOJI BOOK 2 COMPLETE

Haryanzu jikinta kerma yake, kuma bata fasa maganar shan poison ɗin nan ba, burinta ta sanya Sgr a idonta 4 the last time before tabar duniyar, Baiwar Allah
Babu kowa a palor ɗinsa tsit kake ji sai ƙamshin dake tashi, shiga ciki tayi ta ajiye masa a saman table ɗinsa,
Tsayawa tayi tana faman sauke ajiyar zuciya yayin da idonta ke cike taf da hawaye, kamar daga sama taji muryarsa ta cikin bedroom ɗinsa yana faɗin “who’s There”?
Runtse idonta tayi saboda jin sanyayyiyar muryarsa, daker ta dai daita natsuwarta tace “Tukur ne mai aiki,”
Voice ɗinsa tasake ji yace “Come In! i wanna see YOU Right now,” zaro ido sehrish tayi jin abunda yace wato ta shigo ciki yana som ganinta ????????????????????
Dake ta dai dai ta natsuwarta, ta tafi izuwa cikin bedroom ɗinsa kamar yarda ya umarta ta shiga da sallama”Assalamu alaikum”
“Wa’alaikum salam” ya amsa mata,
tsaye yake agaban mirror jikinsa sanye da sleeping dress riga da wando Milk colour masu ɗigon² baƙi ajikinsu ba ƙaramin kyau su kayi mishi ba, turarurruka yake ta fesa ma jikinsa,
Sam tagaza janye idonta akan shi daker ta iya cewa “barka da dare” ya amsa mata da “Yawwa” sannan ta ƙara da cewa “Gani”
Hannu yakai ya ɗauki kalbar turaren SHUMUKH ya feshe shi sannan ya mayar ya ɗauki wani turaren na Jar yana fesawa, mutun ne mai tsananin son ƙamshi shiyasa baya gajiya da bin jikinsa da turare,
Shiru sehrish tayi zuciyarta na ɗar ɗar, kusan 15 minsa sannan Boss Man ɗin yace “Ni zan zo ne”? Ya tambaya yana jiran amsa,
Cikin sauri sehrish ta ƙarasa hankali atashe ta tsaya daga bayansa jikinta na rawa,
Cikin natsuwa yaso ma magana” Wacece ke”?
Waro ido waje sehrish tayi jin abunda yace murya na rawa tace “Ni…..mai…..aiki…ne ….” a wani irin slow sgr ya juyo kai tsaye ya tunkare ta gadan gadan, a tsorace sehrish ke ja da baya tana kallonsa tuni zufa ta gama wanko mata sharkaf a jikinta,
Sam idonsa basa a kanta ƙasa suke, har sai da suka ƙurewa bangon gaba ɗaya, yarfa hannu sehrish ta shiga yi a tsananin tsorace take karanto addu’o’in da duk suka zo mata abakinta, kuma abayyane take yi saboda tsaban ruɗi tuni ƴan hanjin cikinta sun motsa, gaba ɗaya jikinta rawa yake yi kamar wadda sanyi yakama,
Hannunsa yasa ya daki wall ɗin data ke manne ajikinsa ya aza hannun anan jikin bangon ya dafe sannan yace “ƙarya ke bana so arayuwata, am gonna ask u some questions idan aka min ƙarya za’a fuskanci matsala,”
Ya faɗi yayin da idonsa ke a lumshe tamkar a datse suke ba don komai ba sai don gudun kada mai aikin ya Sume a ƙaro na biyu saboda launin ƙwayar idonsa dake razanar da shi, .
Kallon shi kawai take yi zuciyarta na bugawa da ƙarfi, daker take haɗiye yawu ga wani fitsari daya matse ta tunda taji ya ambace ta da mace tasan cewa ya gano ta kenan,
“maca ce ko Namiji”? ya tambaya yana jiran amsa,
Shiru tayi tana tunanin amsar da zata bashi, muddin tamasa ƙarya wannan ba ƙaramin shaqa zata sha ba,
Wannan shirun da tayi masa shiya fusata shi, buɗe Blue eyes ɗinsa yayi duka akanta , ta firgita sosai amma sam ta sanƙare ta gaza motsi da alama suman tsaye tayi
Hannunsa yasa ya damƙi hular kan sehrish yayi wurgi da ita tare da mayafin duka, nan take sumar kanta tasoma warwarowa tana saukowa saman kafaɗarta, kyakkyawan sumar kanta mai matuƙan kyan gaske ga laushi,
mayar da hannunsa yayi saman gashin bakin da take sawa ya cire shi shima, nan take ainihin kyakkwar fuskar reesh ta bayyana a matsayim mace ????????
sam fa bata motsi idonta sun kakkafe sun ƙame, kamar wata saƙago haka tayi,
jinjina kai sgr yayi maganar Adams ta tabbata, yayi mamakin ganin yarinya ƙarama kamar wannan da ƙarfin halin Yin shigar Maza tazo gidan sojoji aiki, ko nawa aka biyata don tayi hakan? Ya tambaya aransa, sam shi baya tunanin ta haura 12years saboda ƙarantarta dayake gani agabansa Ko shouder ɗinsa tsayin sehrish bai kai ba, daga tsaye inda yake yana kallon tsakiyar kanta saboda ba ƙaramin tsayine dashi ba, kowa yazo gabansa kallon ƙarami yake masa,
Janye hannunsa yayi daga jikin wall ɗin da sehrish take sannan yayi tattaki izuwa inda fridge ɗinsa yake, buɗewa yayi ya ɗauko bottle water mai sanyi sannan ya dawo inda take tsaye,
ya buɗe murfin ya yayyafa mata, a wani irin firgice sehrish ta girgiza ta dawo in sense ɗinsa, sai faman zazzare kyawawan idanunta take, bin chest ɗinsa tayi da kallo izuwa face ɗinsa cikin tsoro, hannu tasa ta shafa sumar kanta gabanta ne ya faɗi jin wayam babu yar hularta, hankali tashe ta wurga idonta inda sgr yayi watsi dasu………nan fa tashiga faɗin “innalallahi wa’inna ilaihirraji’un dan Allah kayi haƙuri…..nashiga ukuna……..’ tana kuka tana magana , gaba ɗaya yayi mata rumfa tamkar Zaki haka take ganin sa agabanta ????????????
Idonsa na kumshe yana sauraronta left hands ɗinsa na riƙe da bottle water ɗin, yayin da ɗayan hannun kuma ya mayar dashi jikin bangon ya dafa, sehrish kuma na agabansa suna fuskantar juna,
“haɗiye wannan kukan bana so” cikin hanzari sehrish ta dakatar da kukan tashiga taitayinta, bakomai take kallo ba fa ce damtsen hannunsa, tunani kawai take yarda zai kai mata naushi tabbas tasan sai dai Uwarta ta haifi wata (Hafsat bature ana magana) ????
Cikin natsuwa yasoma magana__________________________________
Abt payment 300 ne, still muna free pages ne wanda suka shirya 08103884440 sumin magana
????
????????????ABBAN SOJOJI????????????
????The Father Of Soldiers????
ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ ﺭﺍﻓﻴﺖ❤????????????????
Story & Written by
Hafsat Bature Muhammad
~????BOSSLADY????~
Sabuwar Marubuciya, mai tafe da sabon salo????
Abban Sojoji part 2
EPISODE 2
????LAFAZI WRITTERS ASSOCIATION????
Cikin natsuwa ya soma magana “tambaya biyu kawai Wacece ke? Kuma waya turo ki”?
Cikin rawar murya sehrish tace “Ni ba kowa bace ba, kuma babu wanda ya turon…….’. Interrupting ɗinta yayi da cewa “ki mun magana a hankali don bana fahimta sosai,”
Gyara muryarta tayi sannan taci gaba da cewa “Sunana Sehrish, kuma ni babu wanda ya turo ni, banzo da nufin na cutar da kowa ba, aiki kawai nake don nasamu kuɗi……..’ buga wall ɗin da yayi yasata dakatawa a tsorace “Nace wa ya turo ki!!?
Hankali atashe tace “Allah shine shaidata, wlh ni babu wanda ya turoni, banzo da nufin na cutar da kowa ba, ƴan uwana ne Basu lafiya an kwantar dasu asibiti ana buƙatar kuɗin aiki shine na nemi aiki gidan wata hajiya……………sehrish bata 6oye masa komai ba ta faɗa masa tass dalilin zuwanta da dalilin yin shigarta na maza batayi masa ƙarya ba ko kaɗan, ta ƙarasa masa labarin tana faman zubda hawaye tsoranta wane hukunci zaiyi mata don tasan watan Cin Ubanta ya tsaya, shiru su kayi na wani lokaci, kafin daga bisa ni Babban yayan yaja da baya ya juya
bedroom ɗinsa ya shige kafin daga bisa ni, ya fito hannunsa ɗauke da wayarsa wuri yasamu ya zauna saman sofa ɗin sannan yaba sehrish damar ta matso kusa, sai da tafara tattara hularta da mayafin da yayi watsi dasu, ta ruƙesu a hannunta sannan jiki asanyaye ta matsa inda yake kamar wadda tayiwa sarki ƙarya, jikinta sai faman kerma yake,
yace “su nan su? da sunan state da sunan hospital da aka kwantar dasu? and the date!?
Murya na rawa tace “Hosana Sayyad, da jahad sayyad an kwantar dasu a Fmc katsina……..”