ABBAN SOJOJI BOOK 2 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 2 COMPLETE

Suna isa asibitin gudu gudu sauri sauri Aunty babba ta ɗauki hosana suka shiga ciki,da hanzari reception nurses suka karbe ta aka shiga da ita ciki, anci sa’a an samu likitan dake a bakin aiki, cikin gaggawa suka shiga duba hosana,
Su kuwa su aunty babba da hafsat suna atsaye sai faman zagaye suke kowa cike da zullumin abunda zai biyo baya in yarinyar ta mutu, jahad kuwa tana abakin ɗakin da aka kwantar da hosana ta kwantar da kanta jikin door ɗin idonta na tsiyayar da hawaye masu ɗumi,????
Gaba ɗayansu babu wanda ya samu bacci adaren nan saboda da tashin hankali,
(Na zubda hawaye saboda halin da su Hosana da jahad suke ciki Ya Allah ka kawo masu ɗauki) ????


Ana cikin kiran sallar asuba Sehrish tafarka a hargitse tana faman dafe saitin zuciyarta dake yi mata wani irin raɗaɗi, sai faman ambaton sunan Allah take yi, tabbas ranta na bata cewa wani mummunan abu ya faru dasu Jahad, cikin hanzari ta sauko daga saman gadon tana faman zagaye ɗakim kafin daga bisani ta shiga cikin toilet ta ɗauro alwala,
Fitowa tayi ta nufi wardrobe ɗinta, hijab ta ɗauko da darduma ta shimfiɗa, ta shiga jera sallah, bayan ta kammala ta zauna tare da ɗaga hannayenta sama tana addu’o’i akan su hosana da jahad da sauran al’ummar musulmai, ta jima tana addu’ar kafin ta koma saman gadon nata ta kwanta tana fuskantar sama abubuwa iri iri na zuwa mata aranta daga bisani bacci ya kwashe ta, bata sake farkawa ba sai ƙarfe 10 na safe,
Firgit ta farka har time ɗin shiga kitchen ya wuce,
Zumbur ta miƙe shaf shaf ta shirya cikin shigarta ta maza da ta saba, saboda zullumi bazai barta ta fita a matsayin mace ba, a hankali ta tura ƙopa ta fuce izuwa kitchen,
Bin ta da kallo azmee tayi wadda ke gyara kitchen don harta kammala breakfast ɗin already tun ɗazu,
Da mamaki tace”Sehrish ya akai naganki kuma da shigar maza?
Shiga ciki tayi tana cewa “Aunty azmee ni tsoro nake ji Allah,”
“Wani irin tsoro kuma,ba wani tsoro abunda nake so dake bayan mun kammala jera abinci, sai ki koma ɗaki ki cire wannan gashin bakin ki sauko da gashin kanki zan kira ki, sai ki fito a matsayin mace”
Shiru tayi tana kallon yatsun hannun ta kafin tace “shikenan Allah yasa komai ya tafi adai dai,

Murmushi azmee tasaki tare da jinjina kai tace”Insha Allah yanzu bari na fara jera miki warmers ɗin kina kaiwa dining,”

Ta amsa mata da “toh”, tana jin ɗar axuciyarta

Cikin ƙanƙanin lokaci suka kammala jerawa, Ayaan da Jahan ne suka fara fitowa sanye cikin kakinsu gwanin kyau, Suka samu wuri suka zauna kusa da Juna, azmee ta soma saving ɗinsu, time ɗin sehrish ta shige bedroom ɗinta don ta kimtsa kamar yadda su kayi da azmee zata fito a matsayin mace,
Bayansu sai kanal yusif ya fito shima sanye da Jallabiya launin ruwan toka, wuri yasamu yazauna yana gaishe da aunty azmee, da fara’a take amsa musu, cikin girmamawa su twins suka gaishe shi shima ya amsa musu daga bisa ni kowa ya mayar da hankali kan breakfast ɗinsa,
Sehrish na cikin ɗaki cike da zullumin yarda za’ae ta fito a matsayin mace, tana a jikin ƙopar ɗakinta tana ruƙe da handle ɗin kopar cike da fargaba,
Gyaran murya azmee tayi ta ɗan ɗaga murya tare da kwaɗawa sehrish kira da sunanta tace “Sehrish ki fito mana,”
Jin sunan da azmee ta ambata yasa su kallonta da mamaki, sake maimaitawa tayi “Sehrish ki fito nace,”
Kallon juna Ayaan da jahan su kayi sannan suka kalle ta atare suka haɗa baki wurin cewa “Wanene Sehrish kuma? Kanal yusif shima cike da mamaki yake kallon azmee jin sai faman kwala kira take yi, zuba ido su kayi don suga wanene wannan sehrish ɗin da Azmee ke faman kira, shin baƙo su kayi ne a gidan nasu ko kuwa?
buɗe ƙopa sehrish tayi gabanta na faɗuwa ta tunkaro hanyar dining area ɗin, jikinta na kerma a tsorace take tafiya,
gaba ɗayansu suka ɗago suna kallon ta tun kafin ta idasa bayyana a area ɗin da suke, bin ƙafafunta su kayi da kallo waɗanda ke sanye da ƴan silifas ɗinta na gado, sai faman kerma yatsun ƙafarta suke yi,
Time ɗin da sehrish ta idasa fitowa a raxane jahan ya miƙe tsaye, ayaan kuwa baisan lokacin da ya saki cokalin dake hannunsa ba ya faɗa cikin plate ɗin dake agabansa, kanal yusif kuwa kallon abun yake kamar a mafarki,
Bin ta suke da kallo cikin mamaki, kamar a mafarki suke kallon lamarin, ƙarasowa tayi ido a zazzare jiki na kerma, riga da wandon nan ne ajikinta , ta cire gashin bakinta, ta kuma zuba da doguwar sumar kanta har gab da waist ɗinta, ta fito asalin macen ta Tsaleliyar budurwa ƴar matashiyya,
A rude jahan yace “Azmee who’s she ? daga ina ta faɗo cikin gidan nan? Da iznin wa!?
Ayaan kuwa cewa yayi “Ku kuke ganin mu bamu muke ganin ku ba ! Wannan Hurool ainin fa? daga aljanna ta gudo?
Kanal yusif sam yagaza magana bayani kawai yake jira daga wurin azmee, ita kanta azmee ta ɗan razana da reaction ɗin da suka bayar, Sehrish kuwa a gefen azmee ta tsaya tana faman zare ido,
“Azmeee Explain !!!!’ jahan ya faɗi azafafe harda dakar table ɗin gabansa da tafin hannunsa,
Murya na rawa azmee tace ” Kuyi haƙuri dan Allah…Am wannan da kuke gani ba kowa bane face Tukur mai aikin ku, nasan zakuyi mamakin hakan……
Dakatawa tayi ganin yarda Ayaan da kanal yusif suka miƙe atare, cike da ruɗu Kanal yusif yace “What ! Wai wane tukur ɗin ake magana ! Ba dai wannan yaron mai aikin namu ba, kina nufin dama mace ce ba namiji ba ….? Ya tambaya hankali atashe ,
Daga sehrish har azmee sun tsorata,
Hannu jahan yasa yasake bugun table ɗin abincinsu yace “Impossible bazai ta6a yiyuwa ba ! muddin kuwa hakan ta kasance dole yarinyar nan ta fuskanci hukunci mai tsanani kuma tabar gidan nan ayau ɗin nan,
Fashewa da kuka sehrish tayi saboda tsorata da maganar Jahan gashi idonsa na akanta ya zare su,
“Dan Allah ku kwantar da hankalin ku, laifi ne nasan ta aikata amma kuyi mata afwa, sam bata da niyar cutar da kowa…..’ dakatar da ita Ayaan yayi da cewa “Ba wannan zancen ! Saboda ƙarfin hali irin na Yarinyar nan, tayo shigar maxa ta saje acikin mu tana mana aiki, babu sirrin mu da bata sani ba, babu irin firar da bama yi agabanta, har yawo muke yi da towel a ƙugunmu, muyi yawo da gajerun wanduna duk idonta na akai, kaf ta haddace ashe kallon mu kawai take yi,”
bil’haƙki ayaan yake kora bani, gaba ɗayansu ba komai suke ji mawa ba face yadda sehrish ta saje A cikinsu matsayin namiji na tsawon lokaci tana masu aiki, duk a tsammaninsu namiji ne ashe maca ce, tagama sanin sirrinsu saboda babu irin firar da basa yi agaban ta, sannan babu irin shigar da basa yi suna yawo duk a idonta,
Hannu Jahan yasa yana ƙoƙarin zare belt ɗin wandonsa da nufin ya jibgi sehrish saboda yafi kowa fusata, gashi dama su Mace bata agabansu balle suga kyanta ko wani abu haka don su tausaya mata,
A tsorace sehrish ta ƙanƙame kanta ta 6oye abayan aunty azmee tana faɗin “Nashiga uku ! Dan Allah aunty azmee ki basu haƙuri, kada su buge ni…zan tafi nabar musu gidan,
ture kujerar gabansa yayi gadan gadan ya tunkari sehrish zai jibge ta,
Kamar daga sama suka ji Muryar Abban su yace “Kada ka kuskura ka ta6a ta!’
Atare suka ɗago suna kallonsa kowannan su na huci,
Ruƙe yake da hannun junaid cikin nasa, yana sanye da jallabiya junaid kuma na sanye cikin riga fara da wando baki, ya tsorata da ganin halin da sehrish ke ciki gashi kuma yayi mamakin ganin ta ta bayyana kanta a matsayin mace, ga kuma jahan tsaye ruƙe da belt wato zai jibge ta,
Idasa isowa sukayi inda suke tunkan abbansu yace wani abu Ayaan yace “Daddy dama wannan yaron tukur mai aikin gidan mu mace ne ba namiji baa !!
murmushi Abbansu yasaki yana kallon su yadda duk suka zabura,
Mayar da idonsa yayi kan Yarinyar dake 6oye abayan azmee yace “Ke zonan,”
“Sehrish ki fito Abbansu na kira,”
Azmee ce ke tunasar da ita, fitowa sehrish tayi jiki na kerma ta ƙarasa inda Abbansu yake tsayawa tayi at front of him murya na rawa take faɗin “dan Allah kuyi haƙuri ku yafe mun, nasan nayi laifi wlh ni banzo da niyar na cutar da kowa ba…..’
tsawa Jahan ya daka mata da cewa “Rufe ma mutane baki kona zo nan na nakaɗa miki shegen duka,”
Abbansu yace “Ya isa haka Jahan, bana so kowa yasake magana,” shiru su kayi gaba ɗayansu suna sauraron mai abban nasu zai ce,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23Next page

Leave a Reply

Back to top button