ABBAN SOJOJI BOOK 2 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 2 COMPLETE

shin wai ina haroon ? Ae tuni ya koma cikin bedroom ɗinsa cikin tsananin ƙunci ransa yayi mugun 6aci sai faman yawo yake a ɗakinsa cike da jin baƙin ciki aransa sai faman huci yake bakowa yafi bashi haushi ba face Abbansu da Babban yayansu saboda sune suka nuna Amincewarsu da ita, a can ƙasan zuciyarshi kuma bakowa yafi ƙuntata masa ba fa ceJUNAID Saboda shine silar komai daya fara sanar da Abbansu akan maganar yarinyar, dama junaid ya jima yana ci masa tuwo a ƙwarya don ya lura Yaron Abbansu yafi Son shi fiye da kowa tunda har bai iya 6oye son da yake mashi agaban kowa, Kuma ya Lura cewa Babban yayansu ya mutu akansa hakan na nufin shima Yafi SonJUNAID bama su kaɗai ba kowa na gidan in kana so kaga fusatar shi to ka ta6a junaid nan xaka ga tashin hankali, shiru yayi a lokacin ya koma gaban mirror ɗinsa yana kallon fuskar shi ta cikin madubi, a fili yace “sabodaJunaid Abba da Babban yaya suka mare Ni, a gaban ƙanne na, mutun Uku da suka kasance maƙiya na acikin gidan nan muddin inaso In ƙuntata musu dole saina Cutar da JUNAID ????

ya faɗi tare da sakin wani irin shu’umin murmushi yace “Haroon kenan Mai Fuska biyu ! Wasu suna mun kallon shashasha ɗan giya yayin da ni kuma nake masu kallon garori wannan Alwashi ne na ɗaukarwa kaina saina Tarwatsa farin cikin gidan nan kuma ba da kowa zanyi amfani ba fa ce JUNAID ????????

“na’am ” ya amsa yana Satar kallom sehrish da ta kira sunan shi ta wutsiyar idon shi, “nifa tsoro nake ji junaid nagaza cin abincin dake gaba ba,” murmushi junaid yasa ki tare da cewa “CALM DOWN your mind reesh, ke fa ynx ƴar gida ce, ki saki jikinki ki ci Abincin ki a natse,” murmushi tasaki yayin da ta sa hannu cikin plate ɗin dake gabanta mai ɗauke da fried chicken taci gaba da ci, ta6e baki Jahaan yayi yana kallonta aransa yace ” ƴar shisshigi da kutsu bansan daga ina aka samo wannan yarinyar ba yanzu haka bata Wuce Zariyya dama gata nan kamar Zararrriya sai faman zare ido take,’ ya yi maganar yana Hura hanci kamar wanda akayiwa dole yana Cusa bugger abakinsa, Ayaan kuwa cewa yake yi aransa “ƙarfin hali irin na Ifritanyar nan kalli yadda ta wani shige tsakanin Abban mu da junaid tana cin abinci ita ga isasshiya mai walkin sa, ala dole ga ƙanwar Sojoji zaki gane kurenki ! Jibi kunnuwanta don Allah kamar na Zomo falo falo sai faman ƴan ƙefce ƙefcen ido take kamar wadda aka aza A saman kujerar lantarki……,????

Har cikim ranta sehrish duk ta tsargu da su Twins kamar tasan abunda suke cewa aransu, Azmee ce keyi mata alamar ta kwantar da hankalinta don itama ta lura da abunda su twins ke mata, wani irin Kallon hadarin Kaji ????????

Tuni sgr ya bar dining ɗin dama breakfast ɗinsa shaf shaf yake yinsa gyaran murya Abbansu yayi ya kalli azmee yana cewa “idan mun kammala ku shirya ke da sehrish da Junaid saboda yi wa daughter siyayyar kayan sawa da abubuwan amfani na mata, hada ma Saloon da gyaran jiki duka komai nake so ayi mata,’
Atare Jahan da Ayaan suka ɗago suna kallon Abban nasu, shima kanal yusif abun ya basa mamaki, Sehrish kuwa murmushi kawai take saki haka Junaid daɗi kamar ya rufe sa,
Azmeee tace “To Abba Insha Allah komai za’ayi mata,”
“Ke ma hada ke, azmee siyayyar duk zakuyi,” cike da farin ciki azmee tace “Mun gode sosai Abba Allah yasa ka da alkairi,”
mayar da idonsa Abban nasu yayi kansu Ayaan da jahan da kanal yusif yace “Bafa ni zan biya kuɗin siyayyar ƙanwarta ku ba, wannan nauyin ku ne, don haka kowa ya tattaro ya bada gudummuwa,

babu wasa a fuskar shi yayi maganar, shiru su kayi don baza suyi mashi musu ba, Abban nasu yaci gaba da cewa “Yusuf kai zaka biya kuɗin siyayyar kayan sawanta, Jahan kuma shi zai ɗauki nauyin kayan ado na mata da za’a siya mata, sannan Ayaan shi kuma zai ɗauki nauyin na gyaran jiki hada takalma da bags ɗin da za’a siya mata ina fata duk kunji,” sam takaici ya hana twins yin magana bawai kuɗin bane damuwarsu ba sam basu da matsalar kuɗi saboda bada albashinsu suka dogara ba, Mahaifiyarsu duk ƙarshen wata tana tura masu makudan kuɗi dollars wannan ba tare da sanin Abbansu ba ko Babban yayansu ba, haushin su yarinyar da aka ƙaƙaba musu wadda basu san daga ina aka tsinto ta ba, gashi kuma har ana ɗaura musu responsibilities ɗinta,

“Naji kunyi shiru”? Abbansu ya tambaya yana kallo su,
Kanal yusif yace “Atm ɗin yana a cikin side drawer ɗina, junaid yaje ya ɗauko in zasu tafi,”
Jinjina kai Abbansu yayi tare da cewa “Haka nake son ji ku fa”?
har suna haɗa baki wurin cewa “akwai kuɗi cash a ɗakin mu junaid yaje ya ɗibi yarda zai ishe su,in kuma Atm suke so shima yana anan saman mirror muka barshi….” suna magana suna yatsina fuska irin an musu dolen nan,

Kanal yusif yace “A’a Abba ba sai sun bada nasu ba, kawai suyi using da Atm ɗina zasu ishe su har ma su rage,” acewar kanal yusif,
Abban su yace “a’a ni nafison su sauke nauyin dake akansu na ƙanwarsu yakamata tun yanzu su son yadda zasu ɗauki ɗawainiyar mace kafin Allah yasa lokacin auransu yazo,”
. atare suka haɗa baki wurin cewa”Aure kuma Abba,”
“Eh mana” ya amsa musu,
Kallon Ayaan jahan yayi tare da cewa “tashi mu tafi lokacin aiki yayi ” miƙewa Ayaan yayi yana cirar tissue yace “Abba mu mun wuce,”
Murmushi Abbansu ya saki tare da cewa “adawo lafiya, aure dae ba fashi in lokacinsa yayi mutun ko bai so saina ɗaura masa in yaso ya haɗiyi zuciya ya mutu, zan zauna in ta zuba muku ido ne,”
fashewa da dariya junaid yayi bashi kadae bama hada su azmee da sehrish, kanal yusif dae murmushi kawai yayi,

Na wani lokaci kowa yabar dining ɗin cikin zumuɗi sehrish ta wuce don ta shirya zasu tafi Shopping mall ɗoki har ba’ayi, shima junaid bedroom ɗinsa ya wuce don ya kimtsa yau zasu yi fita ta musamman da sehrish don ya tsara har ice cream sai sunje sha, haka itama azmee kimtsawar take yi don su fice,

Haroon sam yagaza fitowa saboda kunyar haɗuwarsa da sehrish baisan martanin da zata yi mashi ba, dama jiya ta yarda masa magana a cikin toilet ina ga yau da tasamu ƴanci Allah kaɗai yasan Zagin da zaisha, ga yunwa yana ji amma sai faman zarya yake aransa yana faɗin “Ke ma bazan ƙyale ki ba Yarinya saina ƙasƙantar dake kuma bazan fasa abunda nayi niyya ba akan Ki,YANZU WASAN YA FARA ????

Fitowa azmee tayi jikinta na sanye da doguwar riga ta atampha ta kashe ɗaurin kallabi, sai ƙamshi take cikin hanzari ta wuce kitchen saboda tunawa da Marshal Omar wanda bai fito yin breakfast ba kuma ba’a kai masa ba, shaf shaf ta shirya masa a tray ta wuce part ɗinsa ta shiga da Sallama babu kowa a falonsa hakan na nufin koma bacci bai tashi ba, ajiye masa tayi asaman ƙayataccen table ɗinsa sannan ta fuce,

Tana saukowa down stairs taci karo da haroon wanda ke tafiya cikin sanɗa zai shige kitchen wai don karya ci karo da Sehrish
girgiza kai azmee tayi aranta tace “Shi ko haroon ko lafiya yake faman tafiya cikin sanɗa haka kamar mara gaskiya, Ni wlh nama manta dashi ashe yana nan,’
Gyaran murya tayi tare da cewa “barka da fitowa mlm haroon,” firgit yayi tare da juyowa ya kalle ta, ajiyar zuciya yasaki ganin azmee ce “Aunty azmee barka dae fatan an tashi lafiya, shine aka manta dani ina ta fama da yunwa yanzu da ban fito ba da shikenan sai dae yunwa ta kashe ni ko? Ya tambaya hada ruƙe qugu dama ransa a 6ace yake………
Azmee tace “Kayi haƙuri wlh ni sam na manta ban lura da baka fito ba ba,”
ta6e baki yayi tare da cewa “koda yake dama ae ni ba’a sona na lura, bama kallon mutun ake mun ba acikin gidan nan kowa ya raina ni,”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23Next page

Leave a Reply

Back to top button