ABBAN SOJOJI BOOK 2 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 2 COMPLETE

Murmushi azmee tasaki tana kallonsa tace “kadaina cewa haka bana jin daɗi, koda kowa zai guje ka amma kasan ina tare da kai ko? Ka ta6a ganin inda UWA ta Guji ƊANTA?” tayi maganar ne don ta kwantar masa da hankali ganin ya ɗan fusata,
Sakin fuska haroon yayi sannan yace “Shikenan nadaina aunty azmee tunda baki so, yanzu dai a haɗa mun breakfast ɗina wlh yunwa nake ji har wani jiri nake gani,
Wuce sa azmee tayi tana cewa “a ina za’a kaima abincin anan ko a ɗakin ka,” cikin sauri yace “Ki haɗamun kawai natafi da abuna ɗakina naci,Zai fiye mun kwanciyar hankali na”
Kitchen ɗin tashiga ta haɗa masa a tray sannan ta miƙa masa jikinsa na rawa ya kar6a ya wuce ɗakinsa,
Gefen gadonsa ya zuna hannunsa har kerma yake yi yana cusa abincin abakinsa, kamar daga sama yaga sehrish ta bayyana agabansa jikinta sanye da Kayan Sadaukai na Yaƙi, hannunta ruƙe da Zungureriyar wuƙa kanta na ɗauke da Kambun Sarauta, hankali atashe haroon ya fesar da donuts ɗin daya cunkusa abakinsa yana kallonta cike da tashin hankali, fashewa da dariya sehrish tayi tare da cewa “Kai Haroon! Ƙaryarka taƙare ! ka jima kana ƙuntatamun gashi yanzu Allah ya ɗaukakani, babu wata sauran barazana daga gare ka ta ƙare, nazo ne don na ɗauki fansa akan ka, yanzun nan zan fille kanka da wannan wuƙar ta hannu na,
Da ƙarfi sehrish ta ɗaga wuƙar zata fille ma haroon kai, aikuwa a firgice ya miƙe tsaye yana dafe saitin zuciyarshi a tsorace

Lokaci guda Sehrish ta 6ace masa 6aaat hakan na nufin ba ita bace idonsa ne ke masa gizau,amma shi tabbas ita yagani kodai yarinyar Aljana ce ? Ya tambayi kansa,.wannan ba kowa bace face Hafsat Bature Aljanar sehrish ????
Koma wa yayi ya zauna yana ci gaba da cin breakfast ɗinsa anatse, yayin da ransa ke saƙa mashi abubuwa da dama game da mummunan ƙudirinsa

_ ???? _____

OMAR a hankali ya soma buɗe idanunsa bakinsa na ambaton addu’ar tashi daga bacci, yayin da zuciyarsa ke cike fal da son ganin Tagwayensa, tun da asuba daya sha maganin mura bacci mai nauyi yayi awon gaba dashi sai yanzu Allah yayi mashi ikon Farkawa daga bacci, a hankali yasa hannun sa ya janye blanket ɗin daya lullu6a dashi jikinsa na sanye da Night dress riga ce dai dai guiwa mara nauyi, fararen idanuwansa yafara kaiwa ya kalli agogon dake manne jikin bango ƙarfe 12 na safe yayi mamakin yadda lokaci ke gudu har haka, ko don yayi overdose na maganin muran daya sha ne yasa shi yin dogon bacci har haka,
Cikin sauri ya yunƙura ya miƙe direct toilet ya wuce , brush yafara yi yana tsaye agaban wash basin amma idonsa Fuskar Jahad da Hosana take hasko masa ta cikin mirro ɗin gabansa, shaf shaf yayo wanka ya fito jikinsa sanye da Bathrobe(rigar wanka) fara, wadda ta tsaya masa adai-dai guiwarsa, Marshal Omar kenan Son kowa ƙin wadda tarasa ????
kai tsaye wuce wa yayi ya ɗauki wayarsa dake a saman gadonsa, sak irin ta sgr ce, Company ɗaya ce waya ce ta musamman domin Manyan jami’an sojoji irinsu kirar Companyn Iphone Ce, hamshaƙiyar waya haɗaɗɗiyar gaske wadda kuɗinta sun haura 30millions, ba kuɗinta bane abun mamaki ba a’a amfaninta shine abun dubawa, ƴar bala’en wayace bakowa ma zai iya Controlling ɗinta ba sai mamallakinta.
dannata ya soma yi Contact ɗinsa ya shiga kai tsaye numbar aunty BABBA ya laluba, ya buga mata Calling ta shiga ringing, burinsa tayi picking yasanar da ita cewa Zai shigo kaduna don ya duba su Hosana da Jahad, almost 3 times ba’a ɗaga kiran ba, domin kuwa wayar tabar ta agida, canza ra’ayi yayi ya dannawa Wayar Hafsat kira,

Suna a asibitin nan zaune saman waiting seats, bacci duk ya kwashe su daga zaune don daren jiya ba wanda ya runtsa sai da sassafe wurin ƙarfe 10 suka samu baccin wahala shima saboda likita yasanar dasu cewa Yarinyar da ranta bata mutu ba, farkawa ne kawai batayi ba doguwar suma tayi, shine suka ɗan samu natsuwa suka baje suna bacci kamar wasu shanaye ga uwar yunwa na cinsu, kiran Omar ne yashigo da ƙarfin gaske a wayr hafsat dake acikin purse ɗinta data aza saman cinyarta, a firgice suka farka su duka wuri wuri da ido, cikin hanzari hafsat ta zura hannunta cikin purse ɗinta ta duba me kira sunan MARSHAL OMAR ne ya bayyana, dafe ƙirjin tayi hankali atashe tace “MUNSHI GA UKU ! MOMMY YA OMAR NE KE KIRA”????

Mu haɗu ranar monday Insha Allah????

Kar amanta da paymemt wanda suka shirya sumin magana 08103884440, 300 ne VIP kuma 700 ga wanda basa ra’ayi a grp????????????ABBAN SOJOJI????????????

????The Father Of Soldiers????

ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ ﺭﺍﻓﻴﺖ❤????????????????

Story & Written by
Hafsat Bature Muhammad

~????BOSSLADY????~

Abban Sojoji part 2

EPISODE 7-8

AYAAN arab name ne for boys means God’s Gift (kyautar Allah) ❤️

Waro ido waje aunty babba tayi tana faɗin “Shikenan komai ya ƙare, Hafsat kada ki ɗaga kiran nan, katse shi kwai , a rude take magana, Hafsat tace “Mommy how can i reject his calls ! Idan zuwa zai fa ? ba kwara na ɗaga naji mai zai ce ba, don mu son yadda za’ae mu dakatar dashi ba…..’ ta ƙare maganar tare da ɗaga kiran ta ƙara a kunnanta tana Zabga sallama,
Hankali atashe aunty babba ke cewa “Kisa wayar handsfree,” cikin hanzari hafsat ta mayar da kiran handsfree don aunty babba tasamu damar jin abunda Marshal Omar ɗin zai ce,
Bayan ya amsa mata sallama yace “Zan Shigo kd yau insha Allah ki sanarwa Mommynki,” yana faɗin hakan ya katse kiran since bfr hafsat tace wani abu,
Cikin tashin hankali Hafsat ta janye wayar daga kunnanta,a wani slow tana kallon mommynta wadda itama kallon nata take yi ido azare,
Murya tamkar zatayi kuka tace “Mommy duk ke kika ja mana wannan bala’en da muke ciki, gashi nan daga ni har ke ba wanda ya runtsa daren jiya rabon mu da abinci ma tun jiyan, yanzu kuma gashi Ya Omar zaizo, Ina fata kin tanadi bayanin da zakiyi masa game da Twins ɗinsa da kika Faffasa ma fuska, ki ka canza musu kamanni, nayi imanin kema Ya omar bazai barki ba, sai ya Canza miki kamanni, don Allah naushi ɗaya zai ma kumatun nan naki Mommy sai an neme su an rasa a fuskarki,’
Tuni ido ya raina fata, aunty babba tace “hafsat ki daina mun waɗan nan suratan naki ki barni inji dakaina, yakamata musan abun yi before Omar ya diro garin nan,’

Zama su kayi zugum kowa zuciyarsa na bugawa daram daram, kowa da irin idea dake zuwa masa akai,
Jahad kuwa na a ɗakin da aka kwantar da hosana dama gado biyu ne aciki, itama doctor sai da ya duba ta, baccin wahala kawai take yi saboda allurar da dr yayi mata don tasamu bacci, duk inta farka sai ta ambaci sunan Hosana saboda itace aranta, so take tama fi ƙarfin allurar da dr yayi mata, don ƙoƙori take ta tashi da ƙarfin gaske don taje ma hosana wadda ke kwance magashiyyan rai hannun Allah ????


Bayan Omar ya kammala wayar fitowa yayi daga bedroom ɗinsa ya zauna a palor saman sofa yana yin breakfast ɗinsa anatse, wayarsa ce ta shiga ringing wadda ya ajiye agefensa, kai idonsa yayi ya duba Gwaggon katsina ce ke kiransa, murmushi yasaki don kusan kullum saita kira layinsa ta tambayesa ina Ƴa’ƴan Abusufyan ɗinta ya basu su gaisa, hannu yakai ya ɗauki wayar ya kara a kunnansa yana faɗin “Gwaggona kenan fatan kin tashi lafiya,”
Daga can 6angaren gwaggon katsina tace “Allah sarki Omar jiya ko isasshen bacci ban samu ba saboda tunanin ƴa’ƴan abusufyan ɗina, Jiya zuciyata tayi ta bugawa inaji kamar wani abu ya same su, dan Allah Omar karka bari a cutar dasu,
Sai faman zuba take masa a waya sam taƙi bari yace wani abu har sai da ta gaji ta dakata da maganar sannan Omar yace “Ki kwantar da Hankalin ki goggo na, Ƴa’ƴan abusufyan ɗinki suna nan cikin ƙoshin lafiya,”
Ajiyar zuciya tasaki kafin tace “Suna tambayata ko? Suna atare da kai Omar? Ka basu dan Allah muyi waya mana,”
omar yace “Goggo kin manta suna a kaduna,ae gidan Yaya ishaq nakai su…”
Kamar tana agabansa ta zabga salati
tana cewa “La’ila ha illallah Mahammadar rasulillah Omar ! dama gidan Ishaq ka kaisu? Gidan wannan matar Shuwa mai ƙirar samudawa sam matar nan bata da Imani, zuciyarta irin ta kafuran farkon ce wlh, shikenan ni Allah kaɗae yasan wane hali ƴa’ƴan abusufyan ɗina suke ciki . ……fashe masa da kuka goggon katsina tayi,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23Next page

Leave a Reply

Back to top button