BAKAR WASIKA 11

“Madina ce”
“Eh Momy ya gida?”
“Lafiya Kalau ya Maman ki?”
“Lafiya Kalau take”
Ta amsa tana murmushi, sai Momy ta mike tsaye ta nufi hanyar dakinta dake kasa. Daga Leila har Madina binta su kai da kallo sai da ta shige sannan Madina ta kalli Leila.
“Wai da gaske baki san inda Talba za shi ba?”
“Ba zai wuce Office ba”
“Amman ya karya kamin ya fita?”
Ta daga fadunta alamar bata sani ba.
“Sometime a office yake karyawa wani lokacin kuma a bangarensa”
“Wani lokacin kina bani mamaki Leila, idan an yi magana ki ce kina son Talba, amman baki san abun da yake so ba, da wanda baya so, ba ki kokarin kiyaye bacin ransa”
“Shi yana kokarin kiyaye nawa ne? Yana son a rika masa sakon soyayya ana tambayar Lafiyarsa an damuwa da shi, amman shi be damu yai min ba, ni fa macece be kamata na zubar da kai a kansa ba”
“I know amman idan kin kula haka rayuwarsa, then why ba zaki bishi ku tafiyar da rayuwarku a haka ba, I’m sure idan kuka yi aure komai zai canja”
“Zamu yi aure, amman sai na gasa masa gida a hannu tukuna, and kina bukatar sanin wannan, Talba wanda zan aura ne ba wanda na aura ba, me yace me zai ci rayuwarsa for now bata dame ni ba”
“Haka dai kike gani, amman matakin kulawa daga yanzu ne, ni ina ganin ya kamata ma ki fara aiki ta haka zaku samu fahimtar juna sosai”
Rausayar da kai Leila tai.
“Madina, miyasa kike yawan damuna da maganar Talba ne? Ban shirya aiki yanzu ba sai na yi masters”
“Ina tsoron kar ya kubuce miki ne!”
“Really….”
Leila ta fada tana dariya.
“Ke a tunaninki akwai abun da zan nema na rasa a rayuwata? Haba Madina, ai Talba ko daga wani tsatson ya fita Daddy da Momy za su tsaya min na same shi, ballr kuma a jinina Talba ya fito, ba wai rasa shi ba, soyayyata ma ya hada da ta wata ma be isa ba, balle har ya hada ni da kishiya, haufi daya ne akan halayyarsa”
Madina ta yi murmushi.
“Leila kenan, na san kina da gata ta ko’ina, amman Talba yafi gaban yadda kike tunani, kar fa ki manta shi namiji ne”
Leila ta juya ido.
“Please My friend mu aje maganar Talba a gefe, kin san wai ko jiya na yi mafarki matar nan?”
Madina ta zaro ido.
“Da gaske?”
“Wallahi, ina ganin kamar ko yawan tunaninta da nake ne yasa nake mafarkinta”
Madina ta yi shiru tana kallonta kamin ta ce.
“Amman kin san fa hakkin jini…”
“Hakkin jini Madina sai kace wanda na kwantar na yanka? Kamar yadda Momy tace mistake ne, kuma kowa yana iya yin laifi ai dan adam ajizi ne ko?”
“Yeah.. Amman wannan kamar da banbanci Leila… ”
Ganin Leila zata yi mata wata maganar ta daban yasa Leila kawarta maganar ta hanyar dauko wata maganar.
“Ya aikin ki?”
“Alhamdulillah, ni aikin ma ya fara isata Wallahi”
“Kamar ya?”
“Ayukan ne basa karewa kuma gashi bama tashi da wuri, kuma zuwa kullum ne, ni da zan samu wani aiki ai da na aje wannan”
“Kamar ya zaki samu? Kin fa yi karatu ne Madina”
“Na sani amman idan ba irin kamfaninku ba ne da suke biyan ma’aikata da kyau kin san ba ko wane aiki zan iya ba”
“Idan kina son aiki a kamfaninmu ai zaki iya samu”
Madina ta wara ido tana murmushi.
“Da gaske?”
“Haba dai kina kawata ki nemi abu a gurina kuma ki rasa samu? Ki kawo takardunki kawai zan yi ma Daddy magana”
Da sauri Madina ta bar inda take zaune ta rumgume Leila tana wani irin murna. Leila ta yi dariya.
“Are you kidding me? Ai ko mahaifinku kika yi ma magana zai canja miki aiki domin su ne manya a gobnati, amman kina ta kewaye kamar wanda bata da kowa”
“Ba haka bane, Leila na dade ina mafarkin aiki a kamfaninku Wallahi”
“Amman shi ne baki fada min ba? Haba dai Madina ina ganin kamar mun zama daya ni da ke?”
“Ai da nauyi, amman dai yanzu komai ya wuce na gode sosai zan kawo takardun anjima ko gobe Inshallah na gode sosai dear ina kaunarki”
Leila ta yi murmushi.
“Karki damu, i trust you”
“Bari na tafi kar na yi latti”
Ta fada tana daukar jakarta ta rataya, sai Leila ta rakota har gurin motarta sai da ta shiga ta bar gidan sannan Leila ta juya ta koma ciki.
BATURIYA POV.
Har ta huta ta ci abinci yayanta be dawo ba, daman idan ya fita gurin kasuwancinsa baya dawowa sai dare. Batan ta yi wanka ta fito ta tari Napep ta nufi family house dinsu.
Tana shiga cikin gidan kannenta da mahaifiyarta suka hau murna kamar su hade ta. Ko minti talati ba ta yi da zama ba, Sultan ya shigo cikin gidan da gudunsa, kanwarta ta fara tare shi ta daga shi sama yana dariya.
“Sultan kaga Mama ta dawo?”
“Tace a daina cewa Mama sai Mommy”
Ya fada da yar siriyar muryarsa yana kallon Baturiya dake zaune falon.
“Kai da wa ka zo nan?”
“Daddy yana waje”
Wani tsaki taja ta dauke kai.
“Zuwa zai yi ya fara min bakar masifar nan Ko?”
“Aa ya isa? Ai Raliya ta fada masa halin da kike ciki, ko ma haka be faru da ke ba tun da ya ga baki dawo gida ba ai ya san ba lafiya ba, dole ya daga miki kafa”
“Uhm Umma baki san halin Faruq ba, Wallahi ni da nake tare da shi kawai na san ukubar da nake sha a gidansa, zai iya zuwa a nan ya nuna babu komai sai mun koma gida ya fara min masifa”
“Bayan duk hakurin da kike da shi? Cikin yan’uwanki ke kadai ce baki dace da daki ba Rafi’a, ba mu yi zaton haka ba”
Wannan maganar da Umma tai sai ya saka Baturiya ta kara bata fuska.
“Wallahi Umma ni kadai na san azabar da nake sha a gidan Faruq, bayan yunwa ga rashin sutura da kwadayi, ga masifarsa kamar ni na dora masa talauci”
Umma ta sauke ajiyar zuciya tana kallon yarta cike da tausayawa.
“Shiyasa tun farko ni bana son auren nan na zumunci, mahaifinku ne ya dage sai an yi gashi nan ya tafi ya barki da wahala, haihuwa daya kenan nan gaba idan an tara yara me kike tunani”
“Ni ma tsorona kenan Umma, haihuwa daya, rayuwa tana ta mana haka balle nan gaba, kullum dai dai tai ta min karyar aikin zai fito amman shiru”
“Ni abun nasa har mamaki yake ba ni, wai ko dai be yi karatu mai kyau ba ne”
“Ni ina na sani, tun da ba fada zai yi ba, ni Wallahi makaranta ma nake son komawa, kar na bata nawa future na zama irinsa”
“Aiko da kin yi ma kanki abu mai kyau, sai ayi ma yayanku magana ya biya miki”
A take murmushi ya cika fuskarta.
“Da gaske Umma?”
“To miye a ciki idan ma be biya miki ba, ai ni zan biya miki”
Umma ta fi tausayin Baturiya fiye da kowa a cikin yayanta, domin ita kadai ce take auren matalauci talaucin da abun da zasu ci ma sai ya gagaresu wani lokacin. Ba wasu masu arziki ne can sosai ba sai dai suna da rufin asirin irin na yayan da suka dace da daki, domin kusan duk abun da ake ci a gidan yayyun Baturiya ne dake aure suke kawowa, sauran dawainiyar kuma babban yayansu ne yake yi, domin yana da rufin asiri irin na wanda kasuwanci yai ya aura.
“Sultan je kace Daddy ya shigo kar ya ce an barshi a waje”
Baturiya na fadi hakan Sultan din ya sauka daga kafafuwan kanwar mamansa ya nufi kofa da saurinsa, ko da ya fito Faruq na tsaye bakin karamin gate din gidan rumgume da hannayensa.
“Daddy ance ka shigo”
Faruq ya sakar masa murmushi sannan ya kama hannun dansa suka shiga cikin gidan, cike da nauyi ya shiga kasancewar baya samun riko musu komai idan zai zo, ba kamar sauran surukan ba da har mararin zuwansu ake saboda suna da rufin asiri, Baturiya ma ta sha fada masa shi kadai ne baya kawo komai idan ya zo, hakan yasa idan ba da wani babban dalilin ba baya son shiga cikin gidan duk kuwa da kasancewarsa dan’uwa, shi kansa ya san baya samun sakin fuska a gurin mahaifiyarta yadda ya kamata.
A bakin kofar falon ma tsayawa yai sai da aka matsa iso, sannan ya shiga cike da kunya ya nemi guri kusa da matarsa ya zauna bayan ya gaishe da sarakuwarsa kuma matar Kawunsa.