Labarai

Akan Maganar Aminu da A’isha Buhari

Akan Maganar Aminu da A’isha Buhari.

 

Tunda farko na nuna rashin goyon bayana akan kalaman da zasu iya janyo tashin hankali ko salwantar rayuwa akan kowane ɗan siyasa. Dimokraɗiyya ta yarje mana ƴancin magana har da suka akan duk abinda zai kasance bamu ƙetare doka ba, musamman idan kanada hujja me ƙarfi da zaka iya kare kanka. Haka kuma sam bana goyon bayan amfani da ƙarfin mulki da mulaka’un ƙasar nan sukeyi wajen cin mutunci, ko kame na babu gaira babu dalili ga duk wanda ya qalubalanci wani abu daga mulkin su.

 

Idan har da gaske an lakaɗawa Aminu duka a hannun Jami’an tsaro, to wannan ya saba kowace iriyar doka a ƙasar nan. Idan har ba’a gurfanar da Aminu gaban quliya a kwanakin da doka ta tanadar ba, bayan kammala duk wani bincike, to wannan ma bai kamata ba. Wannan shine gaskiyar zance.

 

Na farko Ina tausayawa Iyayen Aminu da irin halin da suka shiga. Shima Ina jajanta masa, ganin cewa zai iya rasa zana wasu daga cikin jarrabawar da Jami’ar sa zata gabatar nan da wani lokaci. Ya Kamata Uwargidan Shugaban ƙasa ta tuna cewa ita uwace ga kowa. Yacce take mutunta yaran cikinta, haka kowasu Iyaye suke mutunta nasu. Yadda take fatan goben yaranta suyi kyau, haka kowasu Iyaye suke yiwa ƴaƴansu irin wannan fatan.

 

Ina cikin masu goyon baya, tare da kira da murya mai ƙarfi ga Uwargidan Shugaban ƙasa ta tuna matsayinta na Uwa. Ta nuna juriya, kawaici, tare da sanin cewa abubuwa da dama basa tafiya daidai a ƙasar nan, wannan dalili ya sanya mutane da dama ke amfani da hakan wajen nuna rashin jin daɗinsu da salo da tafiyar wannan Gwamnatin. Idan zan iya tunawa, itama ta taba nuna fushinta da salon tafiyar Gwamnatin Mijin nata.

 

Dole ne muyi suka ga duk Gwamnatin, ko wani mai muƙamin siyasa akan duk abinda muka ga ba daidai ba, amma dole muyi hakan da lura. Munada ƴancin hakan, haka itama Gwamnati batada ƴancin daqile wannan ƴancin da muke dashi.

 

Mailafiya.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button