Labarai

Laifin da mamba na dandalin WhatsApp ya aikata ka iya shafar jagoran dandalin, in ji tsohon NBA

Laifin da mamba na dandalin WhatsApp ya aikata ka iya shafar jagoran dandalin, in ji tsohon NBA

 

Wani tsohon sakataren yada labarai na Ƙungiyar Lauyoyin ta Ƙasa, NBA, Douglas Ogbankwa, ya ce alhakin laifin karya dokar amfani da yanar gizo ta 2015 ka iya shafar jagororin dandalin WhatsApp, wato WhatsApp Group admin.

 

Ogbankwa ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN a jiya Talata a Legas.

 

Ya ce da yawa daga cikin jagororin dandalin WhatsApp sun bayyana cewa sun jahilci tanade-tanaden dokar ta Intanet, wadda ta bayyana laifuka irin su cin zarafi da kazafi da sauransu.

 

A cewarsa, rashin sanin dokar ba hujja ba ce.

 

Ya ce sakamakon ƙaruwar aikata laifuka ta yanar gizo, dokar ta intanet ta yi tanadi a tsanake don duba ayyukan intanet da suka hada da kafafen sada zumunta.

 

“Dokar Hana Laifukan Intanet ta 2015, ta tanadi alhakin admins na rukunin whatsapp; don haka ina ganin yakamata admins group su duba dokar domin ta tanadi cewa admins dole ne su kare muradun wasu mambobinsu.

 

“Don haka, idan aka yi wani rubutu da ke barazana ga tsaron kasa ko kuma zaman lafiya, dokar ta ce kaifin ka iya shafar irin wadannan admins ɗin ..

 

“Saboda haka, yana nufin rashin sanin tanade-tanaden irin wannan doka ba zai zama hanyar tsira ga kowa ba kamar yadda aka baiwa admins na WhatsApp ikon goge abubuwan da ba su da kyau gaba daya daga dandalin.”

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button