ALIYU GADANGA Page 21 to 30

Shiko Aliyu tunda ya Shiga bariki abubuwa suka mai yawa,sai zuwa darene,ya samu kiran Ummah tana Shaidamai Azeema tana wajen Madina zatayi sati awajenta kafin Su kawota nan Barrak din,Ummah ta fake ne da cewa akwai wani dan gyare gyare da sukeyene,bai damu ba yace Bakomai,dayake Aliyu Namiji ne,kuma Soja,so kwakwalwarsa bata kawomai wani gyara akema Azeema ba,yafi bada kila lalle za”ayi mata da kitso,kowani Abu dabam????Shiyasa bai damu ba,bai samu komawa gidan kawu ba yabari sai dai da safe,in jabir ya dawo suzo tare dashi Tunda shi bai samu dawowa Aranar ba sai washegari.
Suko Su Azeema basu tafi kasuwa Aranar ba saboda yammah tayi,gashi su hibba sun dawo daga sch nan fa suna cin karo da Azeema sukayita ihun murna kamar su maidata ciki sun hanata sakat,itako tana biye musu Ranar ko Maminsu basu bi ta kanta ba,hatta cire musu uniform da saka musu kaya na Azeema sukace suna so tayi musu,wanu homework ne,harda yar goye goye duk ita kadai,dayake kuma ta saba da yaran,kuma kunsan Aduniya babu aikin da zai gagari Azeema sai dai in ba”a kirkiroshi ba,Karshenta dai Ranar dakinta suka tattara sukace wlh chan zasu kwana har jan madina tayi musu suka makale su Tare Anty Azeema zasu kwana,Azeemar ta roki,Anty madinar kafin ta kyalesu su kwana,aiko sun kai wajen 11 suna hira,kafin su kwanta,ta Shege tsakiyarsu kaunarsu na Ratsata tana fatan kada Allah ya Dau Ranta sai ta haifi mace ta sakamata Suna FATEEMA..,Niko nace karki damu Azeema very soon Aliyu zai baki kwan haihuwa????????
Sai washegari suka samu Tafiya,bayan yaran Sun tafi mkranta,kasuwa suka Shiga Madina ta darzomata Atamfofi Masu Rai da lafiya super,holland,swices less,codde less,material dogayen Rigana,masu sikat da masu wando,Mini sikat da mini wandunan,bras,pants,kayan kwalliya komai da komai da kayan mata sai da ta siyamata harda takalma masu Tsini da Flat,sai kananun jaka,dan kunne,masu sarka da Fashion Bands,da sauransu kafin su wuce shagon dinkinta,tabada dinkunan kayan,wata in yamurace bosse,ta gwada Azeemar tace jibi ta aiko direba ya karbi dinkunar,bayan madinar ta ijiyemata kudinta cash,suna Fitowa dagana shagon salon takaita aka wankemata kai harda gyaran kafa sukayimata,wajen harda gyaran jiki sunayi,ammh sanin itama madinar sana”arta kenan basu mata tayi ba,domin sun santa tun Tuna budurwa suke gyaramata kai,ta yarda da shagon sun san aikinsu sosai,basu dau lokaci ba,suka kammallamata sai ga gashin Azeema ya mike sosai yayi kyau kamar ba ita,ba kudinsu tayi musu Transfer ta banki suka Fito suka wuce,daganan anguwan Rimi suka biya gidan wata kawarta SALAMATU FODIO SG GUMBI..Ta amshi wasu tsimi ahannunta tare da Wasu garin magani cikin wasu robobi,dayake sana”arta kenan itama,basu wani jima ba,daganan suka koma gida,suna komawa gida,madina ta shiga tiolet ta hadamata Ruwan Turaruka masu tsada hadin yan maiduguri ne,ta umarceta data Shiga tayi wanka,ita kuma ta sanya wani kasko ta kunna Hurashi ta watsa Turare,tana Fitowa da digon Ruwan ta Umarceta data tsugguna hayakin Turaren ya dinga shiganta,ba gaddama Azeema tayi yarda Madina tace,sai da ya sike kana tace tatashi,wani hadin mai shima cike yake da wasu hadin Turaruka tabata tace daga yau yazama man shafawanta,karba tayi ta shafa,kayan da suka siyo ta zazzage pants dinta ciro mata kafin ta miko mata wata kwalba tana fadin”Rike wannan almiski ne,zaki dinga digama wandunan ki kafin ki sanya kinji ko? amsa Azeema tayi tana fadin”Naji Anty..”wani riga da Sikat Madina ta mikamata tana fadin”Karbi ki sanyasu,wadandan Dressing din,duk bayan kin daidaici lokacin dawowar yaya captain ya kusa zakiyisu,ammh bayan kin tabbatar da Dinner dinshi is ready kinji ko..”kai Azeema ta gyada tana Fadin”Naji Anty..”kada kai tayi tana fadin”Shirya bari baje na hada miki Sauran magungunar ga Turaran wankan chan a tiolet sau biyar akowanni Rana,Kowani wanka Murfin jarka Uku zaki sanya,na sati daya ne,bari na kawo miki Sauran na garin akwai na karin Ni”ima kana kuma akwai na mganin infection ma”ana Sanyi…”Gyada mata kai Azeema tayi alamun ta Gane ficewa tayi tana fadin”In mun gama da wadanan kingane sai mu dora da lacran mu,munayi lokaci daya kuma muna Shiga kichen tare,domin kinsan Duk wadananan Abubuwan basu tasiri,sai Mace ta kasance ta iya sarrafa mai gida ta hanyar iya girki,balle nasan Sojiji da son cin Abinci mai dadi..”Tana fada tana yar dariya kan Ta fice daga daki.
Yar Dariya Azeema tayi tana bin Tulin kayan da suka siyo wadanda ke zube bisa gado,kayan da Anty tace ta saka take bi da kallo,Tana mamakin yadda zata sakasu,sai da bazata iya bama Anty madina kunya ba,da hanzari ta sakasu,kayan roba ne sai suka lafe bisa jikinta gashi sun kamamata,hips dinta ya fito tana tafiya suna rawa,duk da ta saka pant,sai kirjinta wadanda suka cika fam,suna bin bayyana,gashinta ta daure da band,kayan baida dan kwalli,Sai ta samu wata hula ta saka ta isa gaban mirrior tana kallonta sai da tayi mamakin ganin yadda kwana daya tadawo gawani Fitinannen kamshi na binta da ko”ina,duk inda ta Shinshina ajikinta sai taji kamshi,ita ta kanta take lumshe ido in ta Shaki kamshin jikinta,shafa fuskarta tayi taji wani Santsi Mirmishi ya subuce mata lokaci daya hawaye sun ciko idanunta ta furta ahankali
_Thank you,Yaya captain,Thank you goggo,Thank you Ummah and Thank you too Anty madina.._ take fada tana goge kwallar data zuraromata bisa kumcinta
Madina dake bayanta ta bugamata tafi tana fadin”Weldon matar Yaya da alamun zaki Saurin dauke komai kafin sati dayanmu ta cika,..”Tafada bayanta yar aikinta ne,ke ta Shigo dawasu jarkunan magunguna dawasu arobobi sai madara Sajet sajet,sai Zuma awata katuwar gora sai gumba mai yawa,gabanta tasaka aka zube haka ta zauna ta tankwashe kafa itama Azeemar ta sauko daya bayan daya take maata jawabi,da wanda zata sha da madara,dana sha da zuma,komai dai tayi mata jawabi,harta Fahimta,nan kuma ta ake ta shiga hadamata ta mikamata tana Sha,duk da wasu suna da bauri,ammh hakanan take Daurewa Tunda ba laifi takan danci karo da mai dadi har dawani hadin Dabinon makka mai dan karen dadi,Azeema taji dadinsa sosai,shida wani garin Aya shima da madara ake sha Duk sun mata dadi sosai,Tana gama sha madina ta kwashe ta sanyasu gefen gado tana fadamata Sau daya zata dinga sha Arana,ammh Turaren Tsugguno sau biyu arana safe da yammah Ficewa tayi ta barta tana fadamata cewa gobe zasu Fara lacra su,da safe Allah barshi da yammah sai sudinga Shiga kichen domin koyar da ita girke girken zamani wato Akushi da Rufi????Tuni Azeema ta amsa da toh domin Ta fahimci Rayuwarta ta yanzu tafikomai dadi,koba komai itama tanaso ta waye tazama irin Anty madina da kawayenta,zaka gansu so classisc mallam babu Raini ko kadan.
*Intellenget writers asso..*
*Janafty..Aka Shakira*????
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_
*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty????_
*DEDICATED TO MY MOMMAH…HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*
_Special gift to my Real Dota RAHMA????Ladingo yar mutan Niger_
*Intelligent Writers Association*✏
_*Kyakyawan Shafi lokaci Daya da kyakyawan sadaukarwa,eh mana domin Duka Shafin yau na ALIYU GADANGA.,Kacokan Dinsa sadaukarwane ga Daukacin malamai da Shugabannin dake mkrantar primary U.B.E. KOFAR KIBO ZARIA..,Gaisuwan Fatan alherin zuwa gareki ne mai gayyah mai aiki,headmistrees HAJIYA BINTA UMAR ABUBAKAR(Momy)Allah yaja kwana????????,Tare da uwar gayyah Assitances,HALIMA IDRIS(Goggo balaraba)???? Allah dai ya biya,bazan yi toya na manta da albasa ba,jinjinar ban girma zuwa gareka lantarkin zuciyata,kuma malami na,kuma uba yake awajena,lalle na kasance mai sa”a Tunda Allah yahadani da gwarzo kamar ka,UMAR BELLO SADIQ(Uncle me)????,Soyayyarka gareni sai dai nace A kinda masha Allah,Kulawarka akaina sai da na kirashi da Alhamdulillah Allah nake roko daya iya maka Abunda kagaza,Kafin na wuce zuwa wani ajin yakamata nafara Farawa da gida ne,gaisuwa tare da Fatan alheri gareku MALAMA RUKAYYAH(Maman Suhailat)sai MALAMA AISHA(mmn Fuad)sai MALLAM ABUBAKAR(mallam Ammar),Bazan manta daku ba dole ne nayi jinjinar ban girma gareku iyayan dakina,ANTY HADIZA,tare dake MALAMA AISHA,Bazan manta dake ba kawata abokiyar Cin mushe,????????,kuma malamata ba wato ANTY JUWAIRRIYAH,Son so Fisabillillah,kai zan yi Abun kunya ban ambaci uwata ba takaina ba MALAMA ZAINAB(Anty Ummi)tare dake Malama Hafsart,malama jamila,(Namecy),sai malama Harira,Anty hauwa,Malama Asiya dake da malama Hafsart,ban manta dakai ba Mallam Aminu tare da wadanda ban ambataba,gaisuwan Ban girma gareku Allah yabar zaman Tare Ameen..Ku sani ku kara sani JANAFTY AKA SHAKIRA,na Sonku Fisabilillah*_????????❤????????????????????