ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 1 to 10

 *Chapter 1*

*GOMBE*

     “””Ababban masallacin dake anguwan nan ta masu hali,wato *FEDERAL LOWCOST* Motocine suka cika anguwan Tundaga farkon farata har karshenta,layin mallacin kuwa babu matsaka tsinke saboda yadda motoci suka hada uban gowslow,kana kallon wajen zaka tabbatar da tabbas wani kusane agawannati yake Aure yau,dayake ranar takama Ranar karshen sati ne,wato asabar,Abunda zai baka mamaki,sojojin kasa ne wato army birjit awajen sanye da kakinsu suna mazurai,gefe daya kuma yan sanda ne,suma kamar anyi hayansu,sai gyara parking suke.

  Tawagar ango ce tafara isowa cikin hadaddun motocinsu na alfarma Kirar venza2019,sai 306 kirar toyota,607kirar toyota,sai Benz,bayansu kuma motar sojojine,suna tafe da jiniyansu bindigogine ahannunsu da bulalai suna wani zare ido,Abun tsoro,tuni jama”a Aka dinga darewa domin kowa na tsoron ya gifta soja ya fallamai dorina wacce kila sai ya kwana goma yana jinya bai warke ba.

Motocinsu basu gama tsayawa ba,jiniyar motocin mai girma Kwamishinar jahar Gombe tafarayima mutane maraba wato *CP AHMED SIDI NA IYA* Tare da tawagarsa,suna zuwa suka faka motocinsu nan da nan yan sandan dake biye dasu suka hau bude musu motocin suna bayyana,tabbas inda ake biki chan ake,domin manyan mutane ne,suke Fitowa cikin shigata alfarma,dukkansu sanye cikin wasu dakakkun shaddodi gezner suna daukan ido,da hulunansu zannah bukar,suna fitowa basu tsaya wajen mutane ba,suka shiga cikin massllacin bayan an buda musu hanya,yan jaridu kuwa sukayi yamm dasu suna kokarin, sonjin ta bakin kwamishinan ammh masu tsaranshi basu bada damar haka ba,kakkaresa sukayi har ya danganta da cikin massllacin inda waliyan ango da sauran manyan mutane,harda babban limamin masallacin,suke jiransu domin Daura Auren

  

*JABIR* ya kallesa ganin yadda yawani kishingida kamar yana kwance adakin matarsa yace”Mallam wai bazaka fito bane,kaga fa maigirma kwamishina ya iso,yanzu za”a daura maka ka Aure ka tabbata miji ga *NI”IMATULLAHI AHMED SIDI NA IYA..* “Yafada lokacin daya yana leka kansa cikin gaban motar…

    Yafi minti  goma bai dagoba kuma baiyi mgana ba, *HAISAM* ya gyara tsayuwa yana fadin”Kaga captain zo muje rabu dashi,Kila bai da ra”ayin isa cikin masallacin ne,mu muje saboda mu muntunta abotaka da kuma zaman tare..”Yafada daidai lokacin da suka Fito daga motar dukkansu,mazaje ne dogaye majiya karfi,kallo farko in kayi musu zaka fahimci tsantsan ilimi da wayewa ya ratsatsu,Kyawawa ajin farko ne,daka kallesu sai kara kallonsu saboda yadda suka dau wanka,cikin wani Ubansu yadi,mai ruwan kasa,wanda yanayin yadda yake yarari kadai ya isa yafadamaka sai da aka tada kai akayi iya mallakarsa, kafafunsu duka sanye da wani Brown din takalmin na fatar damisa,ayayinda kansu ke sanye da hula zannah bukar,kuma dukkansu dasame dressing ne ajikinsu,in ka gansu daga nesa kamar wata daren goma sha daya saboda yadda suke haskawa.

Ganin da gaske suke,basu jira cewarsa ba,suka dumfaru cikin masallacin domin Saura Dan mintocine adaura auren,yan jarida daga nesa suke hangosu,domin sojojin sunyi musu katanga tsakaninsu,to soja babu wargi dole sukayi gefe,Cikin wani takama da aji ya sanya tattausan hannunsa mai cike da gargasa wanda ke daure da wani royal watch mai kyau da yarari, ya bude murfin motar ya zuro kafarsa wacce ta kasance farace,ammh tana da Launin ja,kafar nasa tana sanye cikin wani ubansu Rufaffan takalmim brown colour na fatar damisa,kafar nasa itama tana cike da gargasa domin gayinan yayi kwance luf dashi,ban saki da al”amarin gayen ba,sai da duka jikinsa ya bayyana awaje,bansan sadda biron dayake hannuna ba ya subuce saboda yadda girma da haiba tare da wani kwarjini suka dakeni lokaci daya.

tsarki ya tabbata ga Allah wanda yayi wannan kyakyawan halitar,dogon mutum ne,karkafa mai yalwal Fadin kirji da girman jiki kamar ingarma,fari ne tas,mai Launin ja,Hancinsa har baka yake,mai zagaye da wani bakin Saje wanda ke karamai kwarjini da haiba, kwayan idonsa tamkar wanda aka digamai daimond,saboda yadda yake wani haskawa,Yana da manyan idanu,matsaikata,wanda in ya lumshe su,sai ka zata yayi kari,wa gashin idon nasa,don ko wata mace albarka..,bakinsa dan karami ne,wanda ke dauke da wasu pick din lip masu kyau da burgewa,Kansa yana nannade dawani murdadden bakin gashi kamar wanda yayi kari,Ko fuskarsa badon yana yawan askewa ba,akwai kananan gashi da sukayi mai kwamce,Shima din sanye yake da yadi mai ruwan kasa,irn na abokansa,hatta dinkinshi iri dayane sai dai Shi harda babban riga,Hulan kansa ma irin nasu ne,sai da yadda kayan ya amsheshi dabam ne,Kana kallonsa zaka fahimci mai karfi ne shi,saboda yadda mucsles suke yawo ajikinsa,har ana iya ganinsu,Kana kallon Fuskarsa zaka Fahimci yana da miskilanci da wani irin takama,yana da jan aji,ayanayi yadda yake wasu abubuwa sai ka dauka wani basarake ne,saboda komai cikin isa da iko yakeyinshi,baka iya hada ido dashi saboda yana da bala”in kwarjini babu wanda ya taba kallon tsabar idonshi na tsawon minti biyar ,saboda baiwace Allah yayimai mutane dadama basu iya kallonsa ido cikin ido Saboda yadda kwarjinshi yake tasiri azuciyar mutane.

   *CAPTAIN ALIYU ABDULNASEER TAMBARI BUZU*  kenan,kuma COMMANDER YAKI,wanda ke jagoranta bataliyoyin sojoji kashi da kashi zuwa filin daka,ko wani kwantar da tarzoma,Wanda ko afagen fama makiya tsoronsa sukeji,matashin Sojan kasa ne wanda ke aiki a barikin Kaduna wato 1division Nigerian Army kaduna,ko abokan aikinsa sun san waye Aliyu Tambari buzu saboda kwazonsa ga aikinsa ko manyansa ma,suna shakkarsa tare da jinjinamai domin kaf bacth dinsu babu na biyunsa ajajircewa da nuna jarumta…Sai da yawani jingina da kofar motar kafin ya dan Saki Fuskarsa ya fara takawa cikin takun nan nasa na isa da takama,sojojin dake karkashinsa sai kokarin karesa suke har ya samu nasaran Shiga cikin masallacin,kusa da Haisam ya zauna,wanda ke zaune kusa da jabir,gefensa kuma *MALLAM LAWAL BATURE* ne kafin kuma *KAWU BALA* dake gefensa shima cikin Shigan kayan alfarma.

An matso domin fara gudanar da Daurin Aure kani ga kwamishina ya kira kwamishinan gefe suka danyi wasu mganganu Tunda kawu bala yaga haka, sai ya sha jinin jikinsa,yana fata wannan karon kada ayi musu gagarumin wulakanci da zasu kasa mantawa dashi,suna dawowa Sai kani ga Kwamishina ya kalli kawu bala yace”Ina waliyan ango su matso kusa adaura aure..”Yafada yana kallonsa batare da wani Tunani ba kawu bala ya matsa yana fadin”Gani,ai inaga basai ka tambaya ba,tunda ko neman Auren wajenka na neman ma Aliyu..”Yafada Shima kai tsaye.

Bude bakinsa sai cewa yayi”waliyin ango nace,ma”ana Waliyi daga *DANGIN MAHAIFINSA* bakai ba..”Gabadaya kawu bala yaji miyan bakinsa ya kafe,dayake mganar bata karfi akeyinta ba,su Aliyu dake gefe basu wani ji,su azatonsu Ana gudanar da Daurin Auren ne,Kawu bala ya kalli mallam lawal kafin yace”Eh to ai mun fadamuku Dangin Mahaifinsa basu akusa,Shiyasa muka gudanar da komai..”Kwamishina ya murmusa kafin yace” *BALA SHEHU AKARAMI* Shine cikakken Sunanka,kuma  kaine kwamishinar yada lbrai NA ajahar kaduna,kuma kai yaya kake ga mahaifiyar Aliyu,Tunda kuka gudanar da neman Aure bawani daga dangin baban yaran,kenan ya tabbata da gaske bashi da uba,Balle Asali..”

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *


The reCAPTCHA verification period has expired. Please reload the page.

Back to top button