ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 21 to 30

Ad

_____

 “Aliyu yasha barci domin sai wajen karfe daya na Rana ya farka wanka kawai yayi agurguje ya sanya Shadda fara Dinki Muhammed riga da wando,da hula yatafi masallaci saboda ya samu jam”i,,koda aka idar da sallar bai Shigo gida ba,kofar gida yazauna yana waya da Haisam bayan sungama kiran Jabir ya Shigo wayarsa nan fa yazauna Sunata Fira,sun dau tsawon lokaci suna mgana kafin suyi sallama Akan sai sun hadu akaduna don kowannensu jibi yake san Ran komawa bakin aiki.

    Sun yanke kiran kenan sai ga KekenNapep din dayake Kai Azeema mkranta ya iso Faka keken yayi ya fito ya nufo Gadanga wanda yake binsa da kallon mamaki karisowa yayi yana mai sallama lokaci daya ya bashi hannu sukayi musabaha,bayansa Aliyu ke kallo yaga kota ina Azeema zata bullo ammh shuru,da kallon Tambayan Aliyu yake kallonsa kafin yace”Ah Ko Azeemar bataje mkrantar bane yau..?

  Sani mai KekenNapep yace”Shine Abunda yadauremin kai yallabai,ni dakaina na kaita mkranta yau da safe,ina kallo ta shige cikin haraban mkrantar,ammh Abun mamaki bayan antashesu naje daukota,ammh har duka Yan mkranta suka gama watsewa banganta ba,shine nazo nagani kodai tadawo gida da kanta ne..”Sororo Aliyu yayi kafin yace”How comes anya Azeema tadawo kuwa?bandai sani ba,buh bari na shiga na tambayi goggo naji wait for me..”Yafada da sauri yana fadawa gida,Tundaga nan yake kwalama goggo kira wacce ke daki ta zabga tagumi har lokacin dawowan Azeema yayi ammh shuru,da hanzari Ta fito,zaninta ahannun yana neman Faduwa tana fadin”Gani gadanga lafiya irin wannan kira haka? tafada cikin tashin Hankali

Gabanta yaci burki yana fadin”Goggo ina Azeema..”? Fuskar damuwa ta bayyana ga goggo tace”Nima yanzu nake Shirin kiranka awaya Tundazu lokacin dawowarta yawuce ammh haryanzu shuru bata dawo ba,bakana da nombar mai Keken ba kirashi muji kowani aiki ne ya tsaidashi baije ya daukota ba.”Kansa ya dafe yana fadin”Kash..Wayyo To ai goggo ga Sanin chan,yace shima yaje mkrantar su Azeemar ammh har kowa ya watse bai ganta ba..”Salati goggo ta fara tana fadin”Na shiga uku ni Suwaiba.,To yanzu ina yarinyar tashiga kuma ba dabi”arta bane biye biye,toh ina ma ta sani balle taje..”

  kallon goggo yayi kafin yace”Goggo kishiga gidansu kigani kila ta biyo yar”uwarta sun dawo tare..”Da hanzari goggo tace”Eh kila ta yuyu haka din ne,bari naje na gani..”Tafada Tana Fadawa daki,Hijabi ta sanyo ta fice da Sauri ta bar Aliyu na Dafe kansa baisan dalili ba yaji hankalinsa yatashi,goggo na fita taci karo da Dan adaidaita,yana ganinta yahau Fadin”Ah Hajiya an ganta ne..? ko kallonsa Goggo batayi ta fada gidansu Azeema tana zabga sallama ko izini ba”a bata ba,ta sakai cikin Filin tsakar gidan,nan ta iske Azeeza da Inna Ramatu suna zaune kan Tabarma suna cin dankali,suka ga goggo ta fado kai tsaye inna Ramatu ne takalli goggo tana cewa”A”a suwaiba lafiya naga kin fadomana gida,  tamkar wani ya biyoki daga waje..”

  hararanta goggo tayi kafin tace”Azeeza ina Azeema..”?Tun dazu bata dawo gida ba,ko kin ganta yau amkaranta..”?Tafada tana maida kallonta kan Azeeza,Jin haka yasa Ran Azeeza yayi fes Tsarinta yana tafiya kan tsari,Mikewa tayi tana fadin”wlh tallahi goggo yau kaf ban saka Adda Azeema a idona ba,dana ga banganta ba bayan antashi break,naje ajinsu ammh ban ganta ba,na tambayi yan ajinsu sukace batazo ba yau,dama taje mkranta ne yau..? Azeeza ta fada cike da makirci,baya goggo taja tana fadin”Armmm.,Bakomai..”Tana fadin haka tafice da sauri Inna Ramatu ta bita da kallo kafin ta maida kallonta kan Azeeza wacce ke mirmishi mai Fitar da amon Sauti Tabota inna tayi tana fadin”Ke nifa nashiga rudu mai wannan uwar sojan mara mutumci,take son Fada..”

  Kallonta Azeeza tayi kafin tace”Wai bakiji metake fadi bane Adda Azeema ne Tafita da niyyar zuwa mkranta,shine ta sanfe wani wajen haryanzu bata dawo ba…”Baki inna Ramatu ta kama tana fadin”Au hakane eh lalle yanzu na Fahimta,toh ammh ina Azeema zata,bata da dabi”ar yawon banza kuma fa..”Wani kallo Azeeza ta watsama inna kafin ta kama hanyar daki tana fadin”Ada kika sani,ammh yanzu baki  da tabbas akan hakan..”Tana gama fadin haka ta shige daki tana kunshe dariyan Farinciki.

   Goggo ko tana Ficewa sukaji karo da Gadanga awaje Shida sani mai Adaidaita,da hanzari Aliyu ya karisa ga goggo yana fadin”goggo an ganta.”girgiza kai Goggo tayi tana fadin”tace duk yau bata ganta amkaranta ba,tamaje har ajinsu bata gantaba, data tambaya akace batazo mkranta ba yau..”dan yatsansa Aliyu ya sanya abaki ya ciza kafin ya waiga yana fadin”Ka tabbata Sani ka ga Shigan Azeema mkrata yau da safe..”? Rantsuwa sani ya kwaso yana fadin”Wallahi tallahi yallabai da idona naga Shiganta mkranta na Rantse harga Allah…”jin haka yasa Aliyu yin gaba yana fadin”Shiga mutafi chan mkrantan nasu,goggo ki koma gida,komai ake ciki zamu mgana ta waya..”Yafada yana Shiga Adaidaitan,Da hanzari sani ya zagaya ya shiga ya tada adaidaitan suka fice daga layin,goggo na tsaye Abun duniya ya isheta.

  Suna Zuwa mkrantan kai tsaye office din principle,din mkrantan suka nufa,nan suka samu principle din bayanan ammh Vice dinsa na nan,Nan Aliyu yayimai bayanin Abunda ke tafe dashi,Cikakken Sunan Azeema ya tambaya shikuma ya fadamai,report book ya shiga dubawa nan yaga sunanta ita da Azeeza amtsayin wacce ta rakota tabada report din domin Abunda Azeeza bata sani ba kowani report sai an Rubuta kuma in bata manta ba,dukkansu sai da suka fadi sunansu da class din da kowannensu yake,Nan vice principle din ke fadama Aliyu cewa da misalin karfe 8:00am na safe sukazo suka shigar da report din, Azeema lawal bature zata koma gida sakamakon bata da lafiya wacce kuma tabada report din Sunanta Azeeza lawal bature,Aliyu bai tsaya mamaki ba,sai ya tuna Abunda goggo tace Azeezar tace,kenan duk inda Azeema Take Tana da masaniya duk Abunda yafaru da hanzari yayi sallama da vice principle  din yafice saboda bacin rai yana zuwa bakin get din mkrantan,yasaka hannu ya tsaida dan Achaba,yana hawa yakalli sani mai adaidaita yana fadin”kaje kawai mungode..” daga haka yace ma mai mashin yaja suje,Sani yabishi da kallon mamaki ganin yadda yake wani huci kamar mayunwacin zaki saboda Fushi.

Ad

Ad

_____

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button