ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 11 to 20

 “””Karfe 3;00pm na yammah motarsu ta saka kanta cikin kayataccen barikin na sojoji,wanda bariki ne,wanda ke kula da barikokin kaduna,kano,katsina zamfara da Sokoto Shine babban bariki na North a west wato *1 DIVISION NIGERIA ARMY KADUNA*…

     Agaban wasu manyan gidaje daga chan yammah daga cikin barikin suka faka motarsu gidajene jere kamar estate saboda yawansu kuma dukkansu iri dayane komai da komai nasu illah nombobi ne kadai ya rabasu kowani gida dan madaidaicin flat ne mai kyau da tsari dauke da babban Falo da 3 bedroom kowanne da tiolet aciki sai babban kichen dake wajen falo,sai wajen Dining,daga waje Componud kowanne akwai parking space da dan Fili na motsa jiki ko Buga ball,tsakanin kowani apartment akwai dan tazara kadan bada yawa ba,kowani soja an makala masa sunansa da Nombarsa acikin babban kofar part dinshi,ina daga kai naga an saka da manyan baki cikin wani dan anani *CAPTAIN A.A TAMBARI BUZU* naga ansa kenan wannan gidan mallakinsa ne.

    Suna gama Parking Tsirarrun Sojojin dake wayo aharabar wajen da hanzari suka kariso suna rige rigen bude musu mota,lokaci daya suna kame musu ko kallonsu Aliyu baiyi ba,jabir ne,ya daga musu hannu bayan ya nuna musu bayan motar inda kayansu yake,da hanzari suka bude suka kwashi jakukkunansu da hannu Aliyu ya nuna su,kawai sai naga sun rabu biyu,wasu sun nufi Apartment din Aliyu,wasu kuma Sun nufi apartment din dake kusa dana Aliyu dauke da jakar Jabir alamun nan ne barayinsa,Aliyu bayansu yabi duka hannuwansa cikin aljuhun wondonsa yana wata tafiyan takama bayanshi jabir yabi jin alamun tafiya yasa Aliyu ya waigo yana bin Jabir da wani Suprise look,shiko jabir gyara tsayuwa yayi yana fadin”Muje ko..”Akaikaice Aliyu yanuna shi da hannu yana fadin”to go where? dallah mallam kama gabanka,nan din gidanka ne..”? Wata dariya jabir yayi yana fadin”Nifa taimakonka zanyi,naga baka da lafiya,kana cikin damuwa kana bukatar wani akusa dakai…”Rike baki Aliyu yayi yana kallon jabir kafin yadan ware idonsa yana fadin”Don mai garinku nina fadamaka ina cikin damuwa? comon mallam kakama gabanki,yasin karka shigomin gida Ngd da Taimakon..”,yafada yana Wucesa da sauri yar dariya jabir yayi kafin ya juya yana fadin”Kai kasani ga damuwa Aranka,ammh tsinannan iskancinka yasa kana wani basarwa chan ta matse maka gara kawai..”

     “Aliyu bai waigo ba,yace”Ta matse maka dai azariyan wandonka banza Dan saka ido kawai..”Yafada daidai lokacin daya dauko dan makulli daga aljihun wandonsa ya zura akofar yana bude kofar falon,Sojan dake biye dashi daga bakin kofa ya tsaidashi ya karbi jakarsa saramai, yayi ammh Aliyu ko daga kai baiyi ba,sai ma shigewa ciki dayayi ya banko kofa,Sojan bai damu,domin duk wani Soja dake barikin yasan miskilancin Aliyu gadanga,shiyasa babu wanda ma ya damu dashi…

Yana Shiga falon bai tsaya ba,ya isa ga bedroom din,jefa jakarsa yayi kan gadon daya mamaye dakin yayi,kafin yafara tube takalmin kafansa,zuwa duka kayan jikinsa,boxers kadai yabari ya fada bedroom din,bai dade ba ya fito kugunsa daure da wani karamin Towel,yana Fitowa wayarsa tafara neman agaji ta wutsiyar ido ya hango mai kira *Swt Ni”ima* yagani wani dogon tsaki yaja yanajin wani daci aransa,wayar bata gama Ringing ba,ya yanke kiran bayan ya shiga ya sakata cikin blacklist,dama kawarta tun safe ya sakata,saboda bayason Takura sam,Shi yanzuma duk Abunda zai Tunamai da wata Ni”ima ma haushi kamasa yake,Da karamin Towel din ya fice zuwa wajen compound din Flask din da goggo tabasu da kulan Fanken ya duba bai gani ba,Rike kugu yayi yana hangen Apartment din Jabir saboda yasan shi ya dauka,kai gayen nan Dan mtsala ne yanzu yajamai sai ya dafa indomie Tunda bazai sake fita ba,ya dade tsaye yana Tunanin wulakancin dazaima gayen chan kafin yakoma ciki,wani guntun wando ya sanya 3quater ko riga bai dashi Ya fada katon kichen din Gas ya kunna ya dora wata karamar Tukunya,ya zuba Ruwa,lokaci daya yabude wani drower ya dauko indomie cherry guda biyu ya farka ya saka,bai fita daga kichen din ba,saima jawo wani Stool da yayi ya zauna yana ajiyar zuciya kamar wanda yayi wani auki,yunwa yakeji bai wani tsaya indomie ta tsotseba,ya sauketa da ruwa ruwa ya juyeta cikin Filet ya bude fridge ya dauko lemon cway ya fito,bisa daya daga cikin kujerun falon ya yada zangon yana daukan Remot bayan ya kunnah Talabijin din,kallon falon yake,yana ganin yadda yayi kura,karamin tsaki yaja aransa yana fadin”yasin ba sharan da zanyi am tired..”Yafada kamar wanda akasashi Dole,hakanan ya shiga Tura indomie har ya kusa cinyewa kafin ya ture filet din ya mike,ya karishe shanye Cway din,bedroom yakoma ya fada bisa gado,yana damke hannusa bisa kirji bayan ya kulle idanunsa,yashiga Tunanin Abunda ya faru daga jiya zuwa shekaranjiya,yana ta mamakin kansa,Ahaka barci ya kwashesa…

    ***********

_Gombe_

  Tun karfe 4:00Am na Asuba Azeema ke tashi sakamakon tasan yau monday Sunada mkranta,kuma matukar bata tsaya tagama duka aiyukanta ba inna bazata taba barinta tatafi mkrantanba,sai ta kammallah komai koda zataje amakare ne,Shiyasa take tashi da wuri tagama duk Abunda takeyi kafin lokaci ya kuremata Tunda Azeeza dama yar gatace bata changal agidan,sai dai taci ta kwanta da Rashin kunya kadai ta iya.

Kafin 7:49am ta kammallah duk Abunda zatayi tayi wanka ta sanya Riga da wando da hijabi kalan Uniform din mkrantan,Madafi takoma ta dibe Tuwonta tazo tazauna tanaci,Lokaci bayan lokaci tana kallon Azeeza take kwance tana jin shesshekan datake alamar kuka takeyi,Gum Azeema tayi Domin tun dazu take mata mgana tatashi tayi sallar tayi Shirin mkranta ammh Azeeza tamata banza,ganin bazata iya barinta haka ba yasa bayan tagama cin Dumamen Tuwonta tamaida kwanon madafi tazo ta wanke hannu takoma dakin tana fadin”Azeeza keko wani irin barci ne,haka takwas fa takusa ammh baki tashi ba,ni harna Shirya zan Wuce mkranta..”Azafafe Azeeza ta tadago kanta daga kwance idanunta sunyi jawur Fuskarta ta kumbura Saboda kuka tace”Wai miye Ruwanki da Rayuwatace Adda Azeema? kin takuramin kin isheni,baza”ayi sallar ba,in kike da aljannar inna tashi shiga ki tare ni karna samu shiga..”Tafada tana mata wani banzan kallo,Azeema baya taja tana daukan jakarta wacce ta kasance ta hannu ne tana fadin”Allah ya baki hakuri…”,Tafada cikin sanyin murya kafin ta dumfari kofar Fita,karaf inna Ramatu ta dago labulen dakin tana fadin”Kai Ni wannan bala”in ya isheni wlh,ke dai in da diyar wani Shehi ne,da anga kinibibi,to sai kuma kikayi dace ke diyar mallam lawal ne mai Saida kayan gwari,ina Ruwanki da yata,bakiga bata da lafiya bq ne,in tatashi Uwarki zatayi miki..”Tafada tana zabgamata harara,dukar dakai Azeema tayi kafin tadan Rankwafa tana fadin”Ina kwana inna…”Ko kallonta inna batayi ba,saima karisawa datayi cikin dakin tana fadin”Azeeza tashi,ya jikin ki? take fada tana tarairayota jikinta,Ko kallonsu Azeema batayi ba,ta fice kofar dakin inna ta tsaya tana sallama,mallam lawal dake ciki ya amsa bayan yabata izinin Shigowa,Shiga tayi bayan tacire sandal dinta mallam lawal dake kan gadon mai Rumfa ya sauko daidai lokacin da Azeema ta duka tana fadin”Ina kwana baba..”Ya amsa yana fadin”Lafiya lau diyar albarka,har anyi Shirin mkrantar..? ta amsa da cewa “Eh baba..”aljihunsa ya laluba ya fito da Naira hamsin ya mikamata yana fadin”Kin mkara ki hau mashi ko Keken napep,saura ko ruwa kyasha amkranta..”Noke hannu tayi tana mikewa tace”a”a Baba kabarshi Ban mkraba yanzu zan isa insha Allahu,ruwa kuma akwai fa famfo baba Amkrantar..”Tafada tana juya,Sunanta yakira ta waigo tana amswa mikata yayi yana fadin”Karbi diyar albarka bansanki da gaddama ba..”Hannu ta sanya zata karba taji an warje kudin bayan an Dunguremata kai,Inna Ramatu ne tsaye take kallonsu tana hararansu kan tace”ehe sannu mai diya,ammh yanzu kagama cemin baka da kudi,ammh dayake kan wannan banzar yarinyar ne,ai ka ciro ka bata,kuma dakake kokarin bata kudin ka manta kayi Auren jari da ita,Inashi mijin nata da bai bata ba..”Tafada cikin gatsine,Kallonta mallam lawal yayi yana fadin”Wai ke Ramatu meke damunki ne,koda tana da miji ni ba Mahaifinta bane,bata da hakki akaina ne? “Harzukomai tayi Tana fadin”Bata da hakkin akanka,don yanzu ba”a karkashin ikonka take ba,Azeeza ce ke karkashinka yanzu sonkai ne yamaka yawa shiyaasa baka ganin haka,uhm ayi mugani indai mune muna zaune zamu gani,kowa yana gudun hada zuru”a da bara gurbi ammh kai ka Rumguma yaron da”akace Rikakken Dan”iskane bai da aiki sai tara karuwai Achan kaduna..”Salati mallam ya saka yana fadin”Ramatu ina kika samu wannan lbrin kuma,oh ni lawal,yanzu baki Tsoron Allah yayi miki hisabi akan kazafin dakikayi masa..”Babu kazafi illah gaskiya in ba iskanci ba,ubansa yakeyi achan sai yadau lokaci bai zo gida ba,…”Azeema batagama ji ba,ta fice tana kwallah ko waiwaye batayi ba,ta fice daga gidan zuciyarta na kuna,Hanyarta ta dumfara kawai tana tafe tana lissafin zuci,Kamar ta biya gidan Baba ade Ammh kuma sai taga ta mkra sai tace bari sai ta dawo ta biya,Duk saurinta sai da Seniors suka tsaida ta tayi piciking kafin ta isa ajinsu duk wanda yaga Fuskarta sai ya Fahimci tana cikin damuwa kawai boyewa takeyi.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *


The reCAPTCHA verification period has expired. Please reload the page.

Back to top button