ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 21 to 30

*NOT EDITED*????

         *Chapter 21*

   “”Bai isa Shashen mai martaba ba sai zuwa dare bayan an idar da sallar Issha”i lokacin angama hidimar Fada Sarki ya Shiga cikin gida wajen iyalansa,Lokacin da Umar ya tarar dashi yana kishingide cikin kayatattacen Falonsa wanda yaji kayan alatun more rayuwa,Tuffa ne ahannunsa yana Ci,gefe daya kuma yana duba wani littafin Iziya,jikinsa Sanye da riga da wando,irin na gidan Sarautu,Yana ganin Umar yatashi daga kishingiden yana mikamai hannu Karisawa yayi yana mai mikamai hannun yana fadin”Barka da hutawa Ranka yadade…”.

  Kusa dashi ya zaunar dashi yana dafa kafadansa yace”Yauwa Umar Sanda,ya aiyukan,nasamu lbrin dawowarka Tundazu toh lokaci muna fada kasan Sha”anin mulki sai da taka Tsantsan,nima dabakazo ba,yanzu nake Shirin zuwa shashen naka..”mirmishi Umar ya saki yana kallon Fuskar mahaifinsa mafi soyuwa gareshi,kafin yace”Eh Abbah Tun dazu na Shigo nima Ban leka Fada ba,saboda gajiya ammh kasan kowani hali nake ciki Dole nazo har shashenka na isheka..”girgiza kafadansa yayi yana fadin”Hakan na dakyau,ya wajen aikin naka Fata dai komai lafiya.

Ajiyar Zuciya Umar ya sauke kafin yace”Lafiya ba lafiya ba Abbah…”kallonsa yayi idanunsa sanye da Wani Farin medicated glass mai karama Mutum karfin gani,kafin yace”Lafiya meyafaru Umar zaki..”?Kada kai yayi yana Fadin”Wlh Abbah mganar hadin gwiwar nan ne Kasar Nageria ta nemi gwannatin kasarmu data hada hannu Suyi tare,Toh acikin Sojojin, daza”a Tura Nigeria Abbah harda tawagarmu kuma nine shugaban Tawagar..”Kallonsa yake har ya dire dan mirmishi yayi mai kafin ya maida kansa gefe yana kallon wani waje Mamaki yakama Umar a ladabce,yace”lafiya Abbah ko acikin mganata akwai Abunda yabata maka rai ne?..”girgiza kai kawai maimartaba yayi kafin ya saka hannu ya zare gilashin dake idonsa kafin yace.

  “Ko daya Bata batamin rai ba,saima Tuno min da wani gibi dana kasa cikewa,karka damu Umar Allah natare dakai kuma addu”ar iyaye na bibiyanka,insha Allahu zakuje lafiya ku dawo cikin Nasara..”kai tsaye Umar yace”Ammh Abbah ka taba zuwa Nageria ne,wai ina Nufin koda yawan Ran gadin gidan Sarauta ne?” Kallonsa yake kur kafin ya kauda kai yayi Shuru sai zuwa chan yace”Na taba Rayuwa A Nageria bama zuwa ba Umar..”Da mamaki Umar ke kallon mai martaba kafin ya washe baki yace”Toh Abbah wani yanki ka zauna..? Yanayin Fuskarsa sai ta chanza Jikinsa yayi sanyi yayi Shuru baiyi mgana ba,ganin haka yasa Umar Saurin cewa”Afuwan Ranka ya dade bansan Tambayata zata bata maka rai ba Allah huci Zuciyarka..”bai yi mgana ba sai ma mikewa dayayi yazura takalminsa irin na gidan Sarauta hanyar wani kofa ya nufa sai da yakai kofar dakin kafin ya harde duka hannuwansa ta baya ya waigo yana fadin”Baka Batamin ba Umar,tambayarkace ban da amsarta domin nikaina Bansan awani yanki na rayu ba balle har na dora da wani Abun,Abu daya na sani inaji ajikina cewa ada achan baya nayi Rayuwa da wasu mutane,wanda Ahalin yanzu suke bukata,ammh kuma Allah ya boyemin Abun,addu”a zaka taya mahaifinka Allah ya bayyanar da Duhu yazama haske..”Yana gama fadar haka ya Shige kofar da hanzari.

Duk da Umar bai gane ina mahaifinsa ya dosa ba,ammh yasani koma miye shi Toh Tabbas,yana da matukar amfani sai yasamu kanshi da addu”ar Allah ya bayyana koma miyeshi,bai wani jima ba ya tashi dauke da Tuffa guda daya ahannunshi,yana Shirin Ficewa sai ga gimbiya Razeenah cikin alkyabbanta zata Shigo sukaci karo,baya yaja yadan rankwafa yana fadin”Barka da Fitowa Ummah..”Mirmishi ta saki tana fadin”Yauwa Umarur Faruqu saukan yaushe ba lbri,dazu kannenka keta zencenka..”kai ya sosa yana fadin!Dazu ne Ummah,agajiye nadawo Shiyasa ban Shigo ba,Zan Shiga da Safe mu gaisa da kiddo’s dina..”Gaba tayi tana fadin!Ayyah..Yakamata..”Ficewa yayi yana fadin”Afito lafiya Ummah..”Ta amsa Da Allah ya sa Umar.

    ____________________

_Gombe_

   Su goggo sun sauka gida lafiya,goggo akafara Saukewa kafin awuce da Baba Ade gidanta cike da kayan arzikinta ta sanadin Azeema domin kawu sai da yabata 20k dakyar ma ta amsa,sai kayan Abinci wanda yabasu ita da goggo harda na mallam lawal,wanda dama akidane Duk wata in zaiyima goggo sako,toh harda nashi aciki yamaida Abun Nauyi ne wanda ya rataya awuyanshi don ko komai Mallam Lawal nada matukar Tasiri ga rayuwar kanwarshi Suwaiba da Aliyu,balle yanzu da Aliyu ke Auren diyarsa.

Sai washegari  goggo ta Shiga gidansu Azeema ta kaima mallam lawal sakon kudinshi da kayan Abincin Da kawu yabada abashi,haka yaketa zubamata godiya kamar yayimata kuka,domin kudin sunzo akan gabane,kasuwa taja baya gashi babu kudi ahannunsa,toh ga budi daga Allah,Nan yake tambayar Azeema aiko goggo ta tankwashe kafa tana bashi lbrin Azeema na kaduna in ma yaganta bazai ganeta ba,Yaji dadi Sosai yayita musu addu”an zaman lafiya,inna Ramatu kuwa dakyar ta iya bude baki ta amsa gaisuwan Goggo itako ko ajikinta bata damu ba,Tadade suna hira da mallam lawal kafin tayimai sallama zata tafi dago kan dazatayi taci karo da Azeeza Inna Ramatu ta rikota zasu bayi,Goggo ta tsorata da ganin yadda Azeeza ta dawo,saboda yadda ta rame duk kibar nan dakuka sani bata,tayi baki tarame fuskarta tayi wani iri,Bakinta duk ya bushe,dakyar take Tafiya,har suka Shiga bayin,Goggo na binsu da kallo sai da suka Shigene kana goggo ta maida kallonta kan Mallam lawal tana Fadin

  “Mallam lawal,nace meya samu Azeeza ne,naga duk ta kare..? kada kai yayi kafin yace!Wlh bansani ba Suwaiba tun Ranar da kuka tafi ta kwanta ciwo,daga zazzabi shikenan jiki yaki dadi,toh Rashin kudi ne yasa Ita uwar tata bata kaita asibiti ba,ammh Tunda yanzu sun samu gobe sai Su Shirya su Tafi..”Gyada kai goggo tayi kafin tace”ikon Allah,anya ko Tana cin Abinci..”?Girgiza kai Mallam lawal yayi kafin yace!gaskiya bata wani ci,koni sai na mata jan ido take iya ci kadan,bata da aiki sai kuka nayi Tambayan Duniyarnan tafadamun meke damunta taki  mgana,ta tambayi mahaifiyarta itama tacemin bata sani ba..”kada kai kawai Goggo tayi tana fadin!Allah Shi kyauta..Allah kuma yayayemata Abunda ke damunta..”Da Amin ya amsa,kafin Shima yamike har waje ya rakata yanata mata godiya.

   Koda Su Azeeza suka Fito daga bayi basu samu goggo ba,waje Inna Ramatu ta zaunar da Azeeza inda Mallam lawal ya tashi,Kasa zama tayi saboda bata da karfin jiki,komawa tayi takwanta tana tari,inna na mata sannu,dagowa tayi tana fadin”Inna Da Azeemar aka dawo..?”tafada cikin alamun ciwo,Tsaki Inna taja kafin tace”Mtsewww..Bansani mara zuciya koda ita akadawo ubanki zatayi miki,duk uban wulakancin dasukayi miki,aiko yacu ki kama kanki,shiko shegen yaron nan mara asali,wlh ko bayan Ran Azeema ban amince ki aure shi ba..”tafada cikin kakkausan murya kafin ta wucewarta madafi tana ta fada tana zagin Azeezar hade da Azeemar lokaci daya tana kuma tsinema goggo don tace ita tazo anguwansu ta haifan musu dan Shege yazamantomata bala”i.

Azeeza na kwance tana fitar da hawayen bakin ciki,Tunda yaya captain ya tafi da Azeema kaduna ta kwanta wannan ciwon saboda bakinciki da zafin zuciya,akullum kwanan Duniya in dare yayi bata iya barci saboda Shedan na haskomata Azeema da yaya captain kwance agado daya suna gudanar da wata rayuwa mai tsayawa arai,Zafin kishi baya barinta tayi barci ta dinga kuka kenan tana Tsinema Azeema aranta,kuma wata tsanarta na kara girma aranta,domin itace ta Shiga tsakaninta da masoyinta,wanda duk kwanan duniya dashi take kwana take tashi,sonshi bai ragu aranta ba,saima karuwa dayake.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button