ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 21 to 30

jin Shuru yasa ya Nufi bedroom kai tsaye yana kiran Sunanta,Itama kuma Azeema tana kokarin Fitowa daga Tiolet din taji yaya captain na kiranta,tana gyara zaman karamin Towel din dake jikinta ta fada da karfi”Am here Yaya captain..”Tafada tana Rufe baki Tuna abayi take tana bude kofar Tiolet din yayi dai dai da bude kofar bedroom din da Aliyu yayi,ita Fuskarta na Kallon kofar Shigowa ne,tana sakarma Gadanga mirmishi shiko yana Shigowa yayi 4eyes da wani gardi kwance kan gadonsu na Sunnah ba riga,ga rigar da yafita yabar Azeema dashi ajikinsa yana shinshinawa,gabadaya Aliyu jinin jikinsa ne yaji ya daskare,saboda tsoro da dimautuwa,Hannu yadaga yana nuna wajen,bakinsa na rawa Jijiyoyinsa kansa Sun mike saboda bacin rai.

Ganin haka yasa Azeema maida kallonta inda yake Nunawa Abunda tagani ne yakusa sawa towel dake jikinta ya subuce ya fadi,baya taja tadafe hannu akirji Tana zaro ido lokaci daya take fadin”innalillahi wa’inna Alaihirraju’un…”Take Fada jikinta narawa,shiko ganin yadda sukayi yasa ya kalli Azeema yana fadin”Bbby har kin Fito wanka,Toh wlh kizo na karayi don kinsan bai isheni ba..”Yafada yana Rumgume Filo cike da makirci ganin yadda tayi ne tana Rawan jiki,yasa yakalli barayin inda Aliyu yake,da hanzari ya mike yana raruman rigansa yana bayyana tashin hankalinsa,Ammh sai ya kalli Azeema yace”Baby ya haka?Kafin na yarda zanzo sai fa dakikacemin mijin ki bayanan,ammh yanzu ya na ganshi..”Haurowa gadon yayi zai Fita yana bin bango,sai da yazo gab kana Aliyu yayi kukan kura ya damkoshi ya durkusheshi akasa baiyi wata wata ba yafara bashi kulli Afuska,Jikinsa na rawa saboda tashin hankali,kokarin Cire masks din Fuskarsa yake,ammh yaki bari,ammh saboda yafisa karfi,sai da yasamu nasaran ciremai Fuskarsa ya bayyana shakesa Aliyu yayi yana fadin”I will kill u…” yake fada yana zaro ido,ganin yana neman kasheshine,yasanya kafarshi ya tokaraimai gaba da karfi,wanda ya saka dole Aliyu ya sakeshi ya rike gabanshi yana Runtse ido,shi yabashi damar tashi ya Fita da gudu,koda Aliyu yayi yunkurin binsa sai yakasa da hanzari ya Fito da waya yakira Jabir,jabir na dauka muryansa A haukace ya furta..”Jabir ka bada Umarnin Arufe kofofin barikin nan Right now..”gaban Jabir ya fadi da hanzari yace”Aliyu lafiya naji muryanka haka.?.”Tsawa ya dakamai yana fadin”Kayi Abunda nace mallam..”yana gama Fadar haka ya kashe yana kokarin mikewa.

Itako Azeema wajen ta durkushe tana gunjin kuka hannunta bisa kanta,tana kiran sunan Allah,Kukantane yasa Aliyu ya dago yana kallonta da jajayen idanunsa,Yana jin kamar ya tashi yayimata dukan mutuwa ammh bazai iya ba,komawa yayi ya zauna yana cije baki kafin yace” Azeeeemmmmma….”Da karfi sai da ta Razana baya taja tana Rufe baki saboda kuka” kai ya sadda yana fadin”Dame na rageki da har zaki kawomin kato..?Girgizamai kai takeyi tana so tayi mgana ammh kuka yaci karfinta,Rarrafowa tafarayi zuwa gabanshi tana wani irin kuka tana girgiza kai,ganin haka yasa ya yunkura ya mike ya fice da hanzari yana dafe maransa,Bajewa anan Azeema tayi tana fadin” Hasbunallahu wani’imal wakil…”

  Koda Jabir ya Fito Tuni har gayen ya mike inda Muneera tabi Gudu kadan yayi sai gashi wajen motarta da hanzari ya bude ya Shiga,yana Shiga ya Fito da wayarsa ya turama Muneera Text da cewa” _Ki yi hanzari ki Fito aiki ya kammallah sai dai an kusa samun mtsala.._ Muneera dake Ta ribanta Sulaiman tana ganin Shigowar sako ta mike da hanzari tana kara wayan Akunne take fadin”hello mommy…Innalillahi ganin nan zuwa..”Tafada kafin ta kalli Sulaiman wanda ke kwance kan kujera yana kallonta tace”Zan Tafi yanzu Sistern mamata ta kirani wai Anyi Addmitting din mijinta a asibiti,kuma in banzo ba yanzu zata zargi wani Abu,Ammh dont worry zan dawo ko kazo mu hadu..”Tana gama fadar haka bata jira cewarsa ba ta fice da hanzari da gudu ta karisa wajen motar ta shiga tana kokarin bata Wuta ne take fadin”Garin yaya aka samu mtsala..? yana daga baya yace”karki damu mtsalan Fuskatace daya gani,kuma inaga don wannan ba wani damu..”zagi Muneera ta yanko tana fadin”are u mad,kasan waye Aliyu kuwa,he is very smart wlh,fuskarska kadai ta isheshi Shaida..”Take fada tana Figan Motar Jabir daya Fito daga gidansa dahanzari yana kokarin kiran waya motar tazo ta wucesa da gudu har sai da ya bita da kallo,kokafin yayi waya zuwa masu kula da Shige da Fice na barikin Tuni Muneera ta fice daga Barrak din Hankalinta atashe tana ta zazzagamai Masifa acikin mota Ammh hankalinta ya kwanta Tunda dai Aliyu ya ganshi dama su bukatansu kenan.

*Am Srry For d late update,wlh Jiya nayi busy ne*

*,Janafty…*

*ALIYU GADANGA..!*

_(The Story of Young Soldier man)_

*Wattpad:Janafnancy12*

_Mallakar:Janafty????_

*DEDICATED TO MY MOMMAH…HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*

_Special gift to my Real Dota RAHMA????Ladingo yar mutan Niger_

*Intelligent Writers Association*✏

_*Daukaka wata abace,Ta dan lokaci in ta Aureka Duniya zata sanka sosai kayi more porpular,and One Time u bcome Cele by Force ohoo????buh duk lokacin data sakeka kashima yafika Daraja,fans ma zasu daina zencen buk dinka balle akai ga zencenka kazama mar amfani garesu,Shiyasa ka/ki yi Fatan daukaka ko Shahara ita din kamar misalin Duniyace Rigar aroce,in tashiga wanchan gobe zata barkane ta shiga wata,…Shiyasa kazama mai aiki da Hankalinka,kayi komai don Allah sai gaka yama ka sakayyah da kyakyawan sakamako wanda bakayi Tsammani ba✌????????,…Assalamu Alaikum Janafy Fans*_

          *Chapter 24*

    “”Adaddafe Aliyu ya Fito yana Tafe yana rike maransa,Da Jabir ya cikaro akofar apartment dinshi,yana ganinshi ya isa gareshi yana fadin”Wai captain meyake Faruwa ne? lafiya kake dukewa ko baka da lafiya ne? ina ita Azeemar? yafada yana leka kofar Shiga Falon.

  Ture hannunsa,Aliyu yana fadin”Kasa Ayi bincike acikin barikin nan,Kada abari wani ya Shigo kuma kada wani yafita,da anga wata bakuwar Fuska Juz ku sanar dani..”Yafada yana cije baki saboda azaba Hannunsa Jabir ya riko yana fadin”Look Aliyu nifa ba iya abokinka bane don Allah kafadamin meke Faruwa? Wani Mutum ne ya Shigo,dan Fashi ne,ko ko dai aikoshi akayi ne? Aliyu ya dago kansa idanunsa sunyi jawur,baya Jabir yaja ganin yanayin Aliyun baicemai komai ba ya koma cikin gida,ya Rufo kofar,nan ya sulale yana Rike kansa da hannu daya,Saboda yadda yake saramai,So yake yayi kuka,ammh yakasa zuwa Tunda yazo duniya bayan Abunda ya Faru Ranar Daurin Aurenshi da Ni”ima,bai taba Shiga tashin hankali irin na yau ba,dame ya rage Azeema?wata zuciyar tacemai ammh taya zaka yarda Azeema zata gayyato wani kato,karka manta kai kasameta a burduwa fa? toh ammh in ba hakabane babu wanda keda alhakin Shigo da wani cikin bariki nan sai da wanda yasan wajen? Toh ammh ai ita Azeema batasan ko”ina a barikin nan ba,Toh waye ya Shigo dashi yanunamai gidana? wata zuciyartace waye kuwa banda Azeema babu wanda zai gayyatoshi sama da ita.

Kansa ya Dora bisa Tafin hannunsa yana Kiran Sunan Allah,Yana zaune wajen yasamu kiran Jabir kan yazo Security offoce yanzu,da hanzari ya mike Fuskarsa tayi ja,saboda Bacin rai,koda yaje chan Nan jabir ke mai bayanin bakin Fuskar da”aka samu duk ziyara suka kawoma danginsu nan ya Shiga nunamai mutanen da suka Shigo barikin aranar,ammh baiga Fuskar wanda yake nema ba,da hannu yayima Jabir alamu da a sallamesu kuma abude get kowa ya fita,Jabir ya Shiga damuwa ganin Halin da Aliyu ke ciki,ammh bai bashi Fuskar sanin meke Faruwa ba,don Aliyu yace bazai iya kallon idon Jabir yacemai Azeema yakama da wani acikin gidansa ba,Shiyasa yakasa mai mgana sai dai kawai ya kalleshi yana kada kai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button