ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 41 to 50 (The End)

Ad

_____

“Abinci mai Rai da lafiya suka girka,suka zuzzuba amanyan kololi,suka kai kowani Shashe,bayan sun Hada da lemuka da Ruwan gora,Su maimarta suna dai barayin gadanda suna cin nasu,ayayinda su gadanga suka hade Shida manyan Aminan nashi,Azeema ko dasu Zafira,sai su Anty mardiya da ita da Anty madina,goggo kuwa kunya takeji takasa ci,ummah mai babban daki ita kadai takecin nata,Ummah kuma ita da gimbiya Razeenah,Fasilatu kuwa babu wanda yabi ta kanta don Tunda ta Shiga ciki bata Fito ba,bayi da Fadawa ma ankai musu nasu barayinsu.

Ko kafin yammah tayi lbri ya Mamaye gari tako”ina mutane sai Shigowa suke suna ma goggo barka tare da Murna lokaci daya,wasu gulma ke kawosu,na ganin sarki da ake fadi,don wasu gani suke duk zence ne,aikuwa Maimartaba bai hana kowa ganinshi ba, yace abarsu suyi ta Shigowa yama Fi son hakan,da dare yayi maimartaba Sarkin gombe yaso Sarki Abdulnaseer yakoma masarauta,ammh yanunamai yafiso zamanshi anan,ko banza inda Suwaiba tayi rayuwa ne,ita da gudan jininsa,Shiko Aliyu yaso kebewa da Azeema ammh babu dama,yadda gidan yacika ne yasa sukayi musu sallama suka koma hotel din da suka kama ma Umar daki da safe suka kwana da Safe koda sukadawo suna cikin Shirinsu ne,don Maimartaba yace ayau din zasu kaduna sukuma biya zaria duk atare.

Inna Ramatu kunya da Nadama duk sun kamata,yau dai ga goggo data ke zagi tazama matar sarki,yau ga Aliyu datake yawon Fadin baida Asali Ashe dane,ga Sarki,da mallam lawal yadawo ya isketa tana kuka,ko kallo bata iaheshi ba,saima gyara kwanciya dayayi,yanaji tana kuka tana rokonsa wai ya roki Aliyu don Allah yasa baki Asaki Azeema wlh tayimai alqawarin bazata kara barinta ta aikata wani Abu makamancin Abunda ta aikata ba yana jinta yayi mata banza,saima Juyamata baya dayayi,Aransa yana Fadin bai yarda da Nadamar Ramatu ba haryanzu.

Koda su Aliyu suka dawo sun iske kowa ya Shirya, Nan suka iske Baba Ade tazo, yima goggo barka da kuma taya Aliyu Farincikin Saduwa da mahaifinsa,Hatta da goggo ba”a barta abaya ba ta Shirya tsab da ita,akwatun kayansu aka saka amota ita Azeema tunda zasu dan kwana biyu inji kawu,Su Aliyu ne zasu yi Tafiyar mota zuwa kaduna,su kuma sauran Jirgin maimartaba zasu bi,Gabadaya gidan aka Fito domin Tafiya su Aliyu tuni sun mika hanya Su maimartaba ne tsaye suna bankawana da su mallam lawal,sai ga inna Ramatu ta Fito daga gida da gudu ta zube gaban maimartaba tana kuka,mallam lawal kuwa yana ganinta yafara hararaart maimartaba ne ke tambayanta Meyake Faruwa tana kuka tana Fadamai kamun da Aliyu ya sanya akama Azeeza,Jinjina kai maimarta yayi kafin yace”Ash Abu baiyi kyau ba tashi tashi insha Allahu zan shashi yasa asake yau din nan..”Yake Fada yana kallon Kawu kafin yace”Bala don Allah kiramin Aliyu..”Kawu baiyi gaddama ba ya ciro waya ya kira Aliyu wanda ke gefen Jabir yana driving,Umar da Haisam suna bayan mota,da Azama ya daga kiran kawu yana Fadin”Hello kawu..”Bai yi mgana ba ya mikama Maimartaba wanda yace”Aliyu…”Yafada cikin dattako da mulki,saurin gyara zama yayi yana Fadin”Na”am Abbah,kun taho ne..? Bai bashi amsa ba yace”Yarinyar nan daka sa akama kanwar matarka kakira waya yanzu ka saka asaketa Umarni na baka ba Shawara..”gyada kai Aliyu yayi kafin yace”Angama Ranka ya dade..”Yana fada yana katse kiran,nan take yakira DSP MALEEK KABIR KUMO,sukayi mgana kafin ya bada Umarnin sakin Azeeza,nan sukayi mganar cewa bayan ya dawo yazo nan headquater su,akwai File din da zai cike nan sukayi sallama,jabir ne kawai yasan Abunda Ke Faruwa baiyi mgana ba,ko banza ai Ta horu Shegiyan.

Daganan Fadar maimartaba Sarkin gombe Suka wuce sai da sukayi sallama kafin su isa Airport,dama jirginsu na nan,Suka Shiga suka Lula sararin samaniya,Akaduna suka yada zango Tunkafin su iso mai girma gwanna Jahar kaduna * MALLAM NASIRU AHMED YAR RUFA’I yazo da kanshi ya ya tarbeshi Shida tawaganshi,Sai da sukaje gidan gwannati kafin su wuce gidan kawu,wanda ya kasance Aljannar Duniya nan kowa ya baje,don mamaken gida ne,mai Shashe har guda uku,kowanne ya gaji da haduwa,sai lokacin su Aliyu suka kariso suma,kafin isowasu Aliyu ya amsa waya tafi dari na yan”uwa da abokan Arzuka suna tambayanshi Shin Abunda suka gani gaskiya ne,da eh kadai yake amsawa,sai Barka mutane kemai da tayashi murna,daya gajima kashe wayaryi,Ko!ina na garin gombe jaridu suna ta yawo banda gidajen talabijin din da”akayita watsawa ana nuna Hoton Aliyun dana Maimartaba Sarki Abdulnaseer,Wanda jama”a dadama sunyi matukar mamaki,ciki harda da Ni”ima da iyayanta,mami tana hawaye tana kallon Cp Ahmed Sidi na Iya,wanda yayi Tsuru duk kunya ta kamasa,itako Ni”ima daki tayi dagudu Sauri tana kokarin kiran Muneera dataga ta kirata.

 Kunya duk takama Kwamishana,sai zare ido yake,Mirmishi Mami tayi tana Fadin”Ka gani ko? wannan Ranar nake jiyemaka yallabai,kabiyema Sharrin shedan da hudubar dan”uwanka gashi yau kaine,akunya yanzu duk amtsayin kaje kayi gaba da gaba da Sarki,wlh ko haka Allah yabarmu munga sakayyah,Tunda diyar tamu nan harynzu agabanmu kuma tace inba Aliyu bata ba Aure har Abada..”Tana gama Fadin haka tatashi Tafice ta barshi nan yana zufa,lalle al”amarin Allah Kenan,ashe yaron ma yawuce duk Tunaninsu ashe shi din Da ne ga Sarki yanzu haka Shidin yarima ne,Lalle ya tafka kuskure babba ma kuwa.

Ad

_____

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button