ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 21 to 30

    Tana Fitowa ta iske shi Shida Jabir suna Tsaye suna mgana,ammh dukkanasu Fuskokinsu ba Annuri,balle walwala,baya Taja ta Tsaya tana sadda kanta kasa,Jabir yana ganin ta Fito yatako zuwa gabanta yafadin”Azeema ki taimakeni ki Fadamin Abunda ke Faruwa,tunda shi yaki fadamin,Tun jiya na lura wani abu na Faruwa ammh yamin Shuru yanzu kuma gashi kina kwashe kaya don Allah meya Faru..?”Dago idonta tayi dasuka chanza kala tana kallonsa,hawaye suna kwaranyomata,Wani Tsausayin Aliyu ya Tsirgamata,tana kallonsa tana Jin koba komai yayi mata karamci Tunda ya iya boye wannan Sirri,kasa mgana tayi sama jan kafanta datayi da gudu zuwa wajen motar ta bude gidan gaba Tashiga tana kuka mai cin rai,da ido Jabir ke kallonta yana mamakin wannan al”amari,yana kallo Aliyu yazo ya Rufe gidan kafin ya dawo har zai gotashi sai yadawo da baya ya dafa Jabir yana fadin’Am Srry Dude,bafa wani Abu bane wajen goggo zata koma ta Rubuta jarabawarsu ta candy,shine fa kaga munshiga damuwa,ammh babu wani abu ka kwantar da hankalinka yau insha Allahu zan dawo dazarar na kaita bazan tsaya ba..”Juyowa Jabir yayi yana Kallon Aliyu Shiko yaki yarda su hada ido,Girgiza kai kawai Jabir yayi kafin yace”Allah ya kiyaye hanya…” Daga haka kawai yakada kai ya Wuce,don kwata kwata bai yarda da kalaman Aliyu ba,ammh Tunda yana boyemai bazai kara neman yaji ba.

  Da Hanzari Aliyu ya isa ga motar ya Shiga bayan Sojan ya gama Dura kayan Azeema abayan motar,ganinta Zaune agidan gaba ta saka kanta tsakanin Cinyoyinta tana kuka yasa yayi gaggawar Fitowa yana fadin”Plz ki koma baya don Allah,i don”t want to see u in my Side again..”Tana jinsa tayi Saurin danne kukanta ta Fito da Sauri ta bude gidan baya tashiga tana boye Fuskarta cikin hijabi,Sai da ya bata lokaci kafin ya Shigo motar tana jnsa yana karanto addu”ar matafiya ya Daura Belt suka Sulala,basu bata lokaci ba Suka Fita daga cikin barikin kafin su dauki hanyar Gombe.

Karfe goma da wasu mintina Motar Aluyu tayi Parking akofar gidan na goggo,dayake lokacin yayi safe dayawa,shiyasa layin babu kowa,tsit kowa yatafi neman Halali,mataye kuma suna cikin gida,suna Dafa Abun sawa abaka,idonta biyu suka iso,don tunda Suka Fito daga kaduna take kuka,har suka iso gombe,da hanzari Ta bude murfin mota dauke da karamin kit dinta ta Fada gidan goggo da gudu tana kuka,shiko dama bai yi niyyar Shiga ba,waige waige yafarayi kafin ya Hango wani almajiri da hannu yayafitoshi yako zo da Sauri,Yana zuwa ya zura hannu a aljihu ya zaro dari biyar ya mikamai kafin yace”Don Allah kaya zaka Shiganmu dashi Cikin gidan nan..!Yafada yana numa mishi gidan,washe baki almajirin yashigayi yana godiya booth din Aliyu ya budemai yana Fito da akwatunan,shikuma ya fara dauka yana Shiga dashi cikin gidan.

  Goggo na zaune abakin Fomfo tana dauraye yan kayanta taji Fadowar mutum jikinta Ana kuka,ta tsorata ta Waigo da Hamzari tana fadin”Subhannallah waye haka..”?Tafada Tana Rikota Da Hanzari Azeema ta jaye hijabinta kanta tana kallon goggo,Baya goggo taja tana Fadin”Azeema…Azeema,mezan gani haka? keda waye kuka zo?Azeema na kuka tace”Goggo sunyi Nasaran Rabani da yaya captain,Sun rabamu goggo,sunyi Nasara akaina,wayyo Allah na Shiga uku..”Mikewa da hanzari goggo tayi tana Rawan jiki,bata kai ga yin mgana ba,almajiri yayi sallama yana Shigowa da kayan Azeema,da kallo Goggo ke binshi tana kallon Azeema lokaci daya kafin tace”Kedawa kikazo? Runtse ido Azeema tayi kafin tace”Shi ya kawoni yana waje..”Ai goggo ko mayafi bata sanya ba tayi waje da gudu,sai dai tana zuwa Motar Aliyu na barin wajen da hanzari goggo ta Kwalamai kira Tana fadin”Gadanga..”Kai Gadanga..”Ammh ina har Ya kule daga layin.

  

  Baya goggo taja tana dafe kai,Kafin takoma cikin gida,tana bin akwatun nan da almajirin yagama Shigowa dashi da ido,gefe daya kuma tana bin Azeema da kallo wacce tayi zaune akasa hannunta bisa kai tana kuka,duk kammaninta ya chanza bakin goggo na Nauyi tace”Wai Shin Azeema Abunda bangane ba gadanga ya sakeki ne ko yaya,nifa kunsani a cikin duhu don Allah bar kukan nan yimin bayani,naga gabadaya kayanki gasunan meya faru ne? Majina Azeema taja kafin tace”Bai Furta saki gareni ba goggo,ammh yace bazai iya cigaba da zama dani ba..?”

  kusa da ita goggo ta kariso tana fadin”Kam wani dalili..? nace kan wani dalili ko ya dauka aure Shiga jeji ne koko harbin bindigane..?Goggo tafada cikin bacin rai,bakinta Azeema ta dafe tana fadin”Wlh ban aikata ba goggo,Sharri ne,kuma bansan wanda ya aikatamin haka ba,kuma bansan dalilin kowaye ba.”Kuri goggo tamata da ido kafin ta sanya hannu ta rikota tana Fadin”Daina kuka Azeema,taso mu shiga daki,ki warwaremin komai,insha Allahu ina tare dake..”Tafada tana rikota suka Shiga daki,Kan kujera goggo ta zaunar da ita,kafin takoma ta rika jido akwatunan Azeema tana Shigowa dashi,gefe daya na zuciyarta tana cike da takaichin wulakancin da gadanga ya yayi mata,ai ko miye Azeema tayimai ya kirata awaya su tattauna ammh dayake wulakanci ya Shirya harda kawota da kanshi,kuma yajuya yayi Tafiyarshi,wlh zai zo ya sameta zai ya gane ita ba”a mata iskanci Ja’irin yaro kawai.

Share this

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button