ALIYU GADANGA 1-END

ALIYU GADANGA Page 21 to 30

  “La’ila ha”illallahu…”Inji Baba Ade “Muhammadan Rasulillahi..”Goggo ta karishe sunayi suna kama baki lokaci daya Suna kallon Azeeza suna mamakin yadda yarinyar kamar Azeeza ta iya hada wannan makirci ko wata uwar matan albarka,Shiko Aliyu ba Azeeza ce tabashi mamaki ba Azeema ce,ashe haka take da wauta saboda haushi baisan sadda ya matso kusa ba,ba tsammani kawai Sukaji ya wanke Azeema da maruka biyu,saboda azaba da zafin marin sai da ta kife bisa cinyar goggo,Dafe kuncinta Azeema tayi da duka hannunta biyu,domin tadainaji na tsawon wasu mintina,Baki ta bare zata fashe da kuka yayi saurin dakamata tsawa yana fadin”U stupit shout up ur Mouth,wlh kikamana kuka anan wajen yadda nakejin haushinki zan tattakakine anan wajan babu Ruwana,Tunda ke kwakwalwar Tumakai kikedashi koma na beraye ne bansani ba.

Baba ade tace”na ma Tamtabaru ne inaga,ai daka karama sakara mara wayau,ace ki zauna yarinya karama tana waasa da hankalinki Azeema,sai kace wata saunah,shekara biyar fa kikaba Azeeza,aiko yaci ace duk wasu dubarun Duniya da wani tuggu kingama sani..”Rumgumeta goggo tayi tana fadin!”Ya isa Baba,ai gashi gaskiya tayi halinta yanzu sai tafadamana meye dalilinta nayin hakan..? tafada tana kallon Azeza wacce idonta ke tsakar ka ba alamun nadama ko kadan atare da ita.

  Kusa da ita Aliyu ya matso yana fadin”good girl,gaskiya kin burge gaki da kananan Shekaru,ammh Tunaninki ya girmi wayonki,oya tell us mekike nema awajenmu,shin bayan Azeema kikeson gani kokuwa bayana..Ehen fadi munajinki,in ba sokike na tilastaki fadi ba..”Dan mirmishi Azeeza tayi kafin tace”Hmm,ai ko baka tambayeni ba yazama dole kowa yasan wannan gaskiya,Tafada tana haki kan taciga da cewa”Azeema ba itace tadace data mallake ba,nine nan…”Tafada tana nuna kanta,da mamaki goggo da baba Ade ke kallonta balle Azeema data bar jin zafin mari saboda kalaman Azeeza.,shiko Aliyu ko ajiknsa don dama Tuni hasashensa yabashi hakan

Cigaba tayi da Fadin”,Ni nafara Sonshi Tun bansan me ake kira da wata aba soyayyah ba,nasoshi Tun in yarinyata,da sonshi na tashi dakuma shi na girma ya gini ajikina,duk duniya babu wanda nakeso da kishin irin yaya captain Aduniya na tsani in ga wata mace na rabanshi koda mahafiyarshi ce,na tsaneki Adda Azeema wlh banta miki kallon yar!uwata ba sai makiyiyata,Ko shiga jikinki danayi duk don nacimma burina ne,na mallakan muradin Raina ne,ammh kash Duk wani gadan zare dana kullamiki sai ki tsallake,ta hanya yaya captain,wannan karon na dauka bazaki sha ba,sboda sanin yadda kwakwalrki take kamar dussa saboda Rashin lissafi,ammh sai gashi komai ya kwabe,ammh duk da hakan ban sare ba,don hankalina bazai taba kwanciya ba matukar igiyar ukun Aurenku da yaya captainn na Reto Akanki saboda haka kisani nan Duniya kece babban makiyiyata kuma ba wacce na tsani gani kamar ki…”Tafada tana Fashewa da kuka.

Daskarewa Goggo da Baba Ade sukayi itako Azeema tayimata zura kamar wacce aka sassaka,shiko Aliyu mirmishi yake saki kafin yataka zuwa gabanta ya tsugunnah yana fadin”Ban wani ji mugun mamaki ba,mamaki na daya na yadda duk kudin da baba da goggo suka kashe akanki asara kadai sukayi daga bokon har islamiyyah baki gane komai,in banda tsabar jahilci kina tsammanin zan saki Azeema ne,ke sa ma na saketa kina nufin zan Aureki ne,gaskiya ta wannan fannin kina da tunanin kifaye walh toh ai koda Azeema mutuwa tayi kuma matan Duniya kaf sun kare,wlh sai dai ki mutu na mutu ba aure bazan taba Aurenki ba,Domin nafi tsanarki Fiye da yadda na tsani mutuwata……!!!!!!”yafada cikin Tsawa da amo mai sauti kafin lokaci daya ya mike yana saka kafa ya sharbo kafafunta ta zube kasa yace!Kin san Allah kinci daraja daya,ke diyar mallam lawal ne mahaifi ga Azeema,da ba don haka ba,uhmm da yau kin gwammace kila da karatu,ammmh wannan yazama na karshe da zanyi miki kashedi kan Azeema,kifita daga hanyarta in kika kara shigowata gonata har na kamaki toh ki Rubuta sunanki Matatta,oya get out shegiya Tanayi da Fuska kamar mutuniyar arziki..” 

   Mikewa Tayi tana dariya lokaci daya hawaye suna zubomata tace”Ki Rubuta ki ijeye zan dawo gareki,ko ba yanzu ba..”Tana gama fadar haka ta fice da gudu goggo ta bita da fadin”Aniyar tabiki mai bakin halin insha Allahu sai sharrinki yakoma kanki..”Itako Baba Ade gabadaya lamarin ya tsorata tama kasa mgana,Azeema kuwa kuka takeyi sosai kamar wacce ta zauce,Yau ita yar”uwanta ke neman ganin bayanta,Tunda suka taso batataba jin zuciyarta tabata wani mugun nufi akan Azeeza,kullum tana kallonta amtsayin kanwarta mafi soyuwa gareta,ammh ashe ashe ita babu hakan Aranta,wani Abun takaichin ma wai mijinta take so oh duniya ina zaki damu ne,haka Baba Ade keta maimatawa kafin tace”Toh Sakarya ko nace Sauna kindaiji da kunnin ke ko? toh sai ki zama mutum kinaji kinagani itace makiyarki mai son ganin bayanki,in zaki mike ga kanki ki zama mai wayau da lura da abubuwa toh,in kuma zaki cigaba da sakarcin ne,Allah yabaki sa”a Kice zaki Sha wuya..”

  goggo dai lallashin Azeema kawai take Shiko Aliyu yana gafe ya harde hannunsa bisa kirji wayarsa dake Aljihun sa tadau Tsuwa,Fitowa da ita yayi sai yaga major Sadiq Amfani ne ke kiransa kila wani aikin ne ya taso hanyar waje yayi yana fadin”goggo kusameni awaje..”yana fadar haka yafice yana daga kiran da fadin”Hello Sir…”yes Sir…!Ok Sir..”!Thank U sir…”Yafada kafin ya yanke kiran yana Furzar da iskan bakinshi daidai lokacin da Goggo ta fito ita da Azeema Baba Ade na biye dasu suna sallama,mota yafada suma suka Shige baya sukayima Baba Ade sallama ya ba motar wuta sukabar kofar gidan

Amota Azeema ta ishesu da koke koke Ran Aliyu yabaci cikin Fushi yace”Dallah malama kima mutane Shuru in bahaka yanzu na tsaida motarnan na Fito dake nayi miki dukan tsiya kinga sai kiyi kukan mai dalili..”Yafada yana kyafci,Gum Azeema tayi da bakinta don bata manta zafin mari ba.

    Suna zuwa gida goggo da Azeema suka Shiga cikin gida,shiko gareji ya bude ya saka mota,kafin ya tadda su goggo Afalo tana kara bama Azeema baki tare da mata Nasiha,Daga bakin kofar dakin ya tsaya yana fadin”goggo Ta shirya kayanta gobe zan koma kaduna sai muwuce tare da ita don banga amfanin zamanta anan ba,banda karin Sakarci babu Abunda take koyo..”Jinjina kai goggo tayi tana fadin”Eh kayi Tunani,toh ammh wani hanzari ba gudu ya zencen mkrantarta kaga fa bata karisa ba..”Kai tsaye yace mata”Nagama tsara komai in lokacin biyan Jarabawar yan SS3 yayi zan biyamata in lokacin Rubuta jarabawar tayi sai na maidota ta Rubutu Allah barshi in Tafito sai na saman mata wata mkranta achan taciga dazuwa..” gyada kai goggo tayi kafin tace”Shawara mai kyau gadanga Allah yayi maka albarka gwara ka dauketa don ni Al”amarin na Azeeza da uwarta yafara bani tsoro..”Rausayar dakai kawai yayi ya fice zuwa shashensa Shima kayansa ya shiga Shiryawa saboda wannan karon zai dau lokaci don kiran da major yayimai kan Horar dawasu bataliyan kananan sojoji ne,kuma shi aka wakilta,Sai gashi kuma Abun yazomai Adaidai gwara yatafi da ita ta chanza enviroment kila ko ta chanza daga Azeema Wauta zuwa Azeema big girl.

_*Alhamdulillah Da Fari Da Allah zanyiwa godiyata,????Don Shiyatsaramin haka Arayuwata,Duniya sabo gani Acikinta????kuma na samu kula Anbani gata,Rayuwa ku kuka zamto  garkuwata????gani nazo zan nuna godiyata my Real Fans????i dedicated dis wonderfull songs to my real Fans if i say my Real Fans i mean for does people wit they hot hot commenting,Kai am so happy yesterday Saboda murna har nakasa maida reply,ammh nagani kuma duk ngade sosai Allah yabar zumunci da kauna na har abada…Love u to d back and moon Habibates*_????????❤????❣????????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button