AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 19-20

??19 and 20??

Afham bai jira dawowan Aneesah ba ya tashi ya tafi dakinshi cike da farin ciki, ji yake kaman damuwanshi taazo qarshe, Soyayyar Ameela ceh ke ratsa jikinshi tun daga sanda yaga hotanta Yanzunnan!

Wayarshi ya dauko ya shiga gallary, images hotan Ameelah ne farko ya tsaya yana qare matah kallo ko kadan baiso ya dauke ido daga kallonta

Tunanin kiranta yayi harya shiga contacts kuma saiya fasa ya fito ya bude datan shi ya shiga whatsapp yayi refreshing saiga numbrta ta fito, da sauri ya shiga numberta ganin wani hadadden Dp data daura yasha kyau cikin shigar atampa pink ta zubo bakin gashinta mai silbi da yasha gyara fuskarnan tata tasha makeup, naso ace kunganta, ba qaramin kyau Ameela tayi a selfie din ba!

Ya dauki mintina yana kallon pix din nata kafin ya lumshe ido ya bude yana murmushi wani irin farin ciki na ratsashi, shiga yayi zaiyi matah magana amma kuma cikin rashin sa’a bata online, tunani yayi bari yabar mata text idan tahau zata gani (brodza Abdul naga Ya dage yanaso ya hango rubutun da afham yake, daria ya bni nace let it be, mun karantah idan ya turama Ameelan)

Aneesah ce ta shigo dakin tatsaya tana kare masa kallo tana murmushi kafin tace “zan iya karantawa a fuskarka broz, lokaci daya qawatah Ameelah taa sace zuciyannka ko ba haka ba? Taku tafarayi harta karasa bakin gadon tazauna, ta kura masa tana murmushi tace “Kawai kafin in dawo harka tafi, koka mnta wurin zumudi kaa manta da keys dinka, ko duk son ameelar ne?” Daria yayi maicike da farinciki yace “kinsan yayanki sosae 6ter, da gaske ina son qawarki Ameelah!

Aneesah tace “gaskiya naji dadi sosae yayanah, daman Ameelah itace macen data dace dakai, domin nasan yayana yanason macce mai kyau da aji” takarasa maganar da zolaya

Ya shafi kyakkyawan sajenshi tare dayin murmushinshi me kayatarwa yace “shiyasa nakeji dake 6tanah! Kina saurin fahimtar abinda nakeso” murmushi aneesah tayi tamiki masa keys din sannan tatashi tafita takoma dakinta,

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button