AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 91 end

?? 90 ??

Via OHW???? w

Koda su abba suka karaso asibitin har likitoci sun karbesa sunshiga bashi taimakon gaggawa,

Momy tana zaune su abba suka shigo, tana ganinsa ta mike tsaye cike da masifa tafara magana ” meya kawoka, katafi kabarni dashi nizan iya kula da yarona, bazan bar ruywarsa ta lalace ba” abba ya karaso gurinta jikinsa a sanyaye, ya Bude baki zaiyi kenan likita yafito, momy tabar gurin abba tayi saurin karasawa gurin likita,

Likitan yace “hajiya saidai kuyi hkr, gaskiya daurin da aka masa a kafa yakara kwancewa, saboda haka sai aikin yadawo sabo, dan haka ba aikin gaggawa bane, a kalla zakuyi koda kwana biyarne a nan kafin mubarku kutafi dashi”

Momy tashare hawaye ta tace “likita ba matsala koda wata dayane zanyi idai har dana zai samu lafiya”

Likita yace “insha Allah zai samu lafiya, yanzu bara naje nadauko kayan aiki saimu fara” yana gama fada yawuce,

Abba yana gefe yakaraso gurin momy, momy ta dalla masa harara, abba ya soke kansa yanzu harwani kunyar momy yake, a hankali yadago kansa yace “komai yafaru kaddarace sannan kuma …”

Momy ta daga masa hannu ” banason naji komai daga bakinka yanxu, kajira sai yarona yasamu lafiya” abba yayi shiru,

Nan suka same guri suka zauna,
A ranar asibiti suka kwana, abba yayita tarairayarsu duk abinda sukeso shiyakeyi, yayi nadama sosai, ita kuwa momy tadaure masa fuska, gani take duk abinda yafaru da afham laifin abba ne,

Haka dai suka zauna asibiti suna jinyar afham,

**** ******

Ameelah kuwa tasamu sauki, aka sallameta su momy suka daukota aka dawo gida,

Basuda labarin komai akan hilal, ita dai momy tayi imani dazaizo yadauki matarsa sukoma gidan aurensu, ameelah ma haka domin tasan hilal bazai iya rabuwa da ita ba,
Abban ameelah kuwa tun suna asibiti yadaina yiwa momy da ameelah magana wani irin haushinsu yakeji,
Lokacin da suka koma gida lokacin yahada kayansa yabar kasar, saidai yabarsu komai na abinci da kuma kudin kashi,
shidai kawai bayason ganinsu yanzu,


Shirye2 kayan auren hilal da hajna kawai umma take,
Hilal ma haka, en kwana biyun nan dayake zuwa gurin hajna zance sai yaji duk yafara sonta,

Wani sabon gida hilal yakama, acen zai tare shida amaryarsa hajna


Yaune aka daura auren hajna da hilil (H + H) dangin momy ancika gida kowa yazo sai murna ake,

Magriba nayi aka dauki amarya hajna aka kai gidan angonta hilal,


Ameelah tana kan sallaya tagama sallar magariba, tajiyi sallama a falo dasauri tayi adua tafito,

Amrah ce kawarta fuskarta a murtuke, ameelah tace “ah ah manya masu gari, lafiya naga kinwani murtuke fuska haka”

Amrah taja tsaki, cike da mamaki tana kallon ameelah tace “yanzu ke mijinki zai kara aure shine baki gayamunba, lallai..”

Mummunan faduwar gaba yaziyarci zuciyar ameelah, dasairi ta katsewa amrah magana dacewa ” auren kuma, hilal dinne yayi aure, kodai wasa kikemun”

Amrah ta yatsine fuska tace “kamarya wasa, bari kigani, hannu amrah tasaka a jakarta tadauko invitation card ta jefawa ameelah, sannan taci gaba dacewa “kadauki wannan kiduba, wlh hilal yakara aure kuma kawarmu HAJNA ya aura”

Ameelah taja baya tasaka wata irin ihu, a hankali take fadan “innalillahi wa innan ilaihin raju un ” dakyar tasamu tayi controlling din kanta,

A hankali ta zura hannu tadauki invitation card din tana karantawa ,

Tashin hankali karara ya bayyana a fuskarta, gumi yakaryo mata, harwani jiri yafara dibanta, tasa hannunta na nadama ta dafe goshinta,

Tajima a hakan sai cen kuma Ta dago kai ta kalli amrah a alokacin har kuka yasoma zomata…

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button