AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 87-88

??86 and 87??

Via OHW???? www.gidannovels.blogspot.com

BAYAN KWANA BIYU

Ameelah ta farka, momynta tasanar da ita komai akan hukuncin da hilal yayanke, nacewa yanason yasan dalilin dayasa take cutarsa, ba wani kuka tayiba domin ita gani take bazata taba rasa hilal ba,
**** *****
Acen kuwa gidan su afham, kusan kullum sai aneesah ta nemi wayarta amma ta gagara ganinta,

Yauma tashigo dakinta tana kara dundubawa guraren dabata duba ba, cen sai tatuna da kasan gado, wadda tun ranar data fara neman wayar bata taba tunanin taduba kasan gadoba,

Bakin gadon taje tadauke katifar datake kan gadon, tana daukewa kuwa saiga wayar, cike da jin dadi tasa hannu tadauko,
Har a lokacin wayar tanada chaji, sakon da hilal yaturo taci karo dashi, tafara karantawa, tashin hankali karara ya bayyana a fuskarta,

Dasauri tafita taje tanuna momy, momy tana gani tanufi dakin abba, bayan takai masa ya karanta, cike da bacin rai yace “ba inda zamuje”

Momy tafashe da kuka tana cewa “haba alhaji ni wlh narasa gane wace irin zuciyace dakai, gabaki daya bakada tausayi, yanzu a aiko sakon yaronka yasamu hatsari amma saikace baza ajeba, toni zanje, kabani izini natafi,” hawaye tap a idonta takarasa maganar,

“Ni ban baki izinin fitaba koda daga nan xuwa bakin zauren gidan nanne idan kuwa kika fita bada izinina, shikenan kuma kinsan zunubin fitar macce batare da izinin mijintaba” abba yafada yana karasa maganar yafita yabar dakin,

A hankali momy ta sulale tafadi kasan cafet tana kuka, zuciyarta cike da tunanin yaron ta afham,

Tajima tana kuka kafin tatashi tashare hawayenta, takoma dakin aneesah,.itama kuka tasameta tanayi,

Momy takarasa gurinta tace “kishirya gobe muje gombe, wurin afham” takara tambayar aneesah cewa” an rubutu sunan asibitin dayake a cikin text din,

Aneesah tace “eh anturo”
Momy tamike tsaye tace ” toshikenan gobe kishirya mutafi” tohm kawai aneesah tace, momy tafita tabar dakin, …

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button