AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 89-90

??88 and 89??

Via OHW???? www.gidannovels.blogspot.com

Acen kuwa bangaren Afham har kwana biyun nan suka cika kullum a matse yake yanaso yakoma gida domin yanemi gafarar iyayensa,

Tun cikin dare yakarbo takardarsa ta sallama, duk da likitansa baiso hakan bah, amma ganin ya matsu yasa yabashi, a cikin daren likitin yatai maka masa yakaisa har hotel dinda yasauka suka kwaso kayansa, sannan ya hadashi da wani driver, motar afham yajayo suka hau hanyar abuja, cikin daren,

Koda gari yawaye su afham sun isah abuja, sai cikin harabar gidan su driver yaja parking,

Yafito yazo yataimakawa afhan yafito, suka nufi cikin gidan,

A bakin kofar shiga yaci karo da abbansa zai fitowa wani irin wawan kallon yamasa, ya murtuke fuska, ya tare gaban afham “ina zakaje”

Hilal ya sunkuye kansa kasa kai tsaye hawaye suka gaggaro kan kuma tunsa”
Yabude bakin zaiyi magana sai kuma, yafasa,
Abban yaci gaba dacewa “karka shigarmun gida kajecen, kazabi wasu iyayen domin ni baka daukeni da daraja ba” nan fa abba yaci gaba da masifa yana hargowa,

Momy da aneesah suna cikin dakin momy suna hada kayan tafiya sukaji hargowar abba a waje, shi suke jira yafita saisu wuce gombe,

Momy tafito da sauri aneesah tabiyo bayan ta,
A daidai lokacin da suka karaso gurin a lokacin abba ya ture afham,

Afham ya tangada yafadi kasa, ai kuwa nan yasaka kara,
Momy tayi saurin karasawa gurinsa, a lokacin yadafe kafarsa yana kuka, momy hawaye take tana taba jikin afham taji duk ya rame ya chanza,

jini sukaga yafara fita a kafar afham, momy ta firgita sosai, dasauri ta koma cikin gida tadauko mayafinta, gurin fitowa saida ta bangeji abba,
Amma bata kulashiba,

diver daya kawo afham tace yatai maka mata, susakashi a mota akwai asibitin guragu anan kusa dasu suje sukaisa a duba kafar,

Nan suka saka afham a mota sukafitar sukabar gidan,

Abba yayi tsaye, duk yaji yanayinsa ba dadi, aneesah tana kusa dashi sai rusa masa ihu take tana kuka,
Sai kuma yafara jin tausayin afham, meye ribar zafin zuciya, babu abinda yake haifarwa face nadama da danasani,

Bashiru yafara jin saukar hawaye a kan fuskarsa, a lokacin ya juyo ya kalli aneesah yace “tashi kishiga ciki kidauko mayafinki mutafi musamesu”
Da gudu aneesah tashiga gida tadauko mayafinta koda tazo harya tada motar nan suka wuce asibinn…

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button