AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 21-22

??21 and 22??

Ameelah qagara tayi tabar wayanta tayi charge suna cikin fira da ‘Hmm’ wayanta ta dauke don ita saboda tsabar son chat ko bata da charge batason ajiye wayan tayi charge.

Daqyar ta gyara dakin cikin sauri ko shara bata tsaya yiba balle aje ga batun abinci, tayi wankanta ta shirya cikin doguwan riga sky blue tayi kyau sosae sai dai shigar kamatah yayi mijinta ne ta mawa, amma ina bayada AMANAR AURE tadauki rudin shaidan,

Da sauri ta karasa inda wayanta ke charge, wayar na lake da chaja ta dauko ta zauna ta kunna data sannan ta shiga fezbuk, tafara duba text din frds dinta, kamar kullum da frdrsqt akai, nan tayi accept dinsu tun kafin massages su karasa shigo matah, bata dade a ciki ba ta koma whatsapp

Cikin nishadi take replyn har tazo kan numbrr Afham, tsayawa tayi saboda number tayi matuqar burgeta so speacil, shiga tayi ta duba text din kamar haka “Assalamu Alaiki, Sunana Afham! Ina fatan zan iya kasancewa Abokin firanki”

Murmushi tayi a ranta tace “sunan nashi ma mai dadi, ko ya kamanninshi zasu kasance?? Tunanin Amsar da xata bashi ta tsayayi, data rasa me zata ce mishi ta wuce kawai,

Taci gaba da duba text dinta, har a lokacin “Hmm” yana online, text dinsa nakarshe ta karanta kamar haka “beauty idan ina chart dake jinake gabaki daya natsuwata tadawo gareki”
Kalaman sun matukar mata dadi murmushi tayi wadda yakara bayya kyaunta sannan tafara typing

Ameela “??hmm nima hakan nakeji aduk lokacin da muke chart, hakan yasa a duk lokacin da zamuyi chart sainaje nayi wanka na chaba ado kafin mufara”

Hmm “??beauty kenan najidadi sosai, gaskiya inason naga irin kalliyar da kikayiwa wannan chart namu”

Ameela ” To shikenan,
Daidaita zamanta tayi sanan ta kunna camera, ta dauki wani kyankyawan selfie tatura masa,
Photon yanuna alamar yashiga

Hmm “?? wow kinyi kyau sosai, Allah ya mallakamin ke a matsayin matana,
Gaban ameela yafadi ta tsaya tana karewa text din kallo, tana tunanin wace amsa zata bashi,
Nan taji dinn, karar text yakara shigowa, text dinshine kamar haka

Hmm “Naji kinyi shiru bakice ameen ba kobakya sonane”
Ameela tayi rau rau da ido kamar mai shirin yin kuka, ta daura hannunta akan kypat tana tunani mezata rubuta masa…

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button