AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 31-32

??31 and 32??

Via OHW????
AMAL kenan, yarinya mai hankali da natsuwa ga son addini, ta turo kofar falon tashigo, aneesah da Ammi suna zaune a falon amal tashigo, aneesah ta tashi tana murna ta rungume amal, Ammi datake gefe tana murmushi tana kallonsu, bayan aneesah tasaki amal,
Amal ta sukuyar tagaida Ammi,
Ammi ta amsa cike da jindadi, sannan tatashi tabar musu falon, bayan sun zauna,

Aneesah tace ” ya ustaxiya, ke kullum kinrufe jiki da katon hijab saikicevwata matar aure dubi dan Allah duk zafin nan kinsaka safa”

Amal tayi murmushi wadda yakara bayya dimples dinta “eh naji, komai zaki fada kifada, addinin mu yasanar damu cewa duk ilahirin jikin ‘ya macce al’aurace bayan fuskarta da kuma tafin hannunta, kingakoh yazama dole narika rufe duk wata al’aura datake jikina”

Aneesah ta tabe baki “aikuwa daman nasani ana fara miki magana zaki fara yiwa mutane wa’azi “

murmushi amal tayi ta girgiza kai tace “hmm ai yanzu duk duniya tazama daya gaskiya wuyar fadane da ita, ida kuwa ka kuskura kafada to yanzu za’a rika kiranka mai waazi, karfa kimanta a cikin suratul AHZAB aya ta hamshin da tara 59 Allah subhanahu wata ala yana cewa, ” ??? ???????? www.gidannovels.blogspot.com ???????? www.gidannovels.blogspot.com?? ??? ???????? www.gidannovels.blogspot.com?????? ???????? www.gidannovels.blogspot.com??? ???????? www.gidannovels.blogspot.com? ???????? www.gidannovels.blogspot.com?????? ???????? www.gidannovels.blogspot.com? ???????? www.gidannovels.blogspot.com??? ??? ???????? www.gidannovels.blogspot.com??????? ??????? ???????? www.gidannovels.blogspot.com ??? ???????? www.gidannovels.blogspot.com?? ????? ???????? www.gidannovels.blogspot.com?? ??????? ??????? ???????? www.gidannovels.blogspot.com ???????? www.gidannovels.blogspot.com? ” O Prophet! say to your wives and your daughters and the women of the believers that they let down upon them their over-garments; this will be more proper, that they may be known, and thus they will not be given trouble; and Allah is Forgiving, Merciful” ” Yaa kai Annabi! Ka cewa matan aurenka da ‘ya’yanka da matan muminai su kusantar da qasa daga manyan tufafin dake a kansu. Wancan yafi sauqi ga a ganesu domin kada a cucesu. Kuma Allah ya kasance mai garafa ne mai jin qai”

Aneesah taja nunfashi tace “Allahu akbar, nidai yanzu kiyi hkr zanma zo kikoyamun irin wannan shigar taki, nima naxamo ustaxiya” takarasa maganar tare da makkale murya, aneesah taci gaba da cewa ” yanzu dai kitashi muje nakaiki ki gaida yaya afham yana cikin dakinsa, domin nasan wurinsa kikazo”

Amal ta sunkuyar da kanta cike da kunya, aneesah tazo ta kama hannunta suka nufi dakin Afham”

Zaune yake a kan wata kujera datake cikin dakinsa sanye yake da yadi fari, wadda yayi shara2 sosai, daga nesa zaka iya hango singlet dinda kejikinsa, yayi matukar kyau, photon ameelah yake kallon yana murmushi..

Amal ce tafara shigowa cikin dakin tare dayin sallama “Assalamu alaikum warahamatullahi ta’ala wabara katuh” complete ta cika sallamar, hakan yasa Afham ya chanza yanayin fuskarsa, domin yagane ko wace, tun a gurin sallamar,

Kamar bazai amsaba saikuma ya amsa ciki2,

Aneesah tace “to tunda munzo ni bari nakoma nashirya miki abinci kafin kifito”

Cike da kunya Amal tace toh shikenan”
Nan aneesah tafita tabar musu dakin,
Shiru amal tayi tana tunanin mezata cemasa..

Maganar sace ta katse mata tunani, cike da bacin rai yace “lafiya meya kawoki dakina”

Amal tace “gaisawa kawai naxo muyi”

Afham yace ” to shikenan mungaisa, saiki tafi koh”

Amal tayi gyaran murya tadaga edo ta kallesa, a ko wane bugun zuciyarta kara son afham take, amma tarasa dalilin dazaisa ya tsaneta,

Amal tace ” ya Afham meyasa kake wulakantani, nifa mutumce kamarka, kuma yar adam kamarka amma narasa dalilin dazaisa karika wulakantani, dan Adam fa abin karramawane koda kuwa baka sansaba, balleni danake yar uwar, Allah subhanahu wata’ala yana cewa nakarrama dan adam fiye da kowace halinta datake doron duniya, yaya Afham kasani cewa…”

Afham yadaga mata hannu ransa abace, “ya isa haka, naji kuma nayarda, matsalar ki kenan daga anfara magana sai kifara wa’azi, ni ko wannan wa’azin naki yana daya daga cikin abubuwan da banaso, saikace wacca aka haifa agaban littantanfan islamiya, Afham yakara kallon irin yanayin shigar Amal, yaja tsaki yace “lok amal nifa tsarinki kwata kwata baimunba, ke gabaki daya local ce baki wayeba” yatashi tsaye yana nuna mata dan yatsa kamar zaikai mata duka “dubi yadda kike shigarki saikace yar gafaka, dan Allah Amal ki hakura dani, kinji ance kwarya tabi kwarya kibarni nasamu daidaini kema kije kisamu daidai ke”

Amal hawaye take sosai, tana danasanin zuwa dakinsa datayi, daman tasan wulakancine tukwauicin dazata samu, dolece tasa tazo saboda son datake masa,

Yaja tsaki yanufi hanyar fita, a bakin kofar yaci karo ammi dasauri yaja da baya, ammi takarasa shigowa dakin ta kalli amal sannan tajuya ta kalli afham ta bata rai sosai tace “daman nasan za’a rina, hakan yasa nabiyo bayanta domin nasan halin wannan bakar zuciyar taka, inajin duk irin abubuwan dakake fada mata, ka kyauta mutumen bazan, wadda bayajin maganar iyayensa”
Afham yakara tsuke fuska yana gunguni yace ” yanzu ammi saboda amal zaki cemun mutumen banza” cike da hargowa ammi tace “eh nace, maras kunya wadda baya tsoron fushin iyayensa”
“To shikenan, afham yafada cike da bacij rai yanufi hanyar fita da karfi yaja kofar kamar zai karyata, yafita yana huci yabar dakin”….

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button