AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 63-64

??63and64??

Momy tana zaune harya karasa sallarsa, sai da yagama adu a sannan tatashi tafita,
*** *** ***

Hilal kuwa sai bayan magriba yadawo, yayi parking na motarsa sannan yakaraso ciki falon, sallama yayita rabkawa shiru, babu amsa,

A zuciyarsa yace kodai wannan bacci take,

Dakin ameelah yanufa ya tura kofar yashiga, a kwance yasameta kasa tana kakin yawo masu kumfa,

Tadafe cikinta, tana kugi, a firgice yakarasa gurinta ya daga kanta cike da firgita yadaga murya sosai “ameelah meya faru dake, meya sameki”
Ameelah takasa magana, edanu take fitarwa bul2,

Hilal ya tsorata sosai, a gigice yadauketa yaje yasaka ta a mota ya nufi asibiti cikin gudun bala i,

Yana karasa asibin aka karbeta aka bata taimakon gaggawa,

Kusan awa Daya ameelah bata farkaba,
Hilal duk ya tsorata, yaso yakira iyayenta amma yafasa,… Yana xaune Likita yafito a firgice bai tsaya gurin sa ba yawuce office dinsa,

Hilal yatashi yabi bayanshi,

Dashigar likitan cikin office din ya dukufa gurin neman wani abu,

hilal yashigo office din, a tsorace yace “likita meya faru da matata”

likitan yadaga kai ya kallesa sai kuma ya basar yaci gaba da dubin takar dunsa, hilal yakara tambaya, sannan likitan yace ” ba matarka bace a gabana yanzu, domin matarka farkawarta kawai muke jira, guba taci abinci kuma mun magance matsalar domin gubar bamai yawa bace, kuma bamai saurin illatawa bace, amma dai kukiyeye gaba,”

hilal yayi ajiyar zuciya yace “to shikenan Allah ya farkar da ita”

likitan yace amen, bai kara cewa komaiba yafita yabar office din, likitan yaci gaba da neman takardunsa,

Wata takarda yagani acikin wani file, daukota yayi, sannan yaduba yayi ajiyar zuciya, yafita,

Sai bayan isha ameelah tafarka, likita yayiwa hilal izini akan yashigo yaga matarsa,
Hilal yashiga yazauna gefen gadon da ameelah take kwance ya kalleta ta sunkuyar dakai yace “waya baki guba abinci”
Kanta a sunkuye tace “nima bansaniba”
Hilal yayi ajiyar zuciya yace “meyasa baki kiraniba lokacin da kika fara jin abin acikin ki, yanzu da Allah baisa nazo bafa yazakiyi kinga sai kawai nazo natarar da gawarki”
Ameelah tadaga kai ta kallesa cike da mamaki tace “dame zankiraka ai kasan banada waya”

Hilal yaja nunfashi “sorry kinga harnama manta, yayi shiru kamar yana nazarin wani abu, sai cen yace “to shikenan zansan mezanyi akai, yatashi yana kallonta “yanzu kijirani nakarbo takardar sallama saimu koma gida”
Ameelah ta girgiza masa kai yafita…

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button