Labarai

An cafke wasu maza su 10 da laifin yiwa yarinya fyade a Nijar

Labarin na cewa anga Abin ban mamaki a wurin wani sha’ani haka a garin tawa Dake jamhuriyar ƙasar Nijar, inda ake zargin wasu ƙattin maza da yiwa yarinya matashiyar fyaɗe.”

 

Aurene aka yi na ƴar uwatan a dangi, Tom sai yarinyar ta wanke ƙafa da sunan zata tafi wurin bikin, sai ta je garin da taje garin sai akai biki aka ƙare.”

 

 

Bayan kammala biki sai da yamma aka zo ɗaukar amarya haka, ga motar amarya da motar kwashe kaya sun zo, tare da masu mashina suna zuwa su ɗauki ƴan mata domin su tafi da su gidan amarya.”

 

Labarin dake cigaba da bayyana cewa, shi ne fa sai wani ya ganta daga cikin su ƴan matan, sai ya yi mata magana da suna zai ɗauketa zuwa gidan amarya, ita kuma sai ta nuna masu cewar itafa atafaf ba wanda zai ɗauketa a mashin.”

 

Har wala yau dai, kawai sai mai kashin ɗin ya tafi ya barta nan tsaye, sai wani mai mashin ɗin ya zo ya ɗauketa ashe suna tare da waƴan canne, suka haɗe mata kai tun da ta yi masu musu su a ganinsu wulakanci ta yi masu naƙin yarda su hau mashin ɗin nata, hakan ya nuna suna jin haushin ta akan abin da ta musu.

 

Wakiliyarmu ta cigaba da bin diddigin lamarin, inda har ta gano tabbacin faruwar lamarin akan cewa, to shi ne ɗayan ya zo ya ɗauke ta, ana cikin tafiya sai ya tsaya ya ce mai nashi ya ƙare, sai da kowa ya zo ya wuce ya bar su a baya.

Hasalidai Daga nannefa shi ne sai da ya duba ya ga babu kowa a bayansa da gabansa sai ya kwantar da mashin ɗin ya buga sai ya bi wata hanya daban da yarinyar, nan take sai ya tsaya a kusa da wata bishiya ya ijiyeta sai tace mishi malam mai nai maka da zaka kawoni nan ?

 

 

 

Budurwa ta sake masa tambaya da cewa, mai makon ka kai ni gidan amarya! ka kawo ni nan to mene nakeyi anan shi ne fa a she duk suna nan a wajan ɓoye su sauran abokanan, duk suka fiffito hadda wanda ta yi masu musu da cewa ita ba zata hau mashin ɗin su ba, sai suka ce da ita bamu zakima wulakancin ba to zaki gani sai mun wulakantaki, to shi ne fa su 10 nan take suka mata fiyaɗe.

 

Bayan sun kammala jindadin su da ita suka kawo ta bakin titi suka ajjiyeta cikin jini face-face, sai dai hukuma ta shiga ciki inda yarinya ta bada labarin faruwar lamarin da haka aka bi aka kama su, a halin yanzu haka suna gidan yari tare yankewa duk dayansu tarar miliyan ɗaya.”

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button