AURAN WATA DAYA

Hannu kawai ya mi’ka mata yana kallon ta, da sauri ta bud’e maganin ta b’allo masa ta mika masa da ruwan yana shanyew ta mi’ka masa ragowar shima ya shanye, mamaki ya bata ko wannan b’ata ran dayake idan zaisha magani yanzu baiyiba.
‘Kwashe magungunan tayi ta mai dasu inda ta d’auko, har lokacin kallon ta kawai yakeyi, a xuciyarta tace anya kuwa wannan lafiyar sa d’aya?? Komawa tayi kusa dashi tace “yaya ko bakajin dad’i ne??”
Murmushi yayi yace “babu komai maganin dana sha ne”
“Owk Allah ya ‘kara lafiya” tana fad’a ta mi’ke tace “sai da safe ni na tafi”
“Allah ya tashe mu lafiya” kawai ya fad’a ta fice daga d’akin.
*****************************
Haka dai rayuwa taci gaba da tafiya, gaba d’aya Sadeeq ya matsawa kansa da tunanin shin khairat zata yadda su cigaba da zamansu kuwa?? Wani mugu mugun sonta yakeji yarass gane maiyake damun sa,gashi ko wanda zai bashi shawara bashi dashi, harga Allah baxai iya zuwa wajan Abdul ba saboda bai manta yadda sukayi dashi akan maganar Khairat d’in ba,
Yau ta kama saura ‘kwana 2 30dys d’in da Sadeeq ya d’iba musu ya cika, tunda ya fita office ya kasa zaune ya kasa tsaye, daga ‘karshema tattarawa yayi yabar hospital d’in, gida yaso ya koma amma bazai iya komawa ba, ‘kwana 2 Khairat ta isheshi da tambayar meyake damunsa yake wata muguwar rama, tayi juyin duniya amma yace mata babu komai.
Wani lokacin sai yaji kamar ya fito ya fad’a mata kawai a wuce wajan koshima ya samu ‘kwanciyar hankali, fargabar sa d’aya shine amsar da khairat zata bashi.
Yanke shawarar zuwa ya gaida mom d’insa yayi saboda yasan yanzu Dady yana office, yana gama wannan tunanin ya nufi gidan nasu.
Mamaki momy tayi ganin sa a wannan lokacin kallon sa tayi tace ” bakaje aiki bane yau?”
“Naje Momy kaina ke ciwo shiyasa na dawo”
“Toh Allah ya sawwa’ke”
“Ameen”
“Amma ai da kasani gidanka ka wuce ka ‘kwanta kad’an huta”
“Mom gani nayi ‘kwana 2 banxo ba shiyasa nace gwara na fara zuwa na dubaki”
“Toh ka kyauta kuwa”
Aisha Momy ta ‘kira, bata jima ba ta fito ta gaishe da Sadeeq. yana amsawa tace “yaya yana kayi wani mugun rama ne?”
Harara ya watsa mata yace “ina ruwanki?”
Zatayi magana Momy tace “kinga ba surutu na kiraki kiyi ba jeki kitchen ki d’auko masa kunun ayar nan danayi d’azu”
“Toh Momy”
Bata jima da tafiya ba ta dawo hannun ta d’auke da jug, tazo gaban shi ta ajje ta tsiyaya masa, d’auka yayi yanasha ita kuma ta koma d’akinta saboda karatu take.
Momy ce ta ‘kare masa kallo tace “Sadeeq dan Allah karka b’oyemin ka fad’amin abinda yake damunka”
ajje kofin hannun sa yayi yace ” mom nifa babu abinda yake damuna, me kika gani kikayi wannan maganar? ”
Karkad’a kai tayi tace “haba Sadeeq karka manta ni mahaifiyar kace ko kallon ka nayi saina fahimci a wane hali kake ciki, bare kuma irin wannan ramar da kayi tayi yawa”
Kallon ta yayi tabbas bazai iya yiwa Momy ‘karya ba amma bazai iya fad’a mata abinda yake damunsa ba.
Ganin yayi shuru ne tace “kayimin shuru bayan nasan kaji menace”
Sai da ya sauke nan nauyar ajiyar zuciya sannan yace “tabbas momy babu ‘karya ina cikin wani hali wanda yake sanya ni cikin damuwa, amma dan Allah mom ki gafarce ni karki matsa a kan na fad’a miki abinda yake damuna, addu’ar ki kawai bake bukata”
“Shikenan tunda kace haka bazan matsa maka ba,amma inaso ka rage damuwa ka dage da addu’a komai yayi zafi maganin sa Allah”
Haka Momy tayita yimasa addu’a har lokacin da akayi sallah sannan ya baro gidan.
*Neenat seif (Peenah pinkly)????????*
????????????????????????????????????????????????????????????????
AURAN WATA D’AYA
????????????????????????????????????????????????????????????????
*written by neenat seif (Peenah pinkly)????????????????????????????????*
????GORGEOUS WRITERS FORUM????
????G.W.F.????
*Home of gorgeous, intelligent, and expert writers, we are the best among in the rest.*
Https://www.Facebook.com
*Dedicated to my sis jammy Allah yabar ‘kauna wanna page nakine sai yadda kikeso xakiyi dashi ????*
*Page 32*
[ad_2]