Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 51

Episode 51*

……..Anne ta cigaba da maida hankalinta ga Raudha har zuciyarta ta fara hasashen abinda yake dai-dai. Sai dai ta danne komai batace ba har la’asar da aka

tashi salla. Ramadhan ya fito sanye cikin ƙananan kayan daya canja suka sake fita massallaci da Bappi dan Pa na sashensa shima da iyalinsa. Har lokacin su

Rumaisa na tare da Raudha harma sun kara samun yawan ƴan hirar su Sumayya. Magana kawai yay musu su tashi suje suyi salla ya wuce abinsa yana satar kallon

Raudha da tun fitowarsa tai ƙasa da kai tana wasa da yatsun hanunta da jan lalle ya ƙawata dogayen faratanta.

       Koda ya dawo bai samesu a falon ba, acan bedroom ɗin kusa da na Anne yaji hayaniyarsu. bai saniba ko Raudha na tare da su ko tana ɗakin Anne. Haka ya

wuce sashensa ya buɗe garden ɗinsa dake a gyare tsaf da korayen tsirrai masu kamshi da ni’imar ruwa ya shiga. Tunanin kiran wayarta yayi, sai dai akashe ma

akace masa. yaja guntun tsaki dakai hannu ya shafi sumar kansa. Duk saima yaji zuwa gidan ma ya gundiresa, dan ba haka yaso ba kwata-kwata. Ya riga ya gama

tsara kasancewarsu a sashensa daga shi sai matarsa su huta yanda ya kamata, amma sai gashi hakan ya gagara.
       Tun Raudha na daurewa dai har abin yaso fin karfinta. Dan da ƙyar ta iya dauriyar zagaya duka sassan gidan gaishe da matan Pa. Cike da takan tsantsan

da faɗuwar gaba ta isa sashen Gimbiya Su’adah wannan karon, fatanta da addu’ar ta ALLAH yasa karta shaƙa mata tsakin kuka kamar wancan karon. Dan yau kanta

shima wani azabar ciwo yake mata bayan zazzaɓi da ƙasanta da takejinsa kamar ana yankata ana watsa barkono a wajen.
      Badai a mata turaren tsakin kuka ba, amma ta fuskanci cin zarafi wajen su Muneera dake zaune tare da Gimbiya Su’adah a ɗakin. A kuma nan suke tabbatar

mata da auren mijinta da Ayna’u. Sosai hankalin Raudha ya tashi, da jin wannan zance sai dai ta bala’in dakewa kamar babu komai a ranta. Ta saki murmushi

mai kayatarwa da faɗin, “ALLAH ya sanya alkairi”.
        Dukansu kallon mamaki sukai mata dan basuyi zaton tanada bakin amsawaba musamman yanda tsoron gimbiya Su’adah baya ɓoyuwa a saman fuskarta.
       “Idanma baki faɗa har zuciya ba dai sai anyi, nanda sati uku Aunty Aynah nakan karagar mulkin first lady ba illiterate irinki ba…”
      Bumm kakeji Bilkisu da basu san da shigowartaba ta buge bakin Muneera dake maganar. “K dai baki da kunya sam Muneera. K har kina da bakin kiran wani

illiterate? Koda kikai karatun ubanmi kika sani. Dan duk gidan nan kinfi kowa jakanta, badan Pa ba kin isa ki gama jami’a ne iyanzu kullum cikin daukar Cary

over. Ina tausayin randa zaki ɗanɗani azabar gidan aure dan duk abinda kayi kaima sai an maka shi mtsoww”.
      Tana gama faɗa ta kama hanun Raudha suka fice a ɗakin batare data saurari ihun da Lubnah da Ayna’u ke mataba. Gimbiya Su’adah kam uffan batace ba har

bilkisun ta fice da Raudha. Hakama surutan su Aynah ɗin baisa ta tanka ba.

      Kafin su karasa sashen Anne Raudha ta tsaida Bilkisu tana bata haƙuri dan sai mita take da cewa yau saita sanarma su Bappi abinda su Muneera ke 

mata da ɗaurin ƙugun Maah. Roƙonta taitayi akan tabar zancen ita hakan baya damunta, kuma Maah mahaifiyace a gareta ai, ta isa ta mata komai. Amma Bilkisu

ta dage akan saifa ta faɗa an ɗaukama abun mataki. Da ƙyar Raudha ta shawo kan Bilkisu ta haƙura suka karasa ciki Raudhan na tafiya da ƙyar. Dan har cije

lips take da haƙori sannan bata iya haɗe ƙafafun.
        Ramadhan dake bayansu batare da sun sani ba ya bita da kallo cike da tausayinta da wani ƙarin ganin girmanta. Koba komai yana son mahaifiyarsa, sai

dai shima baya ƙaunar wasu halayenta amma babu yanda zaiyi yana ƙoƙarin mata addu’a. Suko su Lubnah lokaci yayi dazai ci ubansu gwargwadon iko.

       Yafendo data kasa haƙuri yanayin na Raudha ce ta fargar da Anne cikin raɗa dan suna tare a falo suna magana akan meeting ɗin da zasu zauna yau iya su

manya dangane da abinda gimbiya Su’adah ta kawo na auren Ayna’u da Ramadhan.
      “Anya kuwa basai yanzu megidana ya taɓa Ameenatu ba? yanayinta yayi kama da hakan”.
     Anne dake bin Raudha da kallo ƙasa-ƙasa itama tace, “Tun ɗazu na lura da hakan wlhy Yafendo, sai dai kuma idan na tuna abinda ya faru tun washe garin

aurensu da ɓarin da tayi saina ture hakan a raina. Ƙila wata matsalace daban kuma”
         “To lallai al’amarin akwai ɗaure kai, kodai akwai abinda bamu fahimta dai-dai ba tun a wancan lokacin, kokuma bai bar halin nasa na idan ya fusata

ya sauke fushinsa kan mace ba?. Ya kamata a binciketa kam a bata kulawa dan yanayinta gaba ɗaya ya fallasa taji ciwo a wajen ko makamancin hakan”.
      Numfashi kawai Anne ta sauke suka bar zancen suka kama wani. Suna wajen har aka kira magrib, a lokacin Raudha na can kwance zazzaɓi ya mata rijif. Da

ƙyar ta iya tashi tai salla. Tana idarwa ta koma saman gado ta kwanta harda jan bargo hawaye na zubo mata. Tambayar duniya Bilkisu da su Rumaisa sun mata

amsa ɗaya take basu (babu komai).
      Bayan sallar isha’i suna falo zaune Raudha nata dauriya Anne ta fito daga ɗaki tai kiranta, da ƙyar ta iya dauriyar ganin ta saita tafiyarta amma

hakan ya gagara. Har suka shiga ciki Anne batace mata komai ba, sai da ta zauna tana gaisheta ta haɗe fuska dan bata son Raudha tai mata gardama. Murya a

dake tace, “Ameenatu faɗamin mike damunki tunda kukazo gidan nan naga baki da walwala kuma idonki ya nuna kinyi kuka?”.
        Da sauri ta girgiza kai tana haɗiye hawayen dake neman zubo mata na zugin da take ji tace, “Ba komai ALLAH Anne. Kawai dai banajin daɗi ne”.
      Shiru Anne tai cike da nazarinta. Sai kuma ta miƙe batare da tace komaiba ta nufi toilet ɗinta. Ruwa mai zafi ta haɗa yanda tasan zai taimaki Raudhan.

Sannan ta fito ta kama hanunta suka shiga ciki. Duk yanda Raudha ke wani zame-zame ga kunya kamar zata halakata Anne bata saurareta ba. Babban towel ta bata

ta ɗaura ta lulluɓa da gyalenta sannan ta sakata shiga cikin ruwan. Wani kuka maiban tausayi Raudha ta sanya har numfashinta na fisga kamar zata shiɗe. Ga

kunyar Anne ga azaba, jikinta har wani karkarwa yake. Anne ta gama fahimtar matsalar Raudha amma mamaki ya hanata gaskatawa.
      Haka ta sake canja mata wani ruwan har sau uku, sai ga Raudha taji wata irin nutsuwa na saukar mata. Anne ta fito tana bata umarnin tayi wanka da

ruwan ɗumi kafin ta fito.

       Ramadhan da tun shigar Raudha ruwan farko ya nufo ɗakin Annen ya tsaya cak jin ƙarar da Raudha ta ɗan saki sanda ruwan ya ratsata, ya dafe kai da

riƙe ƙugu a fili yake faɗin, “Ameenatu kin kasheni, miyasa kikaƙi yarda na tainaka miki gashi nan kin gama tonemin asiri wajen tsohuwarnan da darunta baya

karewa”.
     Duk da Anne kakace renon uwa tai masa ba kaka ba. Hakan kuma baya hanashi yin wasa da ita wani lokacin. Dole ya fasa shiga ɗakin dan yasan rikicin Anne

yanzu saita sauke masa na cikinta. Tun ɗazu itace a ransa. Duk abinda yakeyi hankalinsa na kanta, sai dai kuma haushin yanda ma ta wani sharesa na cinsa,

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button