NOVELSUncategorized

WA ZAI FURTA 18

???? *WA ZAI FURTA?*????
              1⃣8⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri’a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.**KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki…… beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

???????????????????? *RUKAYYA BAKO DAN BATTA i love you so much, remember this always*????????????.

       ***************
*Federal University dutsinma*

“`Ya juya hannun da karfi, wallahi duk ranar da wannan hannun ya yi gigin taba Bilkisu sai na karya shi, nima akanta Zan iya kisa“`……… Ya wurgar da hannun. Sannan ya kalli wadanda ke tsaye *What the hell are you doing here?* Ya daka musu tsawa…… Suka Fara darewa, mufeeda ta juya zata tafi ya fizgota….. “` Bata hakuri“`……. Tayi saurin kallon sa, Jin haka yasa kawayenta Suma suka Fara yin baya,
Bakiji abinda na fada ba?
“`ki Bata hakuri ko Kuma wallahi….“`
Ta fizge hannunta, bazan bayar ba….. Ta wuce da sauri kamar zata tashi sama…..
Aisha ta rike hannun Bilkisu tamau.
Ita kuwa kanta a kasa kawai tayi shiru……
Ya kalli Aisha, me ya hada su ne?
Me kuwa zai hada su inba kaiba??? Ita har Yanzu tana zargin akwai wani abu tsakanin ka da Bilkisu shine fa suka tare mu Yanzu mun dawo sallah….. Mtseww ya doka tsoki.
Ya Mika ma Aisha basket ungo je Mata dashi ciki….. Ta juya kawai zata tafi ya yi saurin fizgota ta fada jikinsa kanta ya daki kirjinshi…….. Yaushe Zaki fahimci da gaske bana so ki ringa tafiya idan nazo wurinki ko muna tare?
Ya hakuri sakeni please….. Ya Kara manneta jikinsa….. Aisha jeki tana zuwa.
Ta wuce tana dariya da mamakin wannan rigimammiyar soyayya.
Wai Anwar Kan ka qalau? Na shiga uku ni Bilkisu ka dubi Allah ka sakeni….. Yana rungume da ita ya Fara tafiya a hankali ….. Na shiga uku Anwar….. Ya sunkuyo Yana kokarin hada fuskar sa da tata tayi saurin sunnewa jikinsa tana Kara fadin na shiga uku ni Bilkisu….. Ya manna bayan ta da Bango sannan ya matsa baya kadan ya rabu da jikin ta yasa hannuwa biyu ya tokare bango tare da Dan sunkuyawa fuskar sa daidai tata suna shakar numfashin juna ya kafa Mata idanu…….
Innalillahi Anwar Wai meye haka? Ta fada tana faman yin kasa da Kai…….Haka zamuyi firar tunda ita Kika zaba….. Na zabi meye? Ka gyara Mana dan Allah ka matsa….. Allah ba inda zanje, ba dai taurin Kai gareki ba? Wallahi zanci gaba da binki yanda kike so, ke me yasa baki da tausayi?…… Tausayin me Wai? Ta fada tana kallonsa kamar zatayi kuka.
Gashi yauma saboda mufeeda zaki Kara guduwa kibar ni anan Kuma kin san zuwan naki ne……. Nayi Alkawarin Zan tsaya I’ll give you the time you…… Never mind, I’m okay like this…..Anwar am not okay please shift back na tuba kayi hakuri Dan …… Ke nafiki wuyar lallashi fa ki natsu muyi magana nafi Jin dadin hakan ma….. Tayi kwal kwal, ya kamata….. Na rantse da Allah kina mun kuka Zan mayar dake Nan… Ya nuna kirjin sa.
Ta hadiye kwallan ba shiri , kayi hakuri Anwar bazan Kara ba I promised.
Yayi murmushi naji but next time.
Kina da sauran tuwon nan?
Babu.
Yayi Yar dariya Yana kallon Dan karamin bakin ta da take ta faman turowa.
Duk kin cinye?, Amma fa yayi dadi. Zuwa nayi godiya waccen useless din ta Bata mun plan…. Ba komai nidai jeka sai da safe.
Ya kyalkyace da dariya kina korata ne?.
Ya Mike ya tsaya daidai ta saki wata ajiyar zuciya Mai karfi ya bita da ido Yana murmushi…… Matsoraciya kina motsawa Zan…. Ba inda zanje ta fada tare da makurewa jikin bango.
Kiyi hakuri ya fada a hankali, wallahi Nima fa bana son Ina taba ki Bilkisu ki daina mun gardama kinji?
To, ta fada a kagare.
Sadeeq ma yaji dadin tuwon nan. Ina Kika Sami manshanu?
Ina dashi. Ta fada a hankali. Duk jikinta yayi sanyi….ya Kara tsareta da ido sai ta bashi tausayi.
Bilkisu…..ya kirata a hankali.
Taji wani Yarrrr, tsikar jikinta duk ta tashi, ta kasa amsawa.
Ya Kara cewa Bilkisu……
Na’am ta fada tana murza yatsunta.
Dan Allah kiyi hakuri kinji ko?
Ba komi ta ce a hankali.
Da komai. Gashi naga duk kinyi relax, please I’m sorry.
Ba Kya so Ina taba ki ko?
Ta daga Kai alamar eh, yayi murmushi to duk laifin da nayi Miki idan muna magana ko Ina a wajen don’t leave me, kinji ko?
Ta Kara daga Kai …..yayi murmushi Baki magana?
Ta ce hmmm.
Dan Allah ki daina bana so kinji?
To Wai me yasa baka iya kyaleni in tafi?…… Saboda.. sai Kuma yayi shiru Yana murmushi.
Saboda me? Ta tsare shi da ido.
Bazaki gane ba, yace Yana Yar dariya.
Zata Kara magana ya yi saurin cewa na saka Miki turaruka a basket din da na maido Allah yasa kamshin suyi miki.
Biyana kayi kenan?
Ya zaro ido na Isa in biyaki? Allah kadai zai iya biyan ki Bilkisu.
Na zo dasu ne tun daga gida ban dai kawo Miki bane ……. Turaruwanka Zan saka ajikina?
Nope, na Mata ne musamman na siyo Miki.
Hmm, na gode sosai.
Yaushe Zaki Kara mun tuwo?
Sai an kwana biyu kuma .
Gobe me Zaki dafa?
Ina ruwanka, Kai fa abinci ne damuwanka ni kuma ba girki nazo yi ba karatu….. Dariya yakeyi har Yana dukewa…… Wannan tsiwar taki na bir…. Sai yayi saurin canza magana yace tana bani dariya.
 Ta ce hmmm, ai gara na fada maka na lura Kai baka san ayi abu Dan marmari ba.
Dan Allah kiyi abinci dani gobe…. Indomie Zan dafa malam….. Zanci indomie din please ki taimaka.
Mtsew taja guntun tsoki.
Amma ki bari Zan Miki waya ten minutes before yanda Ina zuwa kin karasa naci da zafi….. Kaci a Ina? Ka Bari Zan Aiko maka…. Bana cin indomie idan ta shiga wani kwano ba plate ba daga tukunya….. Kiyi hakuri zanzo nan in ci….. Anwar! Ta Kira sunan sa.
Ya kalleta Bilkisu!
Shima ya fadi nata .
Idan na tambayeka zaka bani amsa saboda Allah?
Ya danyi Yar dariya in shaa Allah.
“`me yasa yake son takura mun bayan ga wadanda keson attention dinka kaki basu sai ni da ban nema ba?“`
  Ya fada murmushin fuskar sa ya zuki iska ya hurar….. Saboda kece best friend Dita. I’m More comfortable with you than any other girl in this school.
Tayi shiruuuuu, ya kalleta ko ba wannan amsar kike son ji ba ya karasa maganar Yana dariya.
Ta galla mishi harara.
Kin San fa a tarihi abincin ki daya na taba ci duk school din Nan apart from sadeeq da ke Mana girki sometimes da Abdul Mai indomie…
Yanzu kuwa I don’t think ko na sadeeq zan Kara ci……. Ta zaro ido sai nawa?
Naki zanci. Gaskiya gara na fada Miki Zaki ringa Mana girki once in a day ko twice idan kina da lokaci…… Amma ka debo dala ba gammo ….. Ya kwashe da dariya.
You are my personal person am sure you’ll do it…. Bazan yi ba.
Naji bazakiyi ba shikenan Amma gobe zanci indomie ko?
Eh, amma daga ita karka Kuma cewa don bazaka samu ba….
Yayi murmushi is alright!
Zan koma ciki, na gaji da tsayuwa……. To muje ga bench a can mu zauna akwai sakon da Zan fada Miki…… Tana son mishi gardama tana tsoron ya Kara damkar ta, ta yi Dan jimmm ya tsareta da ido…… Muje ta fada a hankali.
  Kaiiii, amma fa kin bani mamaki na ji dadi sosai ko kefa? Ai gardama bata da amfani….. Suna tafiya Yana surutai kamar ta shako wuyansa takeji.
Suna niyyar Zama wayarsa tayi Kara.
Ya dauka hello…..
Ya zauna tare da Mata nuni da hannu alamar ita ta zauna. Ta Dan raba can karshe a dosane.
Ina jinka ya fada Kai tsaye.
Ta Dan saci kallon sa sai taga hankalin sa na ga babbar wayar sa Yana latsawa lokacin ne ta lura da iPhone 11x+ yake rikewa ta Dan zaro ido tana satar kallonsa.
Wai ita yau wannan tsadadden yaron ke bi…. Ikon Allah, Ina ma  zai *FURTA* Yana sonta? Wallahi zata bashi amsa da gaggawa…. Har Yanzu tana wasi wasi shin da gaske friends din ya tsaya ko kuwa ita ya mayar friends???
Ko in jaraba cewa Ina sonsa?…… Tabb idan Kuma yace baya Sona hakan ya kawo karshen friendship din mu?
Ko Yanzu a tafi a Haka nasan wasu zasuyi ta misunderstanding irin su useless mufeeda…. Ko banza dai a FUDMA nabar record………… Ke kici kanki tubbb ya tofa Mata miyau… Tayi firgigi innalillahi…ta sa hijab tana gogewa… Wannan wane danyen wulakanci ne haka zaka tofan yawu?…. An tofa sai tsareni da ido kina kallo?
Ya harareta….. Bata San lokacin da tayi dariya ba, lallai wanzami baya son jarfa, Kai duk kallon da kakeyi mun nace me?
Eh, aini bana munafurci nake ba ke kuwa sai kin lura bana kallonki sai kina dan sacewa kina….. Mtseww ta doka tsoki.
Ya kyalkyace da dariya.
Ke bakya gajiya da hijab kamar matar liman?
Kai Kuma baka iya gani ka kyale???
Ya langabar da Kai don Allah gobe kisa gyale ki fito idan na zo cin indomie……. Bani da gyale.
Anan ko?
Abuja kina sa…. Maganar ta makale ta bishi da kallo.
Abuja ma bana sawa ni hijab nake sakawa ko gida….. Dan Allah Bilkisu… Ta kalleshi Kai bana sa gyale fa.
Saboda me?
Saboda Ina kishin mijina!!!
Waye mijinki???
Mai rabo…. Ta fada tare da Dan kallon sa….
Yayi murmushi, lallai ya more ko wanene.
Ta ce hmmmm.
Amma fa mijinki zai Sha rigima.
Ko? Ta ce tana murmushi.
Eh, Mana.
Hmmm.
Kaima matarka zata rigima….. Ni Ina da rigima??? 
Kwarai kuwa.
Wace iri?
Na ci, magiya, damuwa….Kai komai ma.
Amma Kuma I’m sweet ko?
Ta harareshi a’a chewing gum…. Ya kyalkyace da dariya…..
Tashi muje ki shiga gida idan Kika biye mun zan iya kwana haka dake ban gaji ba….. Tayi zumbur kamar tana jira.
Ya Mata kallon kasa kasa har taji Yar kunya…. Ta Dan juya tana murmushi.
Kin gaji dani already ko?
Um um.
Eh Mana .
Hmmm. Tace.
Zan tura miki assignment din nan ta WhatsApp kinji ko?
Har kayi?
Yayi murmushi kawai.
Har bakin kofa ya raka ta sannan yace okay have a pleasant sleep….
Same. Ta fada tare da shigewa……
  Ta biya dakin su Aisha ta dauki key ta wuce.
Kagare take taga turarukan da yace.
Ai kuwa ta gansu don tsadaddu ne designers Kai Anwar babba ne ta fada tana juya daya Wanda yafi daukar hankalinta.
  Mashin ya hau bai Kira sadeeq ba.
   Kai Yanzu ka gane firar dare ko?
Kai Kuma ka gane sa ido nonsense ya Kai mishi duka.
Allah Anwar Kai munafuki ne……. Ya kyalkyace da dariya Kai Allah ne ya fiddani da wuri ina zuwa na tarar da mufeeda ta janyo gardawa zasu daki Bilkisu….. Ya dauki waya ya Fara nemanta.
   Da gaske??? Sadeeq ya fada Yana mamaki.
Wallahi, yarinyar Bata da tarbiyya….kaga Ina Kira taki dauka gobe Zan buge Mata warning na karshe idan Kuma bata ji ba nasa a koreta ko waye ubanta…..
  Anwar kabi sannu, fitina kwance take….
Sannan yarinyar nan kada ka takura Mata fa.
Naji. Ya fada Yana kokarin tube Kaya.
  Washe gari ta tashi da wani ciwon ciki Mai tsanani ta kasa zuwa class.
Suleiman na ganin an Gama lecture ya kirata saboda yasan ta dawo…. Anwar na bayansa Koda yaga yasa waya a kunne sai ya kura mishi ido yasan tabbas Bilkisu yake nema.
Hello….
Lafiya dai ko? Naji muryar kamar Mai bacci kamar Kuma wacce bata lafiya….
Ciki?, Subhanallahi….. Anwar najin haka yayi zumbur ya mike ya ce zo muje sadeeq… Sauri yakeyi sosai, sadeeq ya fito da gudu, Ina zamu je?
    Bilkisu ce Bata lafiya…. Me ya sameta?
Kamar naji Yana ambaton ciki it might be ciwon ciki… Suna zuwa bakin titi yace tare Mai napep ka taho dashi…. Ya tsallaka da sauri.
  Allah ya rufa Mata asiri akwai doguwar Riga a jikinta , Aisha na ta faman dama Mata oat ya shigo dakin….. Kanta ba kallabi gashi ya bazo a gadon bayanta ta kifa Kai a filo tana ta murkususu Aisha kuwa daga ita sai shimi…. Ya fado dakin…. Duk suka firgita.
Aisha tayi saurin janyo bargo .
Ko kallonta baiyi ba ya zauna bakin katifar…. Ciwon ciki ke damunki? Ya fada Yana kallon Bilkisu cikin damuwa….
Firgigi ta dago tare da janyo towel dake kusa da filon ta rufe kanta…. Anwar meye haka? Ta fada da kyar .
Ya doka tsoki. Tashi muje hospital.
Ba sai naje ba na Sha magani….. Tashi muje hospital ya fada cikin daga murya….. Ta kalli Aisha ita Daman su kawai take kallo.
Cikin ya Kara katsawa ta runtse ido tare da dukewa…. Ya dagota da karfi ya kalli Aisha Ina hijab dinta?????…. Wayarsa tayi Kara… Ya dauka sadeeq ya?
Kana inane? Gani a bakin gidan ban ganka ba…. Okay Ina zuwa…ya kashe.
Tana son magana amma ta kasa saboda murdawar da cikin keyi … Ya taimaka ma Aisha suka saka Mata hijab kawai sai ya sungumeta…….
Yi sauri ki fito…ya fada Yana kokarin fita da ita.
Sadeeq ya zaro ido Wai ciki ka shiga???? Seriously tayi penting ne????
Aisha ta fito da gudu rike da kofin oat.
Sadeeq ka same mu Sima hospital ya fada, ya kalli Mai napep muje sima.
 Suna Zama ta janye jikinta daga nashi ta dora kanta bisa kafadar Aisha.
Bai bi ta kanta ba yace Aisha meye taci ne?
Bata ci komai ba Daman haka take fama dashi….. Ciwon cikin?
Eh, tana da wani magani da take Sha ne?
Eh, Amma dai baya lafawa da wuri.
Wane irin ciwon ciki ne Haka?
Tayi shiru kawai.
Kinji?
Ta ce hmmm, Daman duk wata sai tayi?
Bai gane ba ya kalleta duk wata Kuma?
Eh.
Mtseww…… Ya kalli Bilkisu kin taba zuwa asibiti an Miki test?
   Tayi shiru kawai tana murkususu.
Ya Kara doka tsoki.
Ya dauki waya….hello yah good morning doctor please I have emergency patient are you…. Good. On my way…
Ya ajiye.
Ya kalleta sorry.
Aisha dai tayi zugum.
Bakin gate suka tarar da kijerar daukar marar lafiya.
Aisha ta Fara sumke dariya.
Suna saukowa yace hau Bilkisu…… Tayi karfin halin maka mishi harara sannan ta dafa Aisha suka wuce….. Ya biyota Baki lafiya amma Baki daina gardama ba ko?
    Dashi aka shiga wurin doctor.
Ka ce ya fita , ta fada tana kallon doctor din cikin fushi..,.. yadanyi dariya to kaji yallabai an koreka.
Wallahi ba inda zanje ka Mata test kayi scanning….. Ya Fara Mata tambayoyi.
Ta yi shiru.. akayi Justin duniya tayi magana taki.
Dole Anwar ya fita. Yana fita sadeeq na isowa….Aisha na zaune tayi zugummm tana kallon ikon Allah.
Doctor menstrual pain ke damuna Amma bana son ya sani. Ina Shan wannan maganin amma baya mun idan akwai Wanda ya fishi pls help me…… Ya danyi murmushi I expect it. 
Ya karbi maganin ta runtse ido tare da dafe cikin lokacin da ya katsa…..
Sorry ya fada tare da mikewa….. Ya dauko wata allura yace Amma fa zata Sanya ki barci sosai, sannan ya rubuta wani magani ya ce  gaskiya babu Shi anan sai Kano ko katsina Yana da tsada kwarai…. Ba komai rubuta… Burummm ya banko kofa daidai ya Gama allurar tana murzawa. Ta dalla mishi harara…..
Doctor meye tace Yana damunta?
Yayi dariya it’s normal an Mata allura ga magani nan na rubuta Yana da tsada da kudi sosai……. Ya karbe takardar Yana karanta sunan maganin.
Ya fiddo waya….. Hello musbah ga magani Nan Zan turo maka asiyo mun carton dinsa a Aiko Yanzu Yanzu ko ka tado wani ya kawo sannan kace a fada maka maganin menene da Kuma yanda ake shansa.
Kaje wurin nagari pharmacy kace ni na Aiko kaga hamisu a wurin…….
Ya Mika mishi hannu thank you doctor.
Tashi muje…. Idan kin hada Baki da doctor wannan maganin zaisa na San komai.
Idanunta suka Fara nauyi alamar allurar ya Fara aiki.
Allaurar zata sanyata barci sosai fa…..okay.
Ya ce Yana Shirin Kai hannu ya taba ta, ta mike da sauri tare da maka mishi harara…… Yayi dariya Kai yau Ina Shan harara ni Hamza.
Ta fito ya biyota ga oat din ki zauna Kisha Aisha Bata… Ka barshi Zan Sha a daki.. muje please.
Ya kalli Aisha allura akayi Mata Mai Sanya barci shine ke dibarta ga idanunta nan sun Fara canzawa da kunje kada ki yarda ta kwanta bata ci komai ba…… Ko na ajiyeta…. Ya banka mishi wani kallo. Wancen Mai napep din da na tsayar Kuma fa?
    Ta kalleshi ka bi sadeeq ku tafi mu sai muje a napep din na gode.
Kamar zaiyi gardama yayi shiru….sai Kuma ya kada Kai okay.
Idan kin tashi barcin ki mun flashing please.
Ta ce toh.
Ya zaro dubu biyu ya Mika ma driver yace mayar dasu inda ka dauko mu.
Ya Dan leka Allah ya bada lafiya Zan kawo Miki maganin kinji ko?
Ta ce toh, tana ta faman lumshe ido….. Jinsa take har cikin ranta. Bata so ya tafi…..ashe shima hakan yakeji…….Sadeeq ya kalleshi abokin Bilkisu….. Ya Kai mishi duka. Shi Kuma ya tuntsure da dariya…..

Ta kalli Aisha kinji yayi waya maganin da aka rubuta a kawo carton dinsa daga Kano…..ta zaro ido carton?
Wallahi….
Bilkisu Anwar ya Fara bani tsoro…Nima Aisha. Anwar Yana bani tsoro. Da na motsa sai yace mun friend…. Ke ya mayar friend wannan abun nasa ya Fara wuce shari’a…Ni saboda ma duk na rikice can daki na bar wayar.
Aisha tayi dariya nima.  Wai Kinga yanda ya wani fado kamar an jefo Shi????
Tayi tagumi tawa ta sameni Aisha……
Ta kyalkyace da dariya ai sai ma ya *FURTA* saboda tabbas Anwar gabbb yake da furta Miki Yana sonki alamomi dai sun gama bayyana….. Gabanta ya Fadi ta dafe kirji….. Na shiga uku…..ta galla Mata harara *Baki sonsa?*……….✍???? *Zainab wowo*????

????????????mowa
???????????? Unex
???????????? Alaweez

KU TABA HOTON KASA DON BADA GUDUN MUWAR KU

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button