BA DON SHIBA HAUSA NOVEL

BA DON SHIBA 1-5

Bismillahir rahmanir raheem
Page 1⃣ to 5⃣

yarinya ce yar kimamin shekara 14 take ta kai kawo a cikin tsakar gidan kallo daya zaka mata zaka gane agalaibe take aikin juyar da kanta tayi zuwa wani sashe dake tsakar hmm tace a hankali nima na kai dubana sashen da take kalla abin mamaki wani uban tulin kayan wanke wankene kamar anyi sati ana tara shi kuda kuwa sai rawar banjo suke akai hawaye ta share a hankali kafin ta doki kujera yar tsugunne ta

karasa wurin zama tayi jiki a sanyaye ta fara wankewa dama ta riga ta dibo ruwan tunda safe kanta a duke yake amma duk hakan bai hana hango hawayen da ke zuba a idonta ba wata irin rayuwa akeyi a gidansu ta rashin adalci akwai yayyanta yanmata har gudu uku amma basa aikin komai sai dai kawai ayi kwalliya a fita harta kayansu ita ke wanke tana cikin wannan tunanin bata auneba taji wani uban rankawashi akanta kwass kake ni kaina sai da na tsorata dago kai tayi da sauri tana shafa gurin domin ba karamin shigarta rankwashin yayi cikin rawar murya tace ki..kiyi hakuri inna mtsww dogon tsakin da matar taja ne yasa na daga kai na kallet kibarta sai data tsora tani ga idonta manya2 bakin wargajeje duk ya baci da goro

kannan kuwa dukun dukun yake kamar an shekara baa kitsa shiba hargowan da takeyi ne ya bani dama hango wawake ken wuwulon dake bakin kai wannan mata ta cika kazama cigaba tayi da masifa tana fadin shegiyar yarinya me bakin halin ubanta tun dazu na saki aiki amma kina nan kina halin na munafunci ta kara kai mata duka a baya wallahi ba zaki makarantar da ake koyo miki iskanci ba bari haladu ya zo yau sai kinfi fulawa laushi kuma ki gama ga wankinsu indo can kije ki wanke su tass tunda anhana kimin tallah aikin gida ma kawai ya isheki shegia mai kama da mayu infito inga baki gama ba tunda ta fara fadanta bata dago ta kalleta ba domin kuwa tasan me hakan zai haifar mata hawayen fuskarta ta share amma kuma wasu kara zubowa suke ba duka ko zagin a akai mata bane damuwarta ta riga ta saba duk da baa sabo da wahala makarantar ta shine damuwarta domin kuwa yau suna da test kuma wannan year din zatai junior waec da sauri sauri ta kama aikinta da yake me kwazo tuni ta gama shi mikewa tayi a hankali ta leka dakin inna asabe munsharin da take ne ya tabbatar datayi bacci da gudu ta shige dakinsu ta dakko uniform dinta kayan tsab domin kuwa a goge suke komai da sauri take yinsa saboda kada inna ta tashi bata dauki jaka ba littafi kawai ta dauka sai biro fitowa tayi fice a gidan a hankali tafiya take cikin nutsuwa duk da kuwa tasan tayi latti wannan nature dinta ne duk napep din data tara a cike suke saboda yau safiyar monday ce dakyar ta sami wani mai mashin ya tsaya mallam gumi college zaka kaini tun kafin ta gama rufe baki yace 200 zaro ido tayi ita da take naira 30 shiru tayi domin tasan ba kaita zaiyi ba dan baida alamun mutunci a hankali tace muje to (nidae nace to waye zai biya ta taro pillars) yan mintoci kadan sukai kaisu bakin makarantar sauka tayi tare da sunkuyar dakai gajiya yayi yace yadai malama kudinafa zan baka tace a hankali
acan gefen kuma wani saurayi na hango zaune a bakin get din makarantar kanshi a duke yake amma haka bai hanani gano baiwar kyau dake kunshe a fuskar sa ba tsayawar mashin diinne yasa shi dago kanshi da sauri masha allah na fada saboda duk inda ake neman mai kyau to wannan guy din ya wuce idanuwan shi manya ne farare tass hancinshi dogo har baka bakin dan mitsili pink dasu mikewa yayi ransa a bace takowa yayi har inda me mashin din yake hararar sa yayi kafin ya ciro kudi ya mika ma dan acaban wuce muje yace mata sai da suka kai bakin ajinsu yace waya ce ki hau mashin turo baki tayi tace to ban samu abin hawa bane ne ai mtsw yayi tsaki kafin yace ya akayi kikayi latti shiru tyi ke dallah kimin magana wanki nayi wankin wa nasu indo mtsw sai naci uwarsu duka yasin wannan tsohuwar kuma inbata yi a hankali ba sai na cire mata murfin kai ya fada yana wani karkta baki kallon shi tayi a tsorace domin kuwa tasan zai iya indai AMMAR ne wuce aji kin wani tsaya kallo na wucewa tayi da murmushi a fuskarta har tayi nisa ya kwala mata kira JIDDAH waigowa tayi zonan yace da sauri ta taho kudi ya ciro ya mika mata ba musu ta amsa nagode hararar ta yayi hmm tace dan tasan manufar hakan baayaso tamai godiya wucewa duka suka yi kowa yayi ajin shi

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button