BA DON SHIBA HAUSA NOVEL

BA DON SHIBA 6-10

Page 6⃣ to 1⃣0⃣

shigarta cikin aji yayi daidai da zuwan teacher din su na english dama shine 1s test da zasu fara,ba bata lokaci ya fara rubuta musu test kan ka ce me har jidda ta kusa gama nata domin kuma jidda akwai kwakwalwa dan ma ana dankwafar da ita,karfe 9:30 daidai ta gama mika mai tayi ya amsa yana murmushi dana kasa gane maanarna sa

fitowarta kenan daga cikin aji,a gajiye take matuka ga kuma yunwar da take ji ita ta kara galabaitar da ita don tun safe har yanzu ko ruwa bata shaba”karon da sukayi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin data lula dago dara daran idanuwanta tayi ta dora akan kyakkyawar fuskar sa“”kallonta yayi a kaikai ce kafin yace “ke”zo muje bai jiran me zata ce yayi gaba abin”hmm kawai tace kafin tabi bayanshi,can bayan ajinsu suka tsaya dama tasan nan zasuje domin duk time din break shi yake sai mata abinci tun tana nauyin ci a gabanshi har ta saba,zai zauna ya jirata har ta gama amma fa ba maganar da zata hada su,ita har mamakinsa take yi amma kuma idan wani ya taba ta to fa anan ne zai nuna rashin mutuncinsa mutane abin na basu na basu mamaki yanda suka ga ammar na damuwa da duk wani lamari na jidda,domin kuwa ammar bai ragawa kowa a unguwarsu inba jidda ba”mtsww” tsakin da ya jane yasa ta dawo hankalinta kallon shi kawai tayi shiko ya tamke fuskar sa”idan ba zaki ci bane yasin zan zubar dashi”da sauri ta fara cin abincin,yanda take cin abincin ya sashi murmushi wanda ni kaina sai dana yi mamakin hakan“”tana gamawa kuwa ana komawa aji kowa ya shige ajinshi sai da yaga shigewarta sannan ya wuce shima

yana shiga ya nemi guri ya zauna “yadai my man auwal ne ya zauna a kusa dashi duk makarantar shi kadai yake kulawa saboda halinsu yazo daya,daga ina kake ne uhm ko dayake nasan daga gurin jiddah kake”uhm kawai yace danshi tunanin yanda zai ci uwar inna asabe da ya’ya’nta yake shegu masu kama da birai yace a fili,da sauri auwal ya kalleshi dan yansan mutane biyu ammar ya tsana duk duniya daga inna asabe sai umma matar babanshi dukan kafadanshi auwal yayi haba man ka share mutanennan mana haka ka bari mu hadu musu target kawai,sai yanzu yayi murmushi kafin yace ai qur’ani sai na cirema asabe awazu ita da shegun yaran nan’ eh naji yanzu dai tashi mu haure ta gatanga kawai kasan fa yau madrid na wasa ko ka mantane”ban manta ba muje kawai to amma wa zai raka jiddah gida???? dallah muje zamu dawo kafin lokacin ok kawai yace tare da mikewa suka tafi

karfe 1:30 aka tashi a fitowa tayi ta tsaya a kofar ajin su ammar amma har suka gama fitowa bata ganshi
“ke”taji ance daga bayanta juyawa tayi suna fuskantar juna”waike wace irin mayya ce ne meye hadinki da ammar duk kin bi kin makale masa“”aysha kenan wadda aka fi sani da easha tana matukar son ammar amma shi bai ma san tanayi ba easha tana kyau daidai gwargado kuma babanta attajiri ne shiyyasa take abinda taga dama a makarantar tun farkon shigowarta ta ga ammar da suna dan mutunci amma tunda tace tana sonsa shike nan ya dauke mata wuta tare bata zazzafan kashedi wannan dalilin ne yasa ta tsani jiddah matuka take kuma mata wulankaci son ranta don ma ammar din yana taka mata burki ,sai data gama jirarta sannan taja yan korenta suka wuce,ita dai jiddah kanta na sunkuye dan ba iya fada tayi ba koma ta iya din ina zata kai easha ita dake kusan 18yrs kada kai kawai tayi ta fita a makarantar a kafa zata koma gida shiyyasa take ta sauri kar tayi lattin zuwa gida ta hadu da sharrin inna asabe”duk da yanzu din ma tana san ba tsira tayi ba

tun daga nesa tage hango wata dalleliyar mota a kofar gidan su ita dai a iya sanin duk danginsu bame ko mashin balle mota tunanin tane ya tsake saboda wadda taga ni ta fito daga motar RABI ce kanwar indo diyar inna asabe ta biyu sai famam washe baki take yi shiko na motar sai riko hannunta yake yi allah ya shirya kawai tace ta shige zauren gidansu turus ta tsaya ganin inna asabe na leke ta dan sakalen kofar batason da mutum a tsaye ba duhun data gani yasa ta dagowa da sauri cikin hargowar data saba ta fara magana don ubanki matsa in kalli abin arziki shegiya matsiyaciya tana bukulun kallon abin duniya yar bakin ciki kawai wuce ki bari wuri sum sum ta wuce cikin gida tana mai tirr da halin inna asabe

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button