BA DON SHIBA HAUSA NOVEL

BA DON SHIBA 11-15

Page 1⃣1⃣ to 1⃣5⃣

kai tsaye cikin daki ta wuce tana mai kara yin tirr da halin inna asabe,,uniform kawai ta cire taji ana kwalla mata kira daga cikin gidan.da sauri ta fita tana amsa kiran‘’haladu ne tsaye rike da tulin kayan wanki a hannun sa watso mata su yayi tare da cewa ‘ke’ ga kayana na nan ki wanke min su yanzu nan,bai saurari me ba zata ce ya kada kai zai kara gaba,da sauri tace mai ina sabulun da zanyi wankin,kallon banza yayi mata kafin yace‘’ ina kudin da yake biyanki na iskancin da kukeyi ko ance miki bamu sani ba to ki cira a ciki ki siyo harara ya wurga mata da jan idon shi kafin yasa kai ya fice a gidan yana wani dage kafada waishi ga gaye,,kwasar kayan tayi ta nufi bakin rijiya kafin ta tashi shiga daki ta dakko ragowar sabulun data ajiye idan zata wanke kayanta

har ta fara wankin sai ga inna asabe ta shigo kamar an korota sai washe baki take daga bayanta rabi ce rike da manyan ledoji a hannunta‘’sai wani yatsinar fuska take,inna asabe kuwa jikina na rawa ta dakko bukiti ta juye ruwan zafi a ciki sai data surka sannan tayi hanyar bandaki ta kai‘’rabi fito ga ruwan can na kai miki kidan watsa ko kya ji dadin jikinki,daga cikin dakin ta fito rike da ledojin da ta shigo da su ke ta ce ma jidda a tsawace,da sauri jiddah ta taso ta bar wankin a bakin rijiya ‘’gani‘’tace a hankali, cikin yatsina ta fara magana kamar ansata dole ki dauki kayan nan ki gyara su duka kawai tace ta nufi hanyar bandakin,ba bata lokaci ta dauka ta fara dubawa ledar farko kajine a ciki dakwala har guda 6 dayar kayan miya ne a a ciki a da kayan dandano biyun kuma da suke gefe duk kayan fruit ne a cikin‘’kajin ta fara gyarawa sannan ta hura ice dakyar wutar ta kama,sannan ta dora akah,kayan miya ta dakko ta wanke ta zuba a karamin bokiti‘’nufar inda inna asabe take a zaune tayi ragwajab kamar kayan wanki sai faman faman washe baki take yau yarta tayi kasuwa,inna kudin nika kayan miyan yana da yawa‘’a hasale ta dago tace dan uwarki baza a bada ba da hannunki zaki nika shi in baki kudin nika ai kinji dadi kenan kin huta niko bana kaunar in ga kina hutawa nafiso kullum ingan ki a wahale jiya iya yau kamar yadda shegiar uwarki tayi har tabar duniya,wuce ki bani guri mai kama da zabaya yarinya sai bakin jinin tsiya.juyawa tayi ta tana share hawayen bakin ciki ,mahaifiyarta na kasa amma duk da haka bata tsira ba amma akwai allah,daukan kayan miyan tayi ta nufi inda ake ajiye turmi ta fara dakawa,,,

hajia umma ce hakimce a kayatacce falonta“”gefen wata matace wadda kallo daya zaka mata kasan cikakkiyar yar duniya,duk da ita umman ta dan taba kafin ta samu alhj mu’azzam,hajia umma ce ta fara magana cike da takaici magajiya na rasa inda zan tsoma raina yaron nan ya gagareni baya shakkata ballantana tsorona na rasa ina zansa raina‘’rufe bakinta keda wuya magajiya ta antayo ashar tare da cewa kin bani kunya umma yanzu akan wannan dan yaron zaki tsaya kina tada hankalinki“katseta umma tayi da sauri‘’ tana fadin ke ammar fa da kika ganshi ko ubanshi baya shakka ballantana ni amma in yasan wata bai wata ba ba’a ja dani a zauna lafiya“”yanzu naji zance kawata kawai kisan yanda zakiyi yabar gidan nan koma kasar gaba daya,da sauri hajia umma tace kai kawata amma fa kin kawo shawara me kyau,wani killer smile tayi kafin tace ammar dani kake magana.

tafiya yake yana wani karkacewa ya zura duka hannu a aljihun wandon sa a bayansa kuma karnuka guda uku ke binsa duk inda yasa kafa kamar rakumi da a kala,duk inda yazo giftawa kafin ya karaso za ka ana darewa kowa yayi takansa,da sun san mistake kadan ne zai hadaku yanzun nan zai gwada ma rashin imani,isarsa kofar gidan yayi daidai da fitowar umma ta rako magajiya kofar gida.wucewa zatayi yasha gabanta sai data tsorata danganin fuskar sa ba alamun fara’a,cikin gadara ya fara magana ke tsohuwa bakiji jan kunnen da na miki ba ko wai gidan tsoho ne,da zaki damu mutane da zirga zirga to yasin na kara ganin ki wadan nan ya nuna karnukan sa su rakaki har gida ko kuma insa addar nan in cire miki rabin kai,kallon addar dake hannun shi magajiya tayi tare da zaro,cikin rawar tace aa basai takai mu ga haka nama daina wallahi wuce shi da sauri tayi ko waige bata kara yiba,umma dake tsaye rai a bace ta bude baki zata fara surfa balaki kallon daya mata yasata fasawa tare da shigewa gida tana mai kara tsanar sa a ranta“”wucewa cikin gida yayi dan shi dama bacci ya kawoshi gidan

sai kusan laasar jidda ta gama ayyukan da inna da rabi suka sata,buta da dauka tayi alwala sannan ta shige daki ta fara sallah taji shigowa hadaladu sallah take amma sai da gabanta ya fadi dan kuwa kayanshi na nan bata wanke ba saboda aikin daya mata yawa.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button