AFRA KO AMRAH HAUSA NOVEL

AFRA KO AMRAH 7-8

????7⃣????
Tsaye JB yake yana ma Afrah bye bye har sai da ya daina ganin su sannan shima yaje ya shiga tashi mota.

Yayinda muka bishi domin ganin shi d’an gidan waye.

Unguwàr New G. R .A ya nufa da ke cikin garin baucci layin farko gida na uku,

horn yake tun kan ya qarasa,
cikin hanzari kuwa mai gadi ya wangale masa qatoton gate.

Da shigar sa ya parker mota ba ma a inda ya da ce ba wanda cikin gudu gudu ya qarasa shiga cikin gidan tare da kiran mom!mom!!mom!!!
Oh no momma! wai ina kika shiga ne?

Wata mata muka hango tana saukowa kan staircase mai kyau da ita wacce kallo d’aya zakayi mata kasan tabbas wannan matar manya ce.

Kan taqaraso take fadin lafiya my son wannan kira haka?
Da sauri yaje ya riqo hannayen ta ya kai ta kan kujera ya zaunar ya durqusa kan guiwoyinsa yana mai fuskantar ta yace “mom albishirin ki yau na samo matar da zan aurà daga yau sae ki huta da min qorafi, da murnar ta tace”wow! gud story my dear son, er gidan wace ce?may be kin santa momma,Zarah ce wacce farhan ke riqo,cike da rashin fahimta take kallon shi tace “wace Zarah ce farhan ke riqo? oh no momma to Afrah nake nufi…. Kaddai kace min Afrah er gidan marigayi Alhj Sadiq wacce shekarunta baza wuce shekara biyar ba… Aha momma ita ce wlh… Mtsw Allah ya shirya min kai junaid,cike da shagwa6a
Yace “momma me kuma nayi? Haba my son ya zaka kawo min er shekara biyar kace min ita kake so ka aura nida banqi a cikin satin nan ma a maka aure ba,amma idan kace sae ka jira ta ban san iya lokacin da za’a dauka ba kenan, wata qil ma bana raye,jikin JB yayi sanyi ya wani 6ata fuska kamar qaramin yaro yace”momma ai kinsan mace ce saurin girma ne da ita,cike da alamun rarrashi tace “kaga my Son kayi haquri ka ajiye zancen yarinyar nan ka samo wata dai dai da kai kaji, fuskar nan tashi kamar zai yi kuka ya tashi daga durqushen da yake tare da sakin hannyen maman shi ya kalli mahaifin sa da ke tsaye a bakin qofa wato uncle Basheer yace “father kaji abinda momma take fada ko,
shike nan ni duk na kawo yarinya ace bata yi ba na nemo wata,kuma kullum a dame ni da qorafi naqi na kawo yarinyar da zan aura.
Mamansa ta girgiza kai hade da murmushi domin tasan JB bai ta6a kawo yarinya yace gata da sunan zai aura ba sae a wannan karon da shine na farkon sa.
Mahaifin dai nasa shima murmushi yayi yace “junaid ai yau ne farkon kawo zancen zakayi aure a gidan nan,kuma zancen naka kamar da wasa a cikin sa yarinya er shekara biyar kuma kurma ce fa….. Ni Abba ko ta had’a da makafta ina son ta a haka kawai dai kace min ka amince na jira ta idan ta girma a mana Aure, kaji dad, don Allah Father kar ka ce a’a wlh ni kadai nasan irin yanda nake ji a game da ita duk da cewa qaramar yarinyar ce,amma tun lokacin da ka d’ora ta a gaban assembly na sami kaina da jin sonta fiye da yanda nake jin son sauran yara,kuma ina ji a jikina rayuwa da ita alhairi ne a gare ni,wanda na tabbatar idan ban same ta ba zai iya haifar min da matsala.
Uncle Basheer dai tsaye kawai yayi da mamaki yana kallon JB na zuba masa rashin kunya,
JB yaci gaba da cewa”Father kar ka ce nayi rashin kunya abinda nake ji ne na gaya maka wanda ina jin hakan zai sa ka tausaya min,pleeease! father.
Uncle Basheer ya nisa yana mai ci gaba da kallon JB wanda ya fahimci tabbas da gaske JB keyi yace”nayi maka alqawari junaid indai har yarinyar nan tana sonka idan ta girma to zan aura maka ita
Him!zo kuga JB a wannan lokaci wanda kan tsananin murna sakin baki yayi yana kallon mahaifin sa domin bai zaci abin zai zo masa da sauqi haka ba,dunqule hannyen sa yayi ya jimqe kamar wanda zai naushi wani abu tare da fadin “wuhuu! Father na gode sosai! yaje ya rungume mahaifiyar sa tare da bata kiss a kumatu yace “momma ki qara min godiya a gun Father zan je na kaiwa Granny labarin farin cikin da nake ciki a yau”yana gama fad’ar haka ya fita da gudu yayinda uncle Basheer ya sami guri ya zauna,wanda tun kan ya zauna mahaifyar JB ke kallon shi da mamaki tace “Abban junaid ya zaka biye ma yaron da yau kamar ba a kan hankalin sa yake ba,
Umman junaid ba wani baya kan hayaccin sa,kin fi kowa sanin halin junaid idan ya qwallafa abu a ransa wanda idan bai sami abin ba kin san babbar matsalar da ke biyo wa baya,kuma kin san irin son da nake yiwa junaid kasancewar shi kad’ai ne d’a a gare mu.
Amma Abban junaid kasan yarinyar nan fa kurma ce bata ji,indai wannan ne mai sauqi ne domin zan iya yin komai na ganin cewa ta dawo normal sbd dama can ba kurma ba ce wata matsala ce tasa ta daina ji domin yanzu haka wani sa’in jin ta yakan dawo mata magana ne kawai da bata iya wanda inshaAllah idan aka fitar da ita qasashen waje zata samu lafiya, kawai abinda nake so da ke ki mana fatan nasara…..to Abban junaid Allah ya sa ayi nasara.

Futha luv???????? & Billy giro????

8⃣????
Sai dai da alama ta fadi haka ne kawai don ba yanda zàtayi, amma ko kadan bata ji dadin hukuncin da Uncle Basheer ya yanke ba,bcs sae magana take a ranta,tana mai cewa:
ni da na matsu naga en jikoki na amma ace sae ya jira er qaramar yarinya har sae ta girma….uncle Basheer ya katse ta da cewa “ina buqatar ruwan sha bata iya tashi ba sae mai aiki da ta shiga qwalawa kira domin ya bata haushi ba kadan ba,
har ma bata jin zata iya kawo masa ruwan da kanta.

Bayan wasu kwanaki da faruwar hakan, farhan ne zaune a bedside daure da towel iya qugu yayinda Amrah ke bayan sa durqushe akan guiwoyinta tana riqe da d’an qaramin towel tana goge masa gashin kansa har izuwa gashin qirjin sa da yasha ruwa ya kwanta luf,
ita ma towel ne a jikin ta da alama wanka suka fito domin kowannen su yana dauke da digo digon ruwa a jikin sa.
Da ta gama tsane masa ruwan jikin sa ne ta wani lafe a bayan sa kamar wata er baby,ta sakado hannayen ta akan qirjin sa tana yawo da su slowly slowly yayinda idanuwan ta suka fara lumshewa alamar bacci take ji.
Farhan yakai hannu ya shafo gashin kanta yace “yadai Amrah ya akayi? cikin muryar ta wacce ako yaushe baya jin ya gaji da sauraren ta tace”uncle na gaji da yawa ga bacci da nake ji sosai, jawota yayi ya maida ta gefen sa ya zaunar tare da dora kanta a qirjin sa yana mai ci gaba da shafar sumar kanta, yayinda yake kallon fuskar ta cike da kulawa,yace”inace komai kin packer mana wanda zamu buqata?komai na packer uncle, sae dai naji dazun kana waya wanda a cikin wayar da kayi na fahimci kamar ba mu kadai zamu yi tafiyar ba, eh ba kowa bane face JB,
sae dai ban san me zai kai shi ba.
Kawai dai yaji naje ma uncle Basheer da zancen ina so ya hada ni da abokinsa qwarraren likita ne fanni ido da kunne yana zaune a qasar India kasancewar sa ba’indiye,
shine yake ce min dama kuwa yaso yamin zancen akai Afrah gurin shi ko za’ayi nasara tunda dama can ba kurma bace, sae gashi na riga shi zancen , shine yake ce min ba ma likitan kad’ai zai had’a ni da shi ba zai d’auki nauyin komai na ganin ta sami lafiya nace da shi a’a ya barshi domin ba ita kad’ai zan kai ba har da ke sbd kema idanuwanki sun sami matsala ne a sanadiyar ulcer.
To shine fa JB yace zai je ya raka matar shi wato Afrah amma nasan da wasa yake akwai dai abinda zai kai shi.
Uhm bare kasan JB da abin wasa yake,
Lallai wasa yake domin yasan Afrah Tawa ce ni kadai bada kowa ba,domin bana jin zan iya bawa kowa Amanata,
cike da shagwa6a Amrah ta masa wani kallo tare da bugo qirjin sa tace”uncle ka fara ko”farhan yayi murmushi tare da girgiza kansa ya tashi ya dauko musu kayan bacci ya bata nata sannan ya saka nashi ya nufi gadon Afrah da tuni baccin ta yayi nisa,
Addu’a yayi mata kamar yanda ya saba yi mata a kullum, sannan yaje ya kwanta tare da jawo Amarah a qirjin sa ya rungume suka shiga baccin da ma’aurata kawai keyin sa bada gwauraye ba????lol!.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *


The reCAPTCHA verification period has expired. Please reload the page.

Back to top button