BA DON SHIBA HAUSA NOVEL

BA DON SHIBA 26-30

Page 2⃣6⃣ to 3⃣0⃣

Sai da ammar da yaransa suka musu wulakanci na bugawa a jarida shafin farko,,,sannan yasa suka kara buge haladu.,inna asabe kuwa tunda aka mata zuwa daya har yau tana kwance shame shame rike da kafarta da wani ya taka mata a cikinsu,,,sai da suka gama duk wulakancin da zasu musu sannan suka fice suka barsu kwance anan bamai taimakon wani a cikinsu,,

fitowar su yayi daidai da komawar kowa cikin gidanshi…dan dama duk mutane najin abinda ke faruwa

sai da jidda taci abinci tayi sallai ishai sannan taiwa maman salaha sai da safe ta tawo gida,,,tana zuwa kofar gidansu gabanta ya fadi ganin kofar a yashe a kasa tasan wannan aykin ammarne..da sallama ta shiga gidan,,su rabi ta samu zaune kusa da inna asabe tana gasa mata kafa da ruwan zafi ita kuma asiya da indo suna kan haladu suna goge mai jinin da ya bata mai fuska duk fuskar nan ta kumbura sai ya kara muni kamar irin horror dinnan….kowa ido ya bita dashi ba halin magana domin su rabi sunji labarin abinda ya faru shiyyasa ba wanda ya tanka mata..daki ta shige kawai tayi kwaanciyar ta..

Tofa tun daga wannan ranar baima dukan jiddah a cikinsu sai dai abita da harara da kuma tsaki..aikin gida ne dai haryau ba fashi,,

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya duk da gidan ba dadi amma yafi da tunda yanzu har abinci ana bata kuma bata musu wanki saidai girki da gyaran gida,,a bangaren ammar kuwa har yanzu umma tana nan tana hada mai tarko duk da abbansa baya yadda,,amma dai bata karaya ba tayi alkawarin sai ya bar gidan duk daren dadewa,

A yanzu jiddah tayi jss c.e kuma ammar ne ya mata komai duk shima wannan shekarar zaigama scondry skul,,da kansa ya mata registration anan makaran tarsu aka bata ss1 science class,,tana makaranta cikin kwanciyar hankali da wuri take tashi ta gama duk ayyukanta na gida sannan ta shirya ta tafi,,tana fitowa zata samu ammar a bakin layi shi zai rakata har bakin makaranta sannan ya bata kudin break,tunda yabar makarantar haka yake mata duk da shima abbansa na neman masa makaranta,,,

inna asabe ce zaune ita da lami,,lami kawar inna asabe ce tun yarinta dan wasu halayen duk ita ta koya mata dan lami bata zaman aure ga bin bokaye,,inna asabe ce ke bata labarin abinda ammar ya musu har gida,,,mtsww lami taja tsaki kina aikin me har haka ta faru idan hagu takiya ai sai a koma dama,,tun farko sai da nace miki mukai sunanta gurin na bakin rafi amma kika ki to yanzu wa gari ya waya ke mana,,duk layi anata yi dake yayanki sun lalace ita kuma sai yabonta ake,,wannan yabon shi zamusa ya koma aibatawa,,yanda shikansa ammar din sai ya kyamace ta,,tabbas kawata kin kawo shawara me kyau gobe da sassafe zan shirya in biyo ta gidanki sai muje gurinshi,,yauwa ko kefa ki maidata abin kwatance,,ki dauki fansar abinda ammar ya miki dan na tabbatar sai yafi kowa shiga kunci idan ya ganta ,,,ai fa nagode lami nida duk banyi wannan tunananin ba,,,har kofar gida ta rakota suna kara tattaunawa akan muguntar da zasu ma baiwar allah da bata rikesu a zuciya ba…

Da daddare jiddah na zaune kofar daki itama inna asabe suna zaune ita da yayanta firar su suke cikin kwanciyar hankali,,sai dai kawai taji suna shewa,,kadaici ne duk ya isheta ina ma tana da iyaye da rayuwar ta bazata zama haka,,wani yaro karami ne ya shigo gidan,yace ana kiran jiddah a waje,,ba wanda ya tanka a cikinsu itace tace kace gani nan zuwa dan tasan ammar ne,,hijab kawai tasa tafita a tsaye ta same shi a kofar gidan,,gaeshe shi tayi ya amsa cike da kulawa,,shiru ne ya biyo baya kafin ya fara magana cikin sanyin murya kamar ba ammar ba,,,jiddah ya kira sunanta da sauri ta dago ta kalleshi domin kuwa yanda ya kira sunan nata ne ya sanyaya mata jiki,,ce mata yayi ga wannan amsa kawai tayi ba tareda ta duba ko meye ba,,shine yace atm carda dina ne sannan ga waya nan itama ya miko mata..amsa kawai tayi tana jiran karin bayani,,,jiddah zanyi tafiya mai tsawo abbana ya sama min makaranta a noida university india,,da sauri ta dago ta kalleshi domin kuwa maganar ta bugeta tuni har ta fara hawaye,,shima dakewa kawai yakeyi amma da ba abinda zai hana shi yin kuka amma bayaso ya karya mata zuciya,,,kuka ta fashe dashi da karfi domin ji take in ammar ya tafi kamar wani abu zai faru,kiyi hakuri jiddah ai zan rinka zuwa hutu akai akai,,,ita dai bata saurare shi ba kukanta kawai takey..jin kukan yake har cikin ransa,,,shima dan dai ba yadda zeyi ne abbansa ya matsa masa amma da ba wanda ya isa yasa shi zuwa wata kasa karatu,,dakyar ya samu ya lallabata har tayi shiru amma fa a zuciyarta ji take kamar ta mutu saboda bakin cikin tafiyar ammar,,,da kyar ya lallaba ta har ta shige gida,,shima ya tafi

a wannan daren ba wanda ya runtsa a cikinsu ,,,dan jiddah kwana tayi tana kuka…shi kuwa tinana shi wani hali zata shiga bayan tafiyar shi…

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button